*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Kar kuji komai allurar ƙarfi aka yi man😂😂😂😂😂shiyasa na zauce hannuna ya HAUKACE yana ta suburbuɗo maku typing, ku sha sha'aninku kawai kafin Nima in sha nawa idan allurar ta sakeni yasin😝*
*Lamba ta 49*
Dijen Baffah kam tunda ta fito ɗakinshi ta nufi ɗakinsu cikin dubarar rufe fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar da ke jikinta, ta ɗauko jakarta da kuɗin liƙinta suke ciki ta rataya, ta fito kamar wacce zata shiga wurin walimar ta fice gidan cikin sauri ta tare Napep ta haye sai babbar tasha, ta ce motar garinsu take nema aka ce da ita sai dai ta Gombe idan taje sai ta shiga motar Kano, daga cen sai ta shiga motar da zata kaita babban birnin garinsu, cikin rashin tsoro ta faɗa motar jikinta yana rawa ta tambayi kuɗin motar aka faɗa mata ta biya, da aka zo wajen rubuta suna da numbar waya kamar tasan za'a nemeta ta rubuta sunan ƙarya da numbobin banza, tunda ita ko wayar ma bata da bale ta yi number, zuwanta bai wuce minti goma ba motar ta cika suka tafi don ko da tara na dare ta buga tana garin Gombe, sai da aka je cen ne wani tsoro ya shigeta saboda batasan inda zata je ta kwana ba, ta rakuɓe gefen wata mota tana ta sharar ƙwallah saboda motar da taga za'a hau a lokacin kuma a ce wai tafiya za'a yi cikin daren, tana nan tsaye sai ga wani ɗan union ya zo yana faɗin
"Ina zaki je ne Kano ko Kaduna ko Bauchi Sokoto ko Zamfara?"
Dije ta yi saurin goge ƙwallarta tace "kano"
Yace "to zo mu je ga motocin Kano cen ina kayanki?"
Tace "babu"
Ya yi saurin waigowa yace, "bangane babu ba an sace kayan ne ko yaya?"
Ta ce "bani da kaya"
Ya ce ",to ai sai ki yi bayani yanda zan gane zo mu je kar motar ta tashi don ta kusa cika"
Dije ta bi bayanshi har inda motar take aka yi mata mazauni ta yi tsalle ta shige saboda ƙatuwar mota ce, ta sami wuri ta rakuɓe tana muzurai saboda tsoron yanda za'a bi hanyar zuwa wani gari cikin daren, zamanta ba wuya aka tada motar suka kama hanya, tafe take tana addu'ar ALLAH ya kaisu lafiya har bacci ya yi awon gaba da ita, ga masifar yunwar da ta addabeta don rabonta da abinci tun Yola.
Cikin ikon Allah Asubar farin suna isa Kano, bayan an saukesu mutane da yawa suka fara arwallah domin su yi SALLAH, itama ta bi sahun mutanen ta siyi ruwan ta yi arwallah ta yi SALLAH duk da masifar ciyon da kanta take ji, sannan ta tambayi wani ina ake shiga motar Katsina, ya yi mata jagora har zuwa inda motocin suke ta ƙara ce da shi "don ALLAH Malam ina zan samu abinci inci WALLAHi yunwa nike ji sosai" ya ce ta zo su je ya nuna mata wani shagon sayar da abinci, aiko ta bishi har zuwa wani ƙaramin shagon, yace da ita ta shiga ta zauna ta jirashi ya kawo mata abincin, ba wani tunani ta shige shagon ta zauna tana kallon mutanen da ke wulgawa ta Kofar shagon, ƴan mintuna a sai gashi ya dawo yana wata dariyar rashin gaskiya, yana zuwa ba wani jinkiri ya rufe shagon, cikin tsoro Dije ta ce
"Ina abincin ?"
Ya sosa kanshi yace
"Ki fara bani naki abincin sannan sai in je in kawo maki nawa kafin lokacin ma mai abincin ta kammala"
Dije cikin mamaki tace
"Ni ina naga abincin da zan baka?da ina da shi ai bazan tambayeka ba"
Ya yi sake yin wata dariyar shakiyanci yace
"Ke ko kike da abincin ci ki natsu kawai mu gama komi cikin lokaci kafin mutane su fara cika tashar"
Dije ta zaro ido cikin tsoro tace, "WALLAHi ko ka bani hanya in fita ko yanzun nan in yi maka sanadin barin duniya"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.