1

339 15 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*LUV U SO MUCH ALL MY FAN'S💋Ina jin dad'in yanda ku ke kaunar book din Dije K'arangiya yawanku ya kai bazan iya lissafoku ba amman ku sani ina yinku sosai all my guys👍🏻*

*Lamba ta 23*

A zabure Baffah'n ya mik'e cikin sabon tashin hankali marar misaltuwa ya nufi wurin k'anen Mahaifin Bala yana fad'in,.  "Daman shi haka sunan Balan na gaskiya yake?"

K'anen Mahaifin Bala yayi d'an murmushin yak'e yace,.  "An samu akasi ne Malam Sanda don ba da Bala aka d'aura auren ba"

Baffah'n yana jin haka ya rud'e tashin hankalinshi ya k'ara k'aruwa cikin zaro Ido waje ya nufi wurin Liman ya shak'o wuyanshi yace,. "Da wa ka d'aurawa 'yata aure ne?? mugu azzalumi ai WALLAHI sai na yi shari'a da kai matuk'ar baka yi gaggawar kwance wannan mugun auren ba"

Cikin masifa Baffah'n Dije ya shak'e Liman tare da kai masa wani azababben naushi mutane suka rirrik'eshi, kafin ka ce me wuri ya hautsine hargitsi tare da gutsuri tsoman jama'a, saboda ruwan bala'in da Baffah yake ta zubawa cikin d'aga murya yana hargowar cewa,. "Ai WALLAHI in duk garin nan za su taru a kaina bazan lamunta ba sai an kwance wannan bak'in auren da aka k'ullawa 'yata, Ni na haifeta kuma nace ba zan bada ba shin auren dole ne ko ita kad'ai ce 'ya mace a garin nan"

Kai rigima fa tun ana ganinta a wasa sai ga abu tana shirin zama Babba, don kuwa Baffah sai zillo yake yi akan sai an barshi ya daki Liman, ana cikin rigimar ne sai ga sak'o daga Maigarin ya aiko duk kowa ya hallara a k'ofar gidanshi, Baffah'n kam har kowa ya tsiyaye aka barshi shi kad'ai k'ofar gidan yanata sauke ruwan sababi, Inna da sauran matan da ke cikin Gidan suka fito sunata bashi baki.

Maigarin ya yi ta aikowa da sak'on neman Baffah'n ya kai sau uku sannan ya nufi gidan Maigarin har lokacin bai daina sambatun fad'anshi ba tamkar wani tabab'b'e sabon kamu.

Abun mamaki k'ofar gidan Maigarin cike dank'am da d'an'adam maza da mata yara da mayan, sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanda kowa yake son ya ji k'waf to hakan ba abun mamaki ba ne ba saboda ba Baffah'n kad'ai ba wasu da yawa suna son su san shin ta yaya aka haifu a ragaya?, Baffah'n da idanuwanshi da ba abunda ke cikinsu a lokacin face tsagwaron tashin hankalin da yake ciki jin yake yi gaba d'aya kowa haushi yake ba shi, yana muzurai zuciyarshi awa garwashin wuta saboda tsabar k'unar da take yi masa, ba tare da ya zauna ba ya tsaya k'ik'am yana huci tamkar wanda ke shirin kai naushi.

Maigarin ya kalleshi da kyau yace,. "Malam Sanda ka zauna wannan taron ba don kowa aka yi shi ba face donka da kuma 'yarka Dije"

Baffahn ya makawa Maigarin wata jar harara yace,.  "Me kuma zan zauna a fad'a man yanzu? wanda ya wuce muguwar kullalliyar da kuka k'ulla kuka rufeni kuka baiwa 'yata Mijin da ba Ni na zab'a mata ba???, Sai na gani da Ni da ku wa ye yake da ikon auradda ita??don ku ma sani wannan auren k'addara mai cike da bak'ar manufar tamkar an kwanceshi an gama"

Ya k'are maganar cikin huci tare da zabgawa Liman wata muguwar harara sannan ya yi  kyafci, Maigarin ya k'ara cewa da shi

"Da kasan irin ta'adin da 'yarka ta shirya idan anyi auren da wanda kake son ta aura d'in,to da baka tsaya gaban Mutane kana wannn shirmen ba, Kai godiya ya dace ace  ka yi wa Mutane  ba wai ka tsaya kana yi wa mutane karatun hauka ba"

Aiko cikin nasara maganganun Maigarin sun saka Baffah cikin shakku da tsoron abunda zai fito akan wani aikin ashsha da Dije ta aikata ko take Shirin aikatawa, saboda yasani sarai ba son auren take yi ba haka ma yasan wacece ita da ayukanta, shiyasa  cikin sanyin jiki ya ja k'afafuwanshi zuwa kusa da wad'annan manyan alhazawan bak'in fuskar ya zauna.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now