*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Masu comments da masu share bani da bakin godiya gareku sai dai ince ALLAH ya biyaku ya saka maku da alkhairi, naga comments dinku all kuma na gode sosai dukanku I love you gabza gabza😉*
*Special gift for you my..... HAJIYA DUDUWA Ina yinki sosai wlh💋*
*Lamba ta 19*
Lawi ya bishi da kallo har ya fice sannan yace,. "WALLAHI ka yi kad'an ka hanani abunda nike so, don son Dije cikin jinina yake kuma aurenta kamar nayi na gama don haka ka zura ido ka yi kallo"
SAFWAN ya dawo da kanshi yace,. "Ka rok'i ALLAH ma akan ka bar garin nan lami lafiya ba tare da ka janyo anyi cikin macizai ba"
Lawi ya mike ya fito shima tare da dafa kafadarshi yace,. "Stof jocking my man WALLAHI da gaske nike son yarinyar, don ALLAH ta wace hanya ka ga zanbi in shawo kan matsalar??"
Safwan da kanshi yake duk'e ya d'ago da jajayen idanuwanshi ya d'orasu kan Lawi yace,. "To be sincere Abokina wannan yarinyar ba ajinka bace, kuma kasancewar iyayenta gidadawa ne zaka sha matuk'ar wuya idan kace ala dole itace zaka aura, shawara d'aya zan baka akan ka bi komi a hankali in matarka ce zaka aureta komi tsanani kuwa, amman idan ka tsaurara to garin neman gira zaka fa rasa Ido, baka ga auren baka ga Mutuncinka da mutane suke gani a garin nan, don yanzu kafin aje ko'ina ma shi kanshi Maigarin zai ga kamar baka ji maganarshi ba, tunda har ya fad'a maka gaskiyar abunda Mahaifin yarinyar yace, tare da guje maka aibin da ke tattare da auren yarinyar"
Lawi ya yi shiru sannan yace,. "Wai Abokina ko dai sace yarinyar nan zan yi ne?, Idan muka yi aure na dirko mata ciki acen sannan in dawo masu da ita, nasan izuwa lokacin dole ne ma su hak'ura su janye tsattsauran ra'ayinsu akan kin aurena"
SAFWAN ya bishi da wani kallo baki sake yace,. "Lalle baka cikin hayyacinka to bari kaji kasan ALLAH WALLAHI duk inda ka kaita ka b'oye Ni sai na zakulota na dawowa da iyayenta 'yarsu, don tun wuri ma ka ajiye wannan bak'in kudurin naka tun kafin zuciya ta debeka ka aikata abunda daga baya zaka zo kana danasani, Ni in bancin k'ulafuci irin naka ma me aka yi aka yi wannan bak'ar magen?? Wadda ita kanta har yanzu bata san me ye duniyar ba, to kaje ka aikata duk abunda kake so tunda har ni baka d'aukeni Abokin kwarai Mai baka shawarar gari ba"
Yana kare fad'ar maganar ya tafi abunshi ya bar Lawi da tunanin zuci mai cike da neman mafita akan matsalar auren Dijen Baffah da Inna Hasiya kanwar Usmanu Mijin Hansai.
***
A bangaren Dije kuwa tsawon kwana biyu ta daina kula kowa a gidan, don Baffah yace da ita bazata sake zuwa Makarantar bokon ba, shiyasa ta k'ara shiga kunci kullum ta shige d'aki tanata kukanta har sai INNA ta fara balbalin fad'a sannan ta yi shiru, don tun tana yin banza da ita har ta fara shiga damuwa akan kuncin na Dije, don Baffah in ya fita gonarshi sai gaf da magriba yake dawowa, kuma da ya dawo yake yin arwallah ya nufi masallaci sai isha yake dawowa, sannan shigowarshi gidan ke da wuya zai fad'a wanka don ko da zai kammala sauran abubuwan tuni Dije ta yi bacci, shiyasa baya sanin halin damuwar da take yini da shi ganin hakan yasa Inna ta fara yi masa korafi akan sabon sauyin da Dijen ta shiga, cikin tashin hankali ya nufi d'akin Innar inda take ta baccinta tana sauke ajiyar zuciya, cikin tausayi Baffah ya kalli Inna yace
"Gobe idan ALLAH ya kaimu na amince ta koma Makarantarta amman da sharadin bata ba wannan yaron, idan ta amince shikenan don shima zan je in fad'awa Maigari ya ja masa kunne sosai akan 'yata, don kada in zo in saki baki ya yi mani sakiyar da babu ruwa don Yan birnin nan ba kunya ce da su ba"
Yana kare maganar ya juya zai fita cikin damuwa yace,. "Ni dai WALLAHI ALLAH banji dad'in zuwan bak'in nan garinmu ba, haka kawai muna zamanmu lafiya su zo muna da wani tsirfin tsiya"
Inna ta bishi baya cikin sanyin jiki tana k'ara zayyana masa irin kuncin da Dijen ta saka kanta akan rashin zuwanta Makarantar.
Aiko tun Asuba Inna ta yiwa Dije albishir da zuwanta Makaranta, cike da d'oki Dije ta je ta d'ora ruwan zafin wanka ta sullo wankanta tas, ta shirya cikin uniform d'inta da suke cikin rigar filonta da kullum take matashin kai da su, sunsha karin guga fess da su sai wasar Baki take yi ta nufi d'akin Baffah da ke zaune yanata laziminshi da ya zame masa jiki kullum, ta durk'usa har k'asa cikin wani sabon ladabi tace
"Ina kwana baffah"
Ya kalleta cikin jin dad'in ganin yanayinta yace,. "Lafiya Lau Makarantar za'a je ne?"
Dije ta washe baki tace,. "Eh nagode Baffah da ka yafe man WALLAHI baka ji yanda naji ba kwana biyu da bana zuwa, har mafalkin Makarantar nake ta yi"
Baffah ya tashi daga kishingidar da yake ya zauna da kyau yace,. "Idan har kina son in barki kici gaba da zuwa to ki yi man alk'awali ba ki ba sake kula Yaron nan, idan kuma kika kuskura na ji ance an ganki da shi to ko ki sani ba ki ba sake zuwa ko k'ofar Makarantar nan, in kin amince shikenan ki tashi kije idan kuma kinga ba zaki yarda da hakan ba to ki je ki cire tufafin ki yi zamanki gida tunda ba da karatun za'a tambayemu cikin kabari ba"
Dije ta yi saurin fad'in
"Na yi maka alk'awali Baffah in kuma na sab'a ka ce man shegiya"
Baffah ya yi saurin runtse idonshi yace,. "Kinga haukarki ko to kar in sake jin kin Kira kanki da suna shegiya kinji ko??"
Ta d'aga kanta alamun gamsuwa .
Akafta😝
D/AUTA CE✍🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/254073193-288-k970802.jpg)
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.