63

361 28 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ruwan sharhin da kuke ta bugawa akan book ɗin nan ba ƙaramin daɗi yake sakani ba, saboda haka ku ci gaba da fafatawa ni ma in ci gaba da sambaɗo maku labarai😉😂*

*Lamba ta 63*

Tunda sassafe Surayya ta zo suka shiga kitchen sunata hidimar ɗora abincin tarbon baƙi kala kala, ko da sha biyu na rana ta yi duk sun kammala abunda ake buƙata,  Dije ta je ta sullo wankan da sai da ta ɓata lokaci sosai wajen wanke ko'ina lungu da saƙo na jikinta, tare da ɗimama kanta da turarukan wanka masu daɗin ƙamshi, waɗanda a hankali har sun fara bin jikinta saboda yanda take yawan amfani da su akai akai tun dawowarta Abuja.

Bayan ta yi SALLAHr azahar ne Surayya ta zauna ta tsara mata kwalliya cikin tsari irin na wayayyun yan birni, kafin ka ce me sai ga Dijen Baffah ta fito sharr! Abunta cikin wata rantsattsiyar shadda golden color har sheƙin maiƙo take yi, ga ɗinkin da aka watsawa shaddar na stone work shuwari stone sai walwalniya suke yi ta ko'ina idan ta motsa, sannan ga danƙareriyar sarƙarta ta gold da ta ƙara ƙawata kwalliyar, wadda Hajiya ta bata a matsayin kyautar suruka lokacin da za ta zuwa gidan mijinta, ta sha manyan awarwaro da agogo tare da Zoben azurfan da ke maƙale a yatsanta na biyu, wanda ya ƙara fito mata da zarazaran dogayen yatsunta da suka sha ƙunshin jan lalle masha ALLAH.

Dijen Baffah ta yi kyau iya kyau kamar ka saceta ka tsere saboda wankan ya hau jikinta sosai ya zauna, suka fito harabar gidan sai ɗaukar photuna suke yi ita da su Surayya da Husnah, Fiddo kam latsar wayarta kawai take yi saboda fushin da take yi na tilastata da Hajiya Mama ta yi akan sai ta zo gidan, don ta so ta yi zamanta acen gida tunda dole a cen ne zasu fara zuwa su ga Hajiyar sannan su yo nan gidan.

Shiyasa tunda ta zo ba wanda ta shiga sha'aninshi sai sabgoginta ta ke ita kaɗai, yanda ta share kowa haka duk cikinsu kowa ya shareta suna ta harkokinsu.

****

Malam Safwanu kam suna fitowa jirgi ya ja numfashi ya shaƙi iskan ƙasarshi ta Nageria da ƙarfi tare da lumshe ido ya kallo Amaryarshi da ke gefenshi cike da wani salon da shi kaɗai yasan ma'anar kallon, ganin haka ta ƙara maƙale hannunshi da take riƙe da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarshi tana murmushin itama, don on ready ko da suka sauko direba yana airport ɗin yana jiran saukarsu, shiyasa ba tare da ɓata lokaci ba ya kwasosu suka nufo unguwarsu Hajiya Mama domin su fara gaisawa kafin su je cen gidan nasu, Zee haka kawai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba tare da jin kwatakwata bata son zuwa gidansu Hajiya Mamar, saboda tunaninta ya tafi ne akan cewa Dijen tana gidan, sai dai har aka gama gaisawa da juna cikin farin ciki da ɗoki tare da murnar ganin juna bata hango ko mai kama da Dijen Baffahn ba, taji daɗi sosai a ranta saboda tunaninta har lokacin tana cen Makarantar da aka ce tana yi, shiyasa ta saki jiki sai wasar baki take yi anata gaggaisawa kafin su yi sallama da juna su fito gidan, tare da rakiyarsu Hajiyar da Aunty Ummi da yaranta da wasu ma'aikata mata da suka biyosu suna yi masu addu'ar sauka lafiya, Safwan ya kalli Hajiyar bakinshi yana rawa saboda son tambayarta da ya ke yi akan alƙawarin da ta yi masa, cikin dariya Aunty Ummi da ta fahimceshi ta yi saurin faɗin

"Mun kai maka tana cen kai take jira"

Zee da ke mota tana wasar baki ba shiri ta ji ƙirjinta ya buga, duk da ce wa bata gano ma'anar inda maganar ta dosa ba amman ta yi wasiwasin cewa

_"Anya ba wannan mayyar yarinyar ba ce ake magana a kanta ba kuwa?"_

Sai gata da haɗe fuska tana dariyar yaƙe har suka bar gidan, cike da tsananin farin da  jin daɗi Safwan ya riƙo hannunta ya ce

"Hajjaju ayi murna mun dawo ƙasarmu ta gado, sai hankali ya kwanta ga ki kusa da Daddynki da kullum kike ta faɗin kin matsu ki ganshi, tsorona ɗaya shine kada ace gulmata ce ake zumuɗin kai wa?"

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now