55

308 18 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Ku yi haƙuri ku yi haƙuri ni ma ba haka na so ba😢*

*Lamba ta 55*

Cikin wani sabon tashin hankali tare da kiɗimewa ya koma wurin Hajiyar, yana sanar da ita halin da Zee take ciki tare neman izininta akan komawar da yake son yi Gomben, ba tare da wata damuwa ba ta ce da shi ALLAH ya tsare, har ya fito ya dawo yana sosa kai yace

"Khadija fa? Don Allah zan bata saƙo kafin in tafi"

Hajiyar tace da shi tana ciki ya yi saurin shigewa ɗakin zuciyarshi cike da tunanin abubuwa da yawa a ranshi, sai dai yanayin da ya taradda ita ne yasa gwiwowinsa suka yi sanyi, cikin mutuwar jiki ya ja ƙafafuwanshi ya isa wurin da take kwance tana ta cisgar kuka, ya yi saurin duƙawa gaban gadon tare da ƙoƙarin ɗago fuskarta amman ta ƙi ba shi damar hakan, cikin damuwa ya ce

"Haba khadija yanzu kuma me aka yi maki?don ALLAH ki yi haƙuri ki yafe mani abunda na yi maki, Ni ma ba da son raina ba na kasa controlling kaina ne shiyasa, ban san me yasa na sake aikata maki abunda na yi ba duk da nasan zan cutar da ke, plss ki yafe mani don ALLAH, plss ki ɗago fuskarki ki ce dani kin yafe mani don ALLAH"

Dije taƙi ɗago fuskar haka ma ta ƙi daina kukanta, yana cikin magiyar ne kira ya sake shigowa wayarshi, cikin sauri ya fiddo wayar ya duba ganin Daddyn Zee ne da kanshi yasa ya yi saurin ɗagawa, cikin muryar kuka mai haɗe da tashin hankali Daddyn Zee ya ce da shi

"Don Allah ka zo ƴata zata rasa ranta a sanadinka, plss ka bi yo jirgi urgently ake buƙatar ganinka, don ALLAH ka taimaki rayuwar ƴata ka zo"

Ya ce "insha ALLAHu zan zo soon" sannan ya kashe wayar ya miƙe jkinshi yana rawa ya kalli Dije da ke ta kukanta, cikin damuwa  ya ce

"Ni zan je Gombe yanzu Khadija ki yi man addu'ar dawo wa lafiya kinji?"

Yana ƙare maganar ya duƙo da kanshi saitin fuskarta ya sakar mata da wani kiss a kumata sannan ya fice da saurinshi, daga nan inda take tana ji yo shi yana yin sallama da su Hajiyar, haka kawai ta ji kamar ta tashi ta bishi ta sanar da shi ta yafe masa, amman wata zuciyar ta gargaɗeta akan kada ta yi hakan saboda kunyar idonsu Hajiya da Aunty Ummin da ke falon, sai dai a zuciyarta ta yi masa fatar ALLAH ya dawo da shi lafiya, saboda bata fahimci ko wanene ya yi kiran nashi ba, ammsn taji rashin son tafiyar har cikin ranta.

Tana kwance ɗakin ne Hajiyar ta shigo ta yi toilet minti biyar a tsakani sai gata ta fito ta ce da ita ta biyota toilet ɗin, cikin fargaba Dije  ta miƙe ta tako a hankali saboda zafin da take ji yana ratsata, sai dai ganin fuskar Hajiyar a haɗe ya sa ta yi saurin gyara tafiyar cikin ƙarfin hali, Hajiyar ta maka mata wata uwar harara ta ce

"Ki cire komi naki ki shiga cikin ruwan nan ki buɗa ƙafafuwanki da kyau su ratsa jikinki, ki yi haka har sau uku duk kika tara ruwan kinga wannan maganin ki zuba a cikin sannan ki sake shiga, idan kuma baki yi yanda na ce da ke ba to ni zan zo da kaina in yi maki, tunda ke Kika janyo wa kanki duk abunda ya yi maki, to ai ga shi nan ya barki da jinyar jiki shi ko a jikinshi"

Cikin fushi ta fice toilet ɗin tana ta ƙananan faɗa, Dije ta bi ruwan da ke cike da bahon wankan har turirin ɗimi suke yi, amman saboda gudun ta zo ta yi matan kamar yanda ta faɗa ya sa ta yi saurin cire kayanta ta shige ruwan zafin ta zauna, ruwan suna shiga jikinta tana yarfa hannu tare da cije leɓe har suka dallashe, sannan ta fara jin ƙarfi a jikinta ta yi hakan sau uku kamar yanda Hajiya ta ce sannan ta yi wanka ta fito, sai gata tana takawa da kyau duk wani zafi da take ji ya rage sosai, bayan ta shirya ta ci abinci ne Hajiyar ta zaunar da ita ta ce

