*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*
*Lamba ta 17*
Ba Lawi kawai ba harta Maigarin da sauran mutanen da ke wajen sai da suka furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un raji'un"
Cikin rud'ewa Maigarin yace,. "Subhanllah! garin yaya hakan ta faru?"
Dije ta mayar da kallonta ga Lawi tace,. "Gashi nan ka tambayeshi ka ji ai Wanda ya mutu a ke yi wa k'arya"
Lawi ya k'araso gabanta cikin rud'ewa tare da kid'imewa bakinshi yana rawa yace,. "Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH yaushe muka yi haka da ke?"
Dije ta galla masa harara tace, "kai ma ka fad'i tsakani da ALLAH in ba cewa ka yi ka yi kana sona ba?"
Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki tana yi masa wani kallon up and dawn, Safwan da ke tsaye yana kallonsu ba shiri ya tuntsure da wata arniyar dariya, sannan ya koma jikin motarsu ya jingina yana toshe dariyarshi da taki tsayawa.
Maigari yayi saurin fad'in, "Ina Dije"
Dije ta waigo da kallonta gareshi tace "gani"
Yace "zauna inji shin shi Lawi ta wace hanya ya bi domin ya lalataki kamar yanda kika fad'a yanzu??"
Dije ta zauna tare da lankwashe k'afafuwa tace,. "Cewa fa ya yi yana sona to Ni kuma WALLAHI billahillazi ban sonshi ku shaida don ni ban shiryawa yin ciki ba yanzu, to haka kawai ya janyo man bala'i ina zaman zamana yasa in haifo macizai su zo su kasheni a banza, to WALLAHI ban sonshi Ni kam ya ma sani tun yanzu"
Cikin k'umshe dariya Maigarin ya kalli Lawi da ke tsaye sororo ya kasa d'auke idonshi akanta saboda tsagwaron tsantsar mamakin da ta bashi, yace,. "Yarona ka zauna don inji ta yaya har hakan ta faru bayan tun farko sai da na sanar da kai gaskiya??"
Lawi ya janyo kafafunshi tamkar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya zauna tare da sunne kanshi cikin jin nauyin su Maigarin, maigarin ya sake cewa
"Me ya hadaka da Dije?"
Lawi ya sauke ajiyar zuciya yace, "WALLAHI Ni ba abunda ya hadani da ita, hasali ma Ni ko maganar da na sanar da kai har yanzu ban tab'a yinta da ita ba, kawai dai ta jahilci abun ne shiyasa"
Dije ta maka masa wata harara tace, "Ai billahillazi ka yi kad'an da ka kirani jahila ko don ka bani littafai to ai ka jira ka ga in ban maido maka da kayanka ba"
Maigarin ya dake cikin bata fuska yace,. "Ke Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH ya tab'a cewa da ke yana sonki bakinshi da naki? Ko kuma ya tab'a nuna maki wani halin rashin da'a Wanda ya danganci k'ok'arinshi na son yi maki cikin kamar yanda kika fad'a??"
Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace,. "Eh to tsakanina da ALLAH bai tab'a cewa dani yana sona ba, don ni WALLAHI ma mutuncinshi nike gani saboda naga yana da kirki, ba kamar Abokinshi da muka fara fad'a ba duk da ko shi d'in yanzu mun shirya har karatu yake koya man"
Lawi sai lokacin ya ji wani sanyi ya ratsa zuciyarshi, cikin tanbaba yace
"To ya aka yi kika ce Ina son in lalataki in yi maki ciki??"
Dije ta ce,. "To wa ya ce ka ce kana Sona??"
Yayi saurin fad'in "au! Don nace ina sonki shine zan yi maki ciki?"
Tace "Eh ai Kai ma kasan da na ce nima ina sonka dole ne inyi cikin, Ni ko don a shawo kan matsalar tun kafin faruwar hakan shine na kawoka kararka"
Cikin k'umshe dariya yace,. "Au yanzu da kince kina sona shikenan sai ki yi ciki.?"
Dije tace "Eh in ma baka sani ba to ka sani yanzu don Ni na dad'e da sanin hakan"
Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki ta kalli Maigarin tace,. "Don Allah ka yi man iyaka da shi tun kafin ya kassarani"
Maigarin gano inda ta dosa yace,. "Ai kