1

415 33 2
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Jinjinar ban girma gareki HAJIYA DUDUWA mai abun mamaki🤣*

*BAK'ON YANAYI littafine mai tafe da nashi kalar salo Wanda yasha banbam da sauran littafan da kuka tab'a karantawa a duniyar littafai, kar ku Bari ayi babu ku Naira 300 kacal zata baku damar tantance gaskiyar abunda na fad'a ma ku, mai bukatar littafin ta tuntubeni ta wannan number 09032685442 sai kun zo sayen nagari mayar da kud'i gida👍🏻*

*Lamba ta 11*

Ido sama ta fara sambatunta da ta saba kullum tana fad'in,. "Ya kai dan Sarkin aljanun yankin barakutusa, ya kai yariman sunbulowa ya kai dan gidan wargaza gumurzun jadduniya, ku garzayo duka anan yau ga ranarku ta zo mu taka rawa mu juyawa bikin cin dafuwar kan mai wankan injin, ku had'a wuta ku zuba ruwa a tukunya yanzu zan tsige maku Kan in baku kuje dashi bakin ruwan tekun bangon duniya, acen zamu yi shagalinmu na yau"

Tana k'are surutan ta mik'e tsaye tana wani juya idanuwa ta zo gaban Safwan tana wani kyarmar jiki tana dalalo da miyau tana wassafa irin shakar da zata yi masa tana shakku, aikuwa dai ta yi jarumtar yin kundunbalar keta wata arniyar kuwwar tace

"Gareeeeeeeki Lugudaniya"

Aikuwa ta cafko wuyanshi iya k'arfinta ta fara yakuce masa wuyan da fuskar duka, cikin azama ya saka hannu d'aya ya fisgota ta fad'i k'asa Tim! Kai tsaya ya d'aga hannu ya kara sharara mata wani marin, Dije ta mik'e ta sake yin cikinshi da yakushi ganin zata ji masa rauni ne yasa ya nufi wani iccen dalbejiya yayi tsalle ya katso wata k'atuwar bulala, Dije kam bata daina biyarshi tana yakucinshi ba don ma da abun yayi mata dad'i har da su cizonta take Kai masa hari dashi, yana samun sa'ar saita bulalar ya ware iya karfinshi ya dinga lafta mata bulalar, tun tana juriya itama tana yin cikinshi da yakushin da cizon har ta Kai ta fasa wata k'arar dole saboda zafin bulolin da ya ke sauke mata a jiki, ba shiri ta fara fad'in cewa

"Sai mun kasheka sai mun tsige maka idanuwa, sai mun nakasa maka k'afafuwa sai mun cire maka halshe"

Safwan kam bai  daina dukanta ba har sai da yaji ta fara fad'in

"Nice Dije su sun wuce ni  ce na iso yanzu WALLAHI nice Dijengalar Baffah da Inna Hasiya, kanwar Usmanu mijin Hansai, abokiyar Ladiyo da jummala"

Gano da gaske ita d'in ce ba aljanun ba yasa ya daina dukanta ko shi sai da Lawi ya zo ya rik'e bulalar, tare da wasu malamai biyu da suka zo suna bashi hak'uri, saboda zafin kan Safwan ba mai sauk'i bane don da ace Dije tasan koshi d'in wanene da bata yi wannan wautar gareshi ba, don kam iya gaskiya Dije ta daku iya dakuwa a hannunshi, don haka ta baje k'asa tana ta tumurmusau tana kuwwar wayyo ita ALLAH ya cire mata zuciya ya karya mata hannu da k'afa saboda tsananin azabar da tasha.

Lawi ya kalleshi ganin yanda yake ta wani sauke numfashi mai cike da tsagwaron fushi da b'acin ran da ya bayyana akan fuskarshi cikin harshen turanci yace dashi,.

"Cool Dawn my man wannan fa ba Sury bace bale ka yi ta dukanta haka, idan wani abin ya sami Yar mutane zaka sakamu shiga Uku fa"

Cikin fushi tare da d'aga murya Safwan ya yi magana cikin turancinshi da ya zame masa jiki yace,.

"WALLAHI I can't tolerate any stupid nonsense from this villagers people, more especially that black cat, WALLAHI I will teach her lessons"

yana k'are fadar maganar ya bar wajen cikin k'unar rai ya nufi wani office d'in da yake da tabbacin nan ne d'akin Malamai, Lawi ya bishi da kallo ya girgiza kai sannan ya nufi inda Dije take ya ce da kawayenta su  Mune su rikata ta tashi, sai dai kowacensu tsoro ya hana su yi abunda ya sakasu saboda sanin wacecen Dijen, Lanti ce ta yi jarumtar zuwa ta rik'o hannunta tace

"Yi hakuri Dije ALLAH zai saka maki tashi muje aji za'a fara yimuna karatun"

