42

370 30 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ku yi haƙuri da rashin mayar da reply akan comments ɗinku wani lkc amman duk wanda ya yi ina group ɗin na gani duka kuma na gode sosai ALLAH ya bar ƙauna.*


*Lamba ta 41*

Inna ta yi saurin faɗin

"Haba Ladiyo wannan hali ba halin macen da tasan haƙƙin aure bane, don na tabbata ke ma kin san cewa abunda kika yi ba kyautawa bace, saboda haka sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan Mijinki, kuma ki yi haƙuri tunda har bai amince da ki zo ba, insha ALLAHu Dije zata zo har gidan naku sai ku gaisa"

Ladiyo ta miƙe tana matsar ƙwallah tace, "Don Allah Inna ki barta ta zo taje gidan kowa fa ni kaɗai ce bata zo wurina ba"

Inna tace,. "Yi sauri ki je kada ya dawo ya taradda baki nan insha ALLAHu zata zo tunda nace maki zata zo"

Ladiyo ta fice da sauri tana faɗin,. "Sai kin zo Dije ina jiranki kinji?"

Dije ta ce "kar kiji komi tunda har Inna ta bari ai zaki ganni, daman cen don ta ce kada in je ne shiyasa......"

Inna ta yi saurin buge mata baki da bayan hannunta tace,. "Shikenan ke ba za'a yi sirri da ke ba? To ni ba wai bana son ki je bane don wata manufa, tsoron nike ki je ki ɓallo muna wani aikin azo kuma ace ke ce mafari, amman yanzun ma ko da zaki je ban lamunta da inji wata mummunar maganar Bala ta shiga kunnuwan Ladiyo ba, ke shi kanshi ma ban amince da ki tankashi ba idan kin ganshi matuƙar ba gaidashi zaki yi ba"

Dije ta turo baki tace,. "Cabɗi ai WALLAHi Inna ban iya gaidashi lalle ma kam yaji daɗi nai"

Inna ta yi saurin kai mata wani mangari Dije ta miƙe cikin sauri ta bar wajen tana dariya tana faɗin,. "Wai ke Inna yanzu duk abunda Bala ya yi man baki ga laifinshi ba?"

Inna ta ce "ai mu godiya ma ya kamata mu yi masa ba muji haushinshi ba, don ke ma da kina da hankali da kin fahimci cewa hakan da ya yi taimakonki ne ya yi, don in banda shi da yanzu baki je makarantar da kike da gurin zama likitar ba"

Dije ta yi saurin faɗin

"Haka ne kuma Inna in don wannan kuma da wannan gaskiya, shege Bala shine ya ƙi yi man bayani tun farko in zo inyi masa godiya?"

Inna ta maka mata harara tace,. "Ke tafi cen sakarya sai aka ce dole shine zai yi maki bayani ba kece zaki hankalta da abun alkhairin da ya yi maki ba?, To yanzu dai gobe idan ALLAH ya kaimu kije gidan ki gayar da Duduwa har shi ma Balan ki gaisheshi ki yi masa godiya"

Dije ta washe baki tace, "aiko WALLAHi zan yi masa godiyar don na fahimci ba ƙaramin taimakona ya yi ba, yanzu ga shi ta sanadinshi na je birni na shiga makaranta idan ALLAH ya cika mani gurina shikenan sai in zama babbar Likita, kai Balan Duduwa dole ne inyi maka godiya yasin, Inna ko ma in je yanzu in dawo da wuri kafin ayi magriba?"

Inna tace,. "A'a ki dai bari sai goben yafi"

Haka ko aka yi goben tana yi bayan ta yi wankanta Inna ta ce ya saka tufafinta waɗanda suka fi kowane kyau cikin kayanta, sannan ta ɗauko kuɗi sababbi yan ɗari bibbiyu cikin waɗanda Hajiya Mama ta baiwa Dije wai ko da zata kasa idan ta buƙata,  tace da ita ta je da su ta baiwa Inna Duduwa ɗari huɗu ta baiwa Jummala ɗari shida, ta ɗauko dubu ɗaya guda biyar ta ce idan ta ga Balan ta bashi ta ce ya yi cefane, sannan ta yi masa godiya, cikin hikima Inna ta dinga koya mata yanda zata yi da abunda zata faɗa, aiko Dije ta riƙe komi a kanta tana harda.

Sai ko ga Lanti da Mune sun zo suka taka mata suna ta yaba irin kyawon da ta yi, sai taɓa lesin da ke jikin Dijen suke yi suna jinjina kyawonshi, Mune ta kasa haƙuri sai da ta ce

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now