*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA Team Dije da team Safwan ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU DUKA👍🏻*
*Lamba ta 12*
Ko da Baffah ya dawo shiru shiru bai ji duriyar Dije ba tun yana zura idon ganin ta inda zata bullo har ya gaji dai ya tambaya, don ita kanta Innar ganinta da yayi sai a hankali yasa ya zargi ko sun k'ara kwatawa ne da Dijen shiyasa yaji Gidan shiru alamun bata nan, Inna kam bata so sanar dashi ba har sai ya ci abinci don tasan muddin yaji ba k'aramin d'aga hankalinshi zai yi ba, sai dai dole ba yanda ta iya saboda yanda ya matsa mata da tambayar ina Dijen taje har lokacin bata dawo Gidan ba?.
Kai tsaye ta ce dashi tana ciki bata da lafiya, hankalin Baffah a tashe ya garzaya d'akin Innar inda Dije take kwance cikin zazzab'i sharkaf sai nishin marasa lafiya takeyi, aiko tana ganinshi ta fashe da sabon kuka gwanin ban tausayi, cike da fad'uwar gaba Baffah ya zauna bakin gadon ya rik'o hannunta yace
"Meke maki ciyo?"
Dije ta share hawayenta cikin rawar murya tace, "jikina gaba d'aya ciyo yake yi man ga raunukan sai zafi suke yi man Baffah, WALLAHI saura kad'an a kashe maka ni yau da baka zo ka sameni ba"
Baffahn ya zaro Ido waje yace,. "Wanene da wannan danyen aikin gareki halan?, Ashe ko yau ba zan saurarawa kowa a gidan nan ba tunda har abun ya zo da cin zarafi irin haka, ki yi gaggawar sanar dani wa ya dake? tashi zaune ki fad'a man don in san irin matakin da zan d'auka kan mutum ko ma wanene"
Dije ta yunkura dakyar ya rikata ta tashi zaune cikin kuka ta fara nuna masa raunukan da Safwan ya ji mata ciyo, Baffah kam ganin jikin Dije duk shatin bulalar yasa ya fara zuba ruwan fad'a bakinshi har kumfa yake yi saboda tsabar b'acin rai, Inna kam ganin yanda ya hau da yawa yasa ta fayyaace masa komi da aka fad'a mata ta sanar dashi, akan wanda ya dake tan tare da dalilin da ya janyo ya yi mata dukan.
Baffah cikin tsananin b'acin Rai ya ja talkamanshi sai Gidan Maigarin, inda kai tsaye ya fara nuna rashin dacewar abunda BAK'ON Malamin yayi wa 'yarshi, Maigari da sauran mutanen da ke wurin Suka dinga bashi hak'uri sannan cikin tattausan kalami Suka nuna masa aibun abunda Dijen ta yi masa wanda Sam Sam bai dace da tarbiyyar dalibi ga malaminshi ba, tun yana ganin laifin Safwan har ya kai ya gano ashe rabin laifin duk na Dijenshi ne, sannan Maigarin da mutanen Suka fahimtar dashi sosai akan ya tsawatarwa Dije akan sake faruwar wata hatsaniya tsakaninsu, daga k'arshe suka bashi hak'uri akan abunda aka yiwa Dijen , sannan ya baro wurin ya koma gida inda dakyar da jib'in goshi ya samu tasha yan farau faraun fura sannan tasha pracetamol ta koma ta kwanta, cikin dabara Baffah yayi ta kwantar mata da hankali akan muddin Safwan d'in ya sake dukanta ta zo ta sanar dashi don wannan karon shi da kanshi zai rama mata, ba ko Malami yake ba ko hukumar ce da kanta sai dai idan an rufeshi mabudin ya b'ace.
Sannan Dije ta rage bak'in cikin da ke cin zuciyarta, amman fa tasha alwashin sai yasan da ita yake zancen, haka ta kwana tanata wassafa irin muguntar da zata yi masa, cikin ikon ALLAH kwananta biyu ta warke Masha ALLAH,a rana ta uku da komawa Makaranta ne ta ci alwashin sai taje school d'in ko don labarin da su Jummala suke ta bata kullum akan yanda suke gane karatunsu, duk da dai shi Safwan d'in ba hausa yake yi masu ba amman dai ba laifi suna dan fahimta sama sama.
Aiko ranar Alhamis tun da sassafe ta shirya cikin uniform d'inta, ta yi sallama da su Baffah cikin natsuwa ta nufi Makarantar, don shi Baffah har so yayi ta daina zuwa Makarantar a cewarshi tunda ba ta ALLAH ba ce, don dai ita Dijen ta nace tana son karatun ne yasa ya amince amman ya ja kunnuwanta da kyau akan ko kallon Safwan d'in kada ta sake yi don gudun wata sabuwar fitinar, sai da ta yi masa alk'awali sannan ya barta akan zata koma d'in, don tun lokacin da tasha dukan ta zama wata so silent da ita ko rashin jin cikin Gida duk ta daina yi, saboda kwata kwata ko walwala daina yi ta yi a gidan kullum tana d'akin Inna dunkule kan gado, don duk masifar da take yiwa akuyarta idan ta zubar da abinci ko abinsha, a lokacin duk ta daina don acen baya har bulala take sakawa ta yi ta dukan akuyar tana yi mata fad'a da kashedi kala kala, har wani zubin sai Inna ta yi mata fad'a akan zalin d'in akuyar da take ci sannan take kyaleta, amman sai gashi Safwan yasata zama kurum kurum dolenta.