Dije da ke kuka har lokacin iya k'arfinta ta yi banza da ita, Lawi ya k'araso wurinta yace

"Ki yi hakuri ki tashi kije class dinku za'a fara yi maku karatu"

Dije ta yi wata zabura Lanti da su Mune duka suka yi baya da sauri cikin tsoronta, ita kam tana tashi ko ta kan talkaminta bata bi ba ta nufi hanyar gida tana tafe tanata rera kukanta har ta isa Gida, tana zuwa ta fad'a d'akin Inna ta dunkule saman gado sai gurzar kuka take yi, cike da mamaki Inna take ta tambayarta lafiya? Me aka yi mata? Amman kuka yaci k'arfinta, dakyar Inna ta samu ta yi shiru sai ajiyar zuciya take yi wata bayan wata tana ciccika, Inna tabi jikinta da kallo da duk shatin bulalar ya fito rad'am a jikinta duk da kasancewarta bak'a, cikin sanyin jiki tace da ita

"Wa kika jangalo yau wanda yafi karfinki yayi maki irin wannan dukan hakan?"

Dije kam tambayar Inna tasata fashewa da wani sabon kuka tana sauke ajiyar zuciya cikin kukan tace,.

"WALLAHI Inna sai na kasheshi"

Inna ta zaro Ido waje tace,  "ke Dije ki kiyayeni kar ki janyo in k'ara yi maki wani dukan a yanzu, WALLAHI ahir dinki kada in sake jin irin wannan kalami ya fito a bakinki, ke da wa halan? me kika yi masa ya yi maki wannan dukan gashi duk ya farfasa maki jiki haka?"

Dije ta saka bayan hannu ta share hawayenta tace, 

"Wani bak'in kafuri ne cikin malaman da aka kawo Garin nan"

INNA ta zaro Ido waje tace,  " cikin bak'in Yan birnin??"

Dije ta d'aga kai tare da saukowar wasu hawayen, Inna tace

"Me kika yi masa"

Dije tace "banyi masa komi ba don kawai zan wuce naga Yana hararata na rama shikenan ya kamani yanata jibga kamar ya samu jaka, har da cewa wai Kuma har ku zai had'e ya daka yaga uban da zai hanashi a garin nan"

Inna ta yi mata wani kallon rashin yarda tace,  "ki fadi  gaskiya Dije don nasan da Baffanki ya dawo sai ya nemi jin ba'asin mafarin abun, kada kije ki sakashi jin kunya a gaban mutane"

Dije ta Fara rantsuwa tace,  "WALLAHI ALLAH har cewa yayi sai ya turo mota daga birni an rushe gidanmu, kuma ni yasa a saceni a tafi Dani birni a sayar da kaina yayi kud'i"

Inna ta zabura cikin tsoro tace,.  "To gashi Kuma kince baki yi masa komi ba, to haka kawai don kinfi kowa bak'in jini zai ce ya dakeki ke kad'ai? Akwai dai bari Baffanku ya dawo shi zai je yaji komi ai tunda ke kink'i fad'in gaskiya"

Inna ta fita ranta a b'ace da ganin dukan da aka yiwa yarta duk da zuciyarta ta bata cewa da walakin goro  cikin miya, don kuwa tabbas banza bazata kai zomo kasuwa ba, dole dai akwai abunda tayi masa ya daketan.

Aiko sai gashi kafin kace me zazzab'i ya rufe Dije saboda kukan da tasha da zugin da bulolin suke yi mata, Koda lokacin tashi Makarantar yayi Lawi dakanshi yasa su Mune suka kawoshi gidansu Dijen, domin ya zo ya baiwa Iyayenta hak'uri duk da yasan itama bata da gaskiya, amman don a Sami zaman lafiya ya zo sai dai Baffah da Usman duk basu gidan Dole  sak'o ya baiwa su Lanti su fad'awa Inna Hasiya, Ladiyo da su Jummala sunata yi masa godiya da kirkinshi da ya nuna masu a cen Makarantar, cike da jin dad'i suka shiga Gidan sai dai ganin Dije lullube tana rawar d'ari yasa duka jikinsu yayi sanyi k'alau, Inna ta washe baki tace dasu

"Yawwa Jummala ku fad'a mani me ya had'a Dije da Bakon dan birni??"

Lanti ta bayyanawa Inna komi da ya faru, sannan suka bada Jakarta da talkaminta da ta baro a aje mata, suka dubo Dijen da ke ta ta bacci sharkaf tana nishin ciyo,  kowacensu cikin tausayi ta nufi gida, Inna kam sai cisgar fad'a take yi ita kad'ai saboda ganin ashe ma Dijen ce ta janyo aka lakad'a mata irin  Wannan shegen dukan gashi ta janyowa kanta ciyo.

An fara wasar fa😹

Akafta🤾🏻‍♂️




D/AUTA CE✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now