65

343 28 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Am sorry fo you my FANS😊 jiya kun ji Ni shiru ko? To ku yi haƙuri yanzu gani tare da ku😸fatana kawai ku biyoni mu je🏃🏻‍♀️*

*Lamba ta 65*

Yana ƙare maganar ya kashe wayar cikin fushi ya miƙe zai bar falon Hajiya Mama ta kira sunanshi a hankali cikin wata murya mai cike da alhini, ba shiri ya waigo ta ce da shi ya dawo ya zauna, sannan ya dawo ya zauna sai wani cika yake yi alamun a wuya ya ke sosai, Hajiya Mama ta sake kiran sunanshi ta ce

"Abunda na ce ka aikata kenan? Me yasa kai a koda yaushe baka iya dafa mutum cikin ruwan sanyi ba?, Nasan Zainab bata kyauta ba amman shi mahaifinta laifin me ya yi da har zaka yi masa wannan cin fuskar?, Yanzu idan kai ne a matsayinshi wani ya kiraka ya saki ƴarka irin haka wane irin hali kake tsammanin zaka shiga?, To bari ka ji banji daɗin abunda ka aikata ba, don Mahaifinta komi lalacewarshi ya gama maka komi tunda har ya ɗauki ɗiyarshi ya baka, don haka ka sani laifin wani baya shafuwar wani, saboda shi mutum daraja gareshi mussaman wanda ya ke sama da kai irin haka, saboda haka ka dinga kwatanta adalci akan duk wanda mu'amala ta haɗaka da shi, don da ace ka yi cuta gara ace kai ne aka cuta, don yanzu wannan abun da ka yi masa har abada ba zai taɓa mantawa ba, tabbas kam ƴarshi bata yi abunda ya dace ba amman ka sani kai ka yi abunda ya fi  wanda ta aikata muni"

Safwan da su Aunty Ummi Suka kallota cikin mamaki ta ce

"Eh tabbas haka ne don ita da makami ta yi niyya kasheka cikin fushi, kai kuka ka yi amfani da dafin harshe ka caki ubanta da mummunar maganar da dole ne ta daki zuciyarshi, ko baki ji ance dafin harshe ya fi na takobi zafi ba?, to bari ka ji yanzu wannan raunin da ta ji maka a hannu zai iya warkewa har wurin ya koma tamkar ma ba'a yi, amman dafin abunda ka yi wa mahaifinta ka sani har abada ba zai taɓa goguwa a cikin zuciyarshi ba, saboda haka ka daina yanke hukunci cikin fushi a koda yaushe idan har kasan abunda zaka faɗa ba mai kyau bane, to ka yi ƙoƙarin danne zuciyarka ka yi shiru saboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ya ce(falyaƙul khairan auliyasmut, ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru) saboda shi baki dafi ne da shi wanda idan aka yi maka wata mummunar magana har abada ba zaka taɓa mantawa da ita ba"

Safwan ya shafo kanshi da hannunshi mai lafiya ya ce "na yi kuskure Hajiyarmu kuma Insha ALLAH bazan sake maimaita kwatankwacin hakan ba...."

Kiran wayar Safwan ce ta katse maganar da yake yi, cikin sauri ya duba mai kiran sai ga shi da kallo Hajiyar cikin sauri ya ce

"Mahaifinta ne"

Hajiyarmu ta ce

"Ka ɗauka ka ji to"

Ya ɗaga ba tare da ya ce ƙanzil ba ya saka hands free, sai ga muryar Mahaifiyar Zee cikin wayar tar! tar! tana kuka tana faɗin

"Me ke faruwa ne? Me ya sami Zainab ɗin ne? ga Daddynta nan ya faɗi rai a hannun ALLAH sai sunanta ya ke kira, me ke faruwa ne na ce?"

Ta ƙare maganar cikin kuka tare da ɗaga murya Hajiya Mama ta yi masa nuni da hannu alamun ya sanar da ita, cikin sanyin jiki ya fayyace mata abunda ya faru a dunƙule, mahaifiyarta ta fasa wata uwar ƙara tare da cewa

"Innalilahi wa'Inna ilairraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa alkhalifni khairun minha"

Sannan ta kashe wayar gaba ɗaya jikin kowa ya yi sanyi, ran Hajiyar a matuƙar ɓace  cikin tagumi  ta ce "ka ga abunda nike sanar da kai ko? To idan har ka yi sanadin mutuwarshi sai kasan abunda zaka faɗawa ALLAH idan kun je lahira"

Hajiyar Mama ta miƙe cikin fushi zata fita ya yi saurin shan gabanta yana bata haƙuri tare da su Aunty Ummi, Dije ta duƙa ƙasa ta riƙo leɓen zanenta cikin kuka ta ce

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now