Aiko tafe take kanta a duk'e tun da ta hangosu daga nesa ta Sha mur tare da saita natsuwarta, don ko da ta zo ta gabansu sai da ta dan rankwafa sannan ta gayar dasu sai dai bata jira sun amsa ba tayi gaba abinta, Safwan ya bita da wata jar harara yayi kwafa yace
"Mumu kawai black cat"
Lawi ya kyalkyale da dariya yana dafe bakinshi don kada Dijen ta jiyo dariyarshi, amman duk da hakan bai hanawa kunnuwanta ji ba sai dai ko kad'an bata waigo ba har ta shige cikin class dinsu.
Dan lokaci a tsakani sai gashi ya shigo ajin yana wani cin magani ya jefa mata chalk tare da nunata yace ta goge allo, ta mik'e ba tare da ta yi gardama ba ta goge black board d'in tass ta koma ta zauna, daga nan ya fara karatunshi mai cike da zallar turanci tsintsa don mugunta duk ya zo tambaya sai ya tambayeta saboda kawai ya kureta,
Wani lokaci ta bashi amsa dai dai wani kuma idan bata iya ba ya kirata jahila, haka ya k'are darasin nashi cikin isa da gadara ya koma tambayoyin cikin tambayoyin ne kawai sai ga wani bera tun daga cen saman rufin ajin ya fado tsakiyar class d'in saboda rufin ajin gaba d'aya duk ruwa sun canye rabin, aiko ba shiri yayi wani tsalle cikin tsoro yace"Oh my gosh"
Bera ko kamar ya san tsoronshi yake yi garin gudun neman mafaka ne ya nufi wurinshi, aiko sai ga Malam Safwan da yin wani uban tsalle ya dale window yana sambatu irin na tsoro, ganin hakan yasa duka Yan ajin suka fara dariya k'asa k'asa, Dije kam fuskarta a had'e tamau tamau ba alamun ma zata yi dariya, bayan beran ya wuce ne a gurguje ya kammala karatun ya fice, Dije ta kalli Yar paper'r da ke hannunta ta fara karanto abubuwan da duk yayi ta fad'a mata kalmomi kanana na turanci kamar haka
Illiterate.
Black cat.
Urgly girl.
Village girlSai maimaitasu take yi amman ta kasa tantance fassararsu bale tasan ma'anarsu, a ranta ta kudurta zata tambayi abokinshi domin ya fassara mata su fillah fillah, Aiko kai tsaye ta fito ajin aka yi dace ta hangoshi cikin wani class yana karantarwa, aiko taje da sallamarta cikin ladabi tace dashi wurinshi ta zo, ya yi Yar guntuwar dariya ya d'auki excuse wurin Yan class d'in ya fito, cikin sakin fuska tace dashi don ALLAH wata tambaya take son yi masa in da Kai tsaye ta fara zayyano sunayen a kanta da ta samu ta hardace su cikin kanta.
Lawi yayi shiru yana tunanin amsar da zai Bata wadda ranta ba zai b'aci ba, don zuciyarshi ta bashi cewa duka kalmomin daga bakin Safwan suka fito zuwa gareta don yasan k'aramin aikin abokinshi ne wannan, aiko dai ya koma class ya dauko wani littafin kalmomin turanci da fassararsu cikin harshen hausa ya mika mata yace taje ta duba da kyau zata gano fassarar kalmomin duka a ciki, cike da jin dadi Dije ta karb'a tana murna har ta juya zata tafi ta waigo tace
"Don ALLAH ka ara man shi nan da kwana Uku zan maido maka"
Yana dariya yace,
"Na baki sati d'aya ma amman ki sani akwai tambayoyin da zanyi maki idan lokacin ya cika kin kawo"
Cike da jin dad'i tace ta amince ta koma class dinsu zuciyarta cike fal da murna, tare da tunanin hanya mafi sauk'i da ta gano wadda zata rama abunda Safwan d'in yayi mata cikin dan kankanin lokaci.
Har aka tashi Makarantar Dije bin littafin take yi d'aya bayan d'aya shafi bayan shafi har ta gano abunda duk yake nufi da miyagun kalmomin da ya yi ta jifarta da su kala kala.
Tsawon kwana biyu Dije tana kamun beraye tana sakawa kwali tana b'oyewa don har da abinci da ruwa take ajiye masu, don kuwa ta kama bera yafi ashirin irin bakake d'in nan manya manyan, kullum Inna da Baffah sai dariya suke yi mata suna fad'in
"Dije Kuma aikin kiyon beraye kika koma yi ??"
Sai dai tayi dariya amman bata nuna masu cewa wani nufi ne a ranta ba, sai ko gashi tun da sassafe zata je Makarantar Allo ta yi dubarar fita da k'aton kwalin berayen, bata zame ko'ina ba sai Gidan Maigarin cikin nasara ba kowa a wajen ta yi dubarar ajiye kwalin ta je k'ofar d'akinsu Safwan ta leka, sai ko gashi shi kad'ai a d'akin yanata baccinshi hankali kwance.
Dije ta d'auko kwalin ta shigo bakin d'akin a hankali ta kwantar da kwalin ta budeshi Aiko sai ga Beraye suna ta fitowa daga ciki suna shigewa cikin d'akin sai da ta juyesu duka sannan ta fito da kwalinta ta janyo k'ofar ta rufe ruf da kwadon da ke makale jikin k'ofar, sannan ta tafi da key din ta cillashi cikin ciyayi cikin sauri ta tafiyarta zuwa Makaranta zuciyarta cike da tsantsar farin cikin rama abunda ya yi mata .
Ku taimaka kar ta yi kisan Kai😳🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
Akafta🤣
D/AUTA CE✍🏻
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.