1

377 30 0
                                        

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*COMMENTERS GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻*

*Lamba ta 20*

Sai da ta yi masa alk'awali sannan Suka yi sallama ta fito ta nufi Makaranta, tana tafe tana wasar baki musamman idan ta tuno watarana ita Likita ce, sai wassafa yanda zata dinga soke Mutane take yi suna ihu, ita kad'ai sai faman murmushi take yi bisa hanya har ta isa makatantar, inda ta taradda Malam Safwan zaune bakin barandar  ya duk'e kanshi ya lula zuzzurfan tunani mai zurfi,don har ta kawo wurinshi ta gayar dashi bai ma san ta yi ba, ganin ya kyaleta yasa ta murgud'a masa Baki ta wuce abunta, tana gaf da shigewa class ne ya ankara da ita aiko cikin sauri ya d'aga murya yace

"Hey!"

Taso ta share amman dai ta waigo don tana da tabbacin da ita yake, amman duk da haka sai da ta nuna kanta tace

"Ni?"

Ya d'aga mata kai sannan ta dawo zuciyarta cike da tsoron laifin me ta yi masa kuma?, Aiko tana zuwa gabanshi zata yi kneel down ya yi saurin girgiza kai yace,.  "No! no!"

Dije ta mik'e cike da mamakin sauyawarshi ta kura masa kallo sai da ya yi shiru sannan cikin yaren hausa yace,.  "Me ya hanaki zuwa Makaranta kwana biyu"

Dije ta zaro ido waje saboda tsananin mamakin da ya bata bakinta yana rawa tace,. "Malam ashe daman cen ka iya hausa?"

Hararar da ya maka mata ce yasa ta yi saurin rufe Bakinta tace,. "Sorry ser"

Ya sake maimaita tambayarshi Dije kam nan take ta bata fuska tace,   "Baffahna ne ya hanani zuwa"

Cike da mamaki Safwan ya yi saurin cewa,. "Saboda mi?"

Dije wasu hawaye suka gangaro mata tace,. "Saboda Abokinka yace yana so ya aureni shine ya hanani zuwa Makarantar, yanzu haka ma sai da na yi masa alk'awalin bazan sake kulashi ba sannan ya barni na tafo, don ALLAH Malam ka ce dashi ya yi hak'uri ya daina yiman magana har sai na kare Makaranta, don WALLAHI ina son karatun bana son a hanani zuwa kuma gashi ma ina son ya kaini Makarantar Likitancin da yace zai kaini"

Ta k'are maganar cikin zubowar wasu ruwan hawayen, Safwan ya yi shiru yana nazarin maganganunta sannan cen ya d'ago da kanshi ya kalleta cikin sanyin jiki ya ce "kina so ki yi karatu mai zurfi bayan kuma kinsan hakan ba al'adar garinku bace, ko akwai wadda ta tab'a zuwa Makarantar gaba da primary a garin nan?"

Dije ta girgiza masa kai tace,. "Ko d'aya duka aure ake masu, yanzu haka ma cikin kawayena Hansai da Ladiyo da Jummala duk suna da Miji da an tashi aure kawai za'a yi masu"

Safwan ya yi saurin zaro ido yace,.  "Cabd'i jam! To ke ba'a yi maki Mijin bane?"

Ta rufe fuskarta tace,. "Ai Ni ba wanda ma ya tab'a cewa yana sona sai mutum biyu"

Cikin kureta da kallo tare da had'e fuska yace,. "Su waye Mutum biyu din?"

Dije ta rufe fuskarta tace,. "Kunyar fad'a nake ji WALLAHI"

Shi kanshi gano wannan firar bata dace da Malami da dalibi ba yasa yace,. "Ok to je ki shiga class amman Kika kuskura naji kince da wata na iya Hausa I will purnish you"

Dije ta dafe bakinta tana k'umshe dariyar da ta zo mata tace,. "Ba zan fad'a ba ai"

Safwan yana shirin sake yi mata magana ne ya hango Lawi zai shigo Makarantar ya yi saurin fad'in,. "Oya go to your class"

Dije ta tafi tana ta k'umshe dariyarta saboda gargadin da yayi mata ya bata dariya, don ganin renin wayon nashi ma ya yi yawa ashe ma ya iya hausa amman kullum yake ta zuba masu zallar turanci, sannan zagin da tasha yi mashi da Hausa ita da su Lanti ashe duk yana ji amman yake yi kamar bai san me suke fad'a ba, sai dai laifi kad'an zai sa ya yi ta harararsu yana muzurai, k'arshe ma haka zai k'are karatun ba tare da sun fahimci komi ba.

