71

297 18 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*ALHAMDULILLAH!!!!*

*Lamba 71*



Dije da yaronta suna samun kulawa sosai tamkar a gaban iyayenta ko ma fi, don ta ɓangaren cima mai daɗi bata da wani aiki sai na cin daɗi, saboda har rago biyu ya sa aka yanke aka soye mata wani bayan an sarrafa sauran kala kala aka tasata gaba ta yi ta kwasar gararta, kwana biyar da haifuwarta ne ƴan'uwanta suka diro Yola ƙatuwar Bus cike da mutane har da masu zuwa ganin ƙwam, don kuwa izuwa lokacin Dije ta yi wata daraja da ƙima a idanuwan yan garin nasu, saboda mutumci da Safwan ya siya mata a wurinsu ba tare da ma ta sani ba, wanda ya janyo har su kansu Inna da Baffah yanzu sun zamo wasu mutane masu daraja a cikin garin na su ta sanadin hakan.

Dije murna baki har kunne saboda jin daɗin ganin ƴan'uwanta da abokan arziki a cikin gidan aurenta, sai haba haba take yi da su cikin mutuntawa tare da girmama matsayinsu a wurinta, wuri na musamman aka keɓe masu ana ta basu kulawa ta ɓangaren abinci da abinsha sai sambarka suke ta yi da sa albarka, Dije kam farin cikin fal ranta bakinta  ya ƙi rufuwa saboda ganin Abokanta na ƙurciya, waton Ladiyo Jummala da Lanti da Mune sai Hansai da ta zame mata tamkar ƴar uwa tuni, saboda auren Usmanu da ta ke yi sannan kuma ga shi tana kyautawawa Innarta shiyasa ta ke jinta ta daban a wurinta.

Mutanen garinsu Dije kam sai mamakin ganin yanda ta koma ƴargayu suke yi, don tuni ta sade da su ba zaka taɓa ganinta ka gano cewa wai tashin ƙauye ba ce, ta burgesu sosai musamman yanda ta ke nuna masu kulawa babu ƙyama bale nuna wariyar launin fata, ganin haka ne su Surayya da Zee da ita kanta Fiddon suke ta Nam nan da su su ma.

Tun ana gobe suna aka watsawa aka fara hidimar bikin don kuwa gidan cike yake fam da mutane ana ta hada hadar bikin, tsakanin soye soye da dafe dafe bayan wanda aka kai wani guri ayo ammsn duk da hakan mutane sai ɓarkowa suke yi.

Ranar suna maijego da yaronta da ya ci sunan Mahaifin Safwan ana kiranshi da Sayyid shi ma kanshi ya sha gayu bayan an ɓata lokaci wajen tofeshi da addu'o'in kariya daga sharrin mutum da na aljan, don farinshi yasa ko wa ya ganshi dole ne ma sai ya maganta, musamman yan ƙauyensu Dijen da suke ganinshi tamkar ba Dijen ce ta haifoshi ba,  saboda ganin yanda yake tamkar ɗan indiyawa saboda kyau da fari.

Dije tare da su Surry da sauran mutane sai ɗaukar photuna ake yi cen na hango wata tawagar mutane ta doso Dijen ko da na duba da kyau na hango Shaharrun marubutan nan masu ji da kansu da amfani da lokacinsu wajen farantawa al'umma irinsu

Hannah Suhana (Hajiya Duduwa)da Billy s fari Ayusher Muhammad, tare da Ummi Garkuwa, Nimcyluv, Maizafafa, Oum Mumtaz, Ummu Najma, Salaha Muhammad, sai Mmn Musaddiq, Firdausi mrs shugaba, Ameera Adam, Mmn Shaheed, Mmn Maleek, Autar manya, tare da Ummu Ja'afar.

Ganin yanayin takunsu yasa ta gano su ɗin ba ƙananun mutane ne bay yasa ta sa aka tanadar masu wurin zama na musamman, sannan ta je rungume da Sayyid tana gaisawa da su ɗaya bayan ɗaya sannan kowacensu ta gabatar mata da kanta cikin raha da wayewar kai irinta Marubutan, sannan suka dinga ɗaukar photuna da ita tare da Baby, sai ga shi na hango ana rigimar karɓar Sayyid tsakanin ƙannena biyu  Billy s fari da Hajiya Duduwa, ko wace ta na faɗin ita ce zata ɗauka sannan dai Ƙanwata Ummi Garkuwa ta raba gardamar wajen shiga tsakiyarsu ta riƙe yaron aka fara ɗaukar photuna.

Tana cikin marubutan ne Fiddo ta zo tana haki ta ce ta zo ga wasu gungun mata cen su zo suna nemanta, Surry ta ce ta je ita zata ji da su aiko ta saki jiki ta dinga lodo masu abinci da abinsha da maƙulashe ko wace ta ci ta sha sannan ta cika mas ledodinsu na kayan bikin kala kala.

Dije ta je ta sauyo wasu kayan cikin wani arnen tsadadden less wanda yaji shuwari stone ta ko'ina sai walwalniya suke yi, ta fito tana takun ƙamshi ta nufi inda ake nemanta, sai ko ga Maryam Omee ta yi saurin zuwa wurinta ta rungumeta tana faɗin

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now