*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Wannan page kyauta ce gareki sukutum Kanwata ta hannun damata, wadda nije jinki har cikin b'argona, ke ta daban ce a wajena HANNAH MAHMUD SUHANA ina yinki har abadan abade😍*
*Lamba ta 30*
Yana k'are fad'ar maganar ya mik'e tsaye zai fita har ya kai bakin k'ofa zai fita, Hajiya Mama ta kira sunanshi cikin wata muryar da shi kanshi sai da ya ji kiran ya fad'ar masa da gaba, cikin sanyin jiki ya dawo ya zauna tare da b'ata fuska tamkar wanda aka daka yace
"Nasan tambayar da kike son ki yi man Hajiya Mama plss ki yi hak'uri WALLAHI ni ma bansan me ya ja ni na kasa barinta ta auri D'ankauye irinta ba, ni dai abunda kawai na sani taimakonta na yi niyyar yi saboda naga tana son karatu sosai,kuma matuk'ar ta yi aure wannan bak'in k'auyen na su to gurinta ba zai tab'a cika ba, kinji abunda ya sa na aureta Hajiya Mama don nasan Mahaifinta ba zai bani ita haka kawai ba in zo da ita"
HAJIYA Mama tun daga kallon da ya ga tana yi masa ya gano cewa maganarshi bata yi tasiri a wajenta ba, shiyasa ya yi shiru dolenshi zuciyarshi cike da takaicin me ma yasa bai barta ta yi aurenta ba?.
Hajiya Mama ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya sannan tace,. "Baka sonta ka hana Abokinka Lawi ya aureta??? Bayan kasan cewa shi ma ai taimakonta yake son ya yi akan buk'atarta me ya hana ka taimakeshi ya sameta????"
Safwan ya sosa kanshi yace "ai baya garin ne shiyasa da ni ba abunda zai sakani wannan aikin, saboda haka ki barta a nan kawai ta shiga cikin ma'aikatan, su ci gaba da aikinsu kud'inta na wata idan an tara zan dinga aikawa iyayenta"
Hajiya Mama ranta a b'ace tace,. "Safwan ka fita idona in rufe yarinya dai ko kana so ko baka so yanzu ta zama matarka, kuma ko kai baka isa ka kunce shi ba matuk'ar ina raye, kai ko bayan raina ban amince da ka saki yarinyar cen ba matuk'ar ba wani k'wak'k'waran dalili ba"
Safwan ya yi saurin fad'in "haba Mama WALLAHI ni bana son zama da ita da sunan aure ki bari kawai a taimaketa ta yi karatun shikenan kin ga zamu sami ladar, amman a ajiye zancen auren kawai Hajiya Mama yafi gaskiya, don ni Makaranta ma zan koma in k'aro karatu har zuwa lokacin da zan sami wadda nike so in aura"
Ranta ya kai iya k'ololuwar b'aci tace,. "Tashi daga gabana Safwan bana son in sake jin wata magana daga bakinka, ka je kawai akwai ranar da gaskiya zata yi halinta, amman ina son ka fara cukucukun nema mata Makarantar saboda ka samu ka cika alk'awalin da ka d'auka tun wuri"
Safwan ya marairece yace,. "Don Allah Hajiya Mama kiyi hak'uri naga kamar ranki ya b'aci WALLAHI bana son ganin fushinki ke ma kin sani, kada ki bari wannan 'yark'auyen ta shiga tsakanina da ke don ALLAH"
Ta yunk'ura ta mik'e fuskarta a sake tace,. "Ka je ka ji da bak'in in sun kammala in zo mu gaisa amman ina son kafin su tafi ka kai Mahaifinta Gidanka ya ga muhallin 'yarshi"
Safwan ganin yanda yanayinta yake ya sa bai musa ba ya mike ya fice, zuciyarshi cike da tunanin yanda zai yi ya kunce auren cikin ruwan sanyi ba tare da ya b'ata ran Hajiya Mama ba.
Dije kam tana cen Surry tanata shiryata cikin tsanaki duk da taso ta zuba d'ige d'igen kwalliyarta da ta saba amman Surryn ta hanata, sai ko ga Dije ta fito Masha ALLAH da ita saboda daman cen ita mai kyau ce duk da ta kasance bak'ar Mace, amman bak'inta mai kyau ne don bai b'oyewa kyawunta fitowa ba, Dije sai wasar baki take yi tana kallon kanta cikin madubi ta makawa Fiddo harara tace da Surry
"Ashe haka nike da kyau ni ma ban sani ba? Ji rigar nan WALLAHI ta yi man kyau sosai amman ta Makkah ce ko?"
Surry tana 'yar dariya tace, "a'ah a nan garin aka siyeta ba ma ita kad'ai ba ce da wasu ma suna d'akin Hajiya Mama kuma donki kawai aka siyo su, ki yi ta sakawa ke ma ki zama 'yar gayu irin Fiddo"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.