Lawi kam tun daga nesa da ya hango Dije yake ta sauri sai gashi kafin ya k'araso har ta wuce, cikin damuwa ya isa wurin Safwan ya zauna ya na bin class d'in su Dijen da kallo, Safwan ya yi masa wani kallo ya yi wani mere yace

"To yarinyar nan dai ka d'aga mata k'afa don yanzu ta ke sanar dani Mahaifinta ya hanata zuwa Makaranta ne saboda kai, idan har da gaske kana sonta to ka barta ta yi karatunta, don an gargad'eta a gida duk ranar da aka sake ganinta da kai za'a cireta daga school d'in gaba d'aya"

Lawi ya yi saurin fad'in

"Innalilahi wa'Inna ilairraji'un kai wannan bala'i da me yayi Kama?? WALLAHI kwana biyun nan da ban ganta ba jinsu nayi tamkar shekara biyu, Abokina ka taimaki rayuwata WALLAHI mutuwa zanyi idan har ban auri yarinyar nan ba"

Safwan ya yi saurin mik'ewa tare da buga wani uban tsaki ya barshi a nan ya shige Ofishin Malammai, Lawi ya bishi da kallon mamaki sannan ya yu shiru yana nazarin mood d'in abokin nashi akan matsalar, da kullum baya bashi goyon baya akan soyayyarshi da Dijen, asali ma sai Kara dakushe masa karsashi yake yi kullum safiya, a ranshi yace

_"shin wai  shi baya da imani ne da har ba zai taimakeni na samu abunda yafi soyuwa agareni ba?, Ko don shi har yanzu bai San zafin son bane?"_.

Ya furzar da iska mai zafi a bakinshi ya mike ya nufi office d'in ranshi a b'ace, saboda damuwowin da suka yi masa yawa ga rashin goyon bayan Safwan akan masoyiyarshi Dije, ga kuma wata bakuwar matsalar da aka kunno masa da ita, don rashin magana da Dije a wurin ba k'aramin purnishmen ne aka bashi ba, yarinyar da har gizo take masa a ido baya da wani mafalki a Yan kwanakin nan sai nata, lokaci d'aya a rabashi da ita irin haka ai an ci da zalinshi.

Ranar har aka tashi ba wata walwala ko wata huld'a mai k'arfi da ta shiga tsakanin Abokan biyu, abun takaicinma lokacin da aka tashin k'iri K'iri Dije ta ki tsayawa ta ji uzurin Lawi da ke son yin magana da ita, saboda tsoron a ganta aje a fad'awa Baffanta Safwan kam ba k'aramin dad'i hakan ya yi masa ba, ya sake girmama lamarinta saboda ganin ashe rashin kunyarta da sauk'i tunda har tana jin maganar iyayenta.

Lawi kam ko dakinsu bai nufa ba ya isa wurin Maigarin cikin damuwar da ta kasa boyuwa akan fuskarshi, Maigarin ya kalleshi cikin tausayawa don yasan labarin gizo baya wuce na koki, amman duk da hakan sai da ya wayance yace dashi

"Yarona lafiya Na ganka haka? ko wani abun ne ya faru cen Gida? "

Lawi ya kara sunne kai yace,.  "A'a Baba akan dai matsalar nan ne"

Maigarin ya ce,. "Wace matsala Kuma? Ko ta Yar Gidan Malam Sanda?"

Lawi ya d'aga kanshi yace,.  "Eh ita to yanzu abun ya Kara rikicewa saboda ko magana ma an hanata tsayawa ta yi dani"

Maigarin ya yi shiru sannan yace,. "Ka yi hak'uri yarona Ni zan ga Malam Sanda duk yanda muka yi zan neme ka"

Lawi ya mike tare da yi masa godiya ya yi d'akinsu, zuciyarshi cike da takaicin bala'in da ya janyowa kanshi yana zaman zamanshi.

Maigarin kam bai yi k'asa a gwiwa ba dakanshi bayan magrib ya yi tattaki tare da mukarrabanshi suka nufi gidansu Dije, cike da mamaki Baffah'n ya shimfida masu tabarma suka zauna tare da  yi masu sannu da zuwa.

Bayan an k'are gaggaisawa ne Maigarin ya yi gyaran murya yace,. "Malam Sanda nasan zaka yi mamakin abunda yasa na yo tattaki zuwa wajenka?, To ba komi ba ne akan matsalar Bakon yaron cen ne da Yar wajenka Dije, a zahirin gaskiya yaron nan dai na gano ba k'aramin so yake yi mata ba, shiyasa nace bari in zo in jaddada maka zancenshi da muka yi a kwanakin baya, shin har yanzu kana kan bakanka akan bazaka baiwa mutumen nesa yarka ba Koko ya abun yake?"

Baffah kam Nan take wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi amman cikin dariyar yake yace,. "Ranka shi dad'e ina mai jin kunyar sanar da Kai cewa na yiwa Dije Miji, kuma insha ALLAHu wata mai kamawa Zan auradda Dije ga Bala dan Gidan Mariganyi Mamman jikan Inna Duduwa"



To fa rigiji Gabji😳 lalle akwai kwacagiya😝


Akafta🤣





D/AUTA CE✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now