"Gobe idan ALLAH ya kaimu Ummi zata je da ke Abuja, zaki zauna a cen ki ci gaba da karatunki a cen, insha ALLAHu zata riƙeki kamar yanda na yi maki a nan, fatana kawai ke ma ki ɗauke ta tamkar yanda kika ɗaukeni, don duk da kinsani amman dole in ƙara sanar da ke cewa itace gaba da Safwan shi yake bi mata, ki yi haƙuri da duk abunda ya yi maki da sannu zai hankalta har ya dawo ya baki matsayin da nike ta yi maki fata a wurinshi, sai dai ki iya mu'amala da kowa saboda yanzu da da cen inda aka fito ba ɗaya ba, kina da aure kuma Mijinki yana sonki ko da ko bai faɗa ba, saboda ki riƙe masa amanar kanki kuma ki riƙe mutuncin aurenki, ALLAH ya baku haƙurin zama ki dage ki yi karatunki don shine gatanki ko don ke ma ki tallafi iyayenki da hannunki"

Dije ta yi shiru tana sharar ƙwallah tace   "ALLAH ya bamu haƙurin zama"

Ummi da Hajiya ta ce "Ameen"

Tun cikin daren ranar Hajiya ta haɗa mata kayanta tsaf! Asubar farin Garba ya zo ya ɗaukesu suka kama hanya sai fatan sauka lafiya ake ta yi masu, bayan tafiyarsu ne Hajiya Mama ta riƙo kunnen Fiddo ta ce

"Ke kuma WALLAHi ko da wasa na ji kin sanar da shi cewa ga inda Matarshi ta ke, to ki sani daga ranar kin bar gidan nan, don kuwa ƙauyensu Baabah Kulu zan kai ki cen ki zauna har sai an tashi aurenki a dawo da ke nan"

Fiddo ta zaro ido waje tace "Haba Hajiya wannan mugun ƙauyen? Ai WALLAHi ni ko yini ɗaya ba zan iya yi a cen ba bale har in yi rayuwa a cen tab! Mutuwa, Hajiya garin da ko toilet ba bu daji ake kashi kike so in je inyi rayuwa a cen?"

Hajiyar ta sunne dariyarta tace, "to idan ba kya so ki ceci kanki kawai a wuce wurin, amman WALLAHi duk ranar da naji kin faɗa masa inda take  to a ranar zaki bar garin nan ki je cen"

Fiddo ta yi saurin shigewa ɗakinsu tana zancen zucinta tana faɗin, "to ni me ma zai sa in faɗi inda take tunda har ma ba wani damuwa ya yi da ita ba, kuma ma ni daga ALLAH ya rabamu da ƙaya ai godiya yakamata inyi wa ALLAH ba wai faɗa masa ba, don ni har kuɗi ma zan iya badawa akan kada ya gano inda take"

Ta faɗa gadonsu cike da jin daɗi tace"ALLAH ya raka taki gona WALLAHi Ummu ta gayar da Aysha"

***

Safwan kam a kiɗime ya isa Gomben kai tsaye Asibitin ya nufa don ko Lawi bai nemi rakiyarshi ba, sai kuwa ga shi zuwan ya yi rana don kuwa ko da ya je numfashinta sama tana kiran sunanshi cikin dusashiyar muryar da ta sha ciyo na faraɗ ɗaya, mahaifiyarta da Daddynta da sauran Yan uwanta da Aminu da ƙawarta Ruma duk kuka suke yi, ganin Safwan ɗin da ta yi ne yasa ta yi saurin kiran sunanshi da ƙarfi ta some, ai kuwa ɗakin ya ɗauki kuka saboda tsammaninsu ko ta rasu, shi kanshi Safwan ɗin kwatanta tashin hankalin da ya shiga abu ne babba, saboda ganin yanda ta rame lokaci ɗaya sai karen hanci da ya fito idanuwanta duk sun zurma, hankalinshi bai kwanta ba har sai da  likitoci suka rufu a kanta tare da yin nasarar zuƙo numfashinta, cikin dawowar numfashin ne ta fara nishi sama sama tare da sauke numfashin da sauri da sauri, Mahaifin Zee ya zo gabanshi ya duƙa hawaye suna kwaranya akan fuskarshi ya ce

"Ka taimaki ƴata ta dawo cikin natsuwarta"

Aminu da ke tsaye ranshi a ɓace ya fice ɗakin, Safwan ya ɗago Mahaifin Zee ɗin ya miƙe cikin kwantar da murya yace

"Ka yi haƙuri Alhaji Insha ALLAHu ALLAH zai bata lafiya"

Muryarshi da ta ji yo yasa ta yi saurin faɗin sunanshi, Likitan ya ce ya matso kusa da ita ya bashi wuri ya matsa jikin gadon, Zee ta yi saurin riƙe hannunshi ƙam ƙam tana zubar da wasu hawayen takaicin kanta ta ce

"Me yasa ka yi man ƙarya? Me yasa ka amince da ni bayan kasan kana da matarka wadda ka fi so fiye da ko wace mace?, a hakan ka so in aureka in je inyi auren boranci? Ina sonka my man amman ka sani ko da zan mutu ba zan aureka ba, na yafe maka abunda duk ka yi mani ALLAH ya haɗa fuskokinmu a al..ja..n...n...ah"

Sarƙewar da numfashinta ya yi ne yasa ta sake somewa, Mahaifiyarta ta fashe da wani uban kuka, Ruma da ƙawarta da sauran matan da ke ɗakin suma suka kwantsama kukan, da ƙyar likitoci shawo kansu wajen fitar da su ɗakin suka dawo kan Zee ɗin suna ta aikin neman ceton rayuwarta.





Wayyo Zee Baby😢


Akafta🥰







D/AUTA CE✍🏻

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now