1

302 24 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi  ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅*

*Lamba ta 33*

Cikin wata ɗaya da zuwan Dije makarantar da yawa mutane sun fara saninta, saboda halin nata da a ko'ina baya b'oyuwa don kuwa watarana tana zaune kan barandar da hostel ɗinsu, taga wata house captain ɗinsu ta saka wata yarinya kneel down tanata dukanta, kuma ga shi ita yarinyar har ta fi Captain ɗin tsawo da girma saboda jin haushin zaunen da ta yi anata dukanta tana ihu yasa Dijen ta nufi wurunsu ta tsaya, cike da fushi ta fisge bulalar hannun Captain ɗin ta zubawa yarinyar bulala ɗaya iya k'arfinta tace

"Kinga yanda na yi maki ko to haka nike so ki karɓi bulalar ke ma ki rama ko in haɗa maki jini da majina yanzu"

Ba Captain ɗin ba harta ita kanta yarinyar da sauran mutanen da ke wajen sai da suka zaro ido, saboda mamakin ƙarfin halin Dije a matsayinta na junio a house ɗin, ganin yarinyar ta ƙi karɓa cike da tashin hankali da tausayin Dijen yasa ta rufe bakinta alamun firgici.

Captain ɗin ta riƙe ƙugu tana ƙarewa Dije kallo sama da ƙasa tace,.  "Ashe ko yau zan ci Uban Matar aure a makarantar nan sai naga uban da ya ɗauke maki gindin da zaki tunkarata da wannan baƙin gangancin"

Ta yi wata arniyar dariya ta fisge bulalar a hannun Dijen ta yi ta zabga mata bulolin ta  duk inda ta samu, Dije kam jin zafin dukan yana ratsata yasa ta yi wani ihu ta yi tsalle ya haye kan Captain, kafin kace me wurin ya cika maƙil da yan makaranta, tsakanin prefet da senios  har ma da juneos ɗin ba'a bari ba, don kuwa Dije ta zage damtse sai artabun doke doke take yi tsakaninta da Hause Captain ɗin, in da da ƙyar aka ɓanɓari Captain ɗin a hannun Dijen, don kowa ƙasa ta murƙusheta tanata kai mata naushi aiko gaba ɗaya prefet suka taru kan Dijen sunata jibga saboda takaicin abunda ta yiwa ƴar uwarsu a gaban junios ɗinsu masu ganin girmansu da kuma jin tsoronsu.

  Hannatu a gefe sai uban kuka take ci saboda ganin dukan da ake yiwa Dijen, ganin za su kassarata ne yasa ta bazama aguje sai gidan principal ɗinsu tana sanar da ita, aiko a firgice principal ɗin ta nufo Hostel ɗin don zuwa lokacin makarantar gaba ɗaya ta taru wajen ɗauki ba daɗin dukan da prefet ɗin suke yiwa Dijen, don kowa ya kasa karɓarta a hannasu hasali ma wata ɗaya daga cikinsu da ta so a ƙyaleta itama aka hayayyaƙo mata dole ta yi shiru.

Ko da principal ɗin ta zo tuni sun jigatar da Dijen Baffah don kuwa gaba ɗaya sun ji mata raunuka don ko motsin kirki bata iya yi, cike da tashin hankali principal ɗin ta  sa aka ɗauketa aka nufi clinic da ita cikin sauri aka fara treatment ɗinta, sannan ta sa aka haɗa assembly na gaggawa  ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya hallara prefets ɗin da suka yi aikin kam gaba ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, don kuwa sai a lokacin ne wasu da yawa suka ji labarin cewa wai matar aure ce, duk da cewa wasu sam basu yarda da cewa matar auren ba ce duba da yanayin karancin shekarunta, don kwata kwata a lokacin Dijen shekararta goma sha huɗu.

Cikin tsananin ɓacin rai principal ɗin ta yi ta faɗa cikin firgici da jin tsoron abunda zai biyo baya, saboda jan kunnen Da Hajiya Mama ta yi tun farkon kawo Dijen akan kada a daketa ko a sakata wani aikin wahala saboda matar aure ce,  sannan ta yi hani ga kowace prefet da ta sake dukan juneos ba tare da ƙwƙƙwaran dalili ba, sannan ta tsawatar sosai akan kada a sake yiwa kowa irin wannan dukan da ake yiwa yaran mutane.

Bayan an sallami sauran ɗaliban ne aka bar prefets ɗin inda aka yi bincike aka fitar da waɗanda suka daki Dijen aka yi masu horo mai tsanani sannan aka karɓe ɗankwalayensu sannan aka basu suspension na kwana uku zuwa gidajensu.

Sannan sauran ta tsoratar da su sosai akan kada su sake dukan ƴar kowa uwa uba kuma ita Dijen da ta kasance matar aure inda gaba ɗaya dukansu sunyi mamakin jin cewa wai ita Dijen matar aure.

Hakan da aka yi shi ya janyowa Dije suna a cikin makarantar, sai dai kuma waɗanda abun ya shafa tuni sun k'ulla gaba da sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu da ita, inda wasu da yawa sun ci alwashin cewa sai sun ja mata abun da za'a koreta makarantar.

Not editing😻

😝😝😝😝

Akafta😝



D/AUTA Ce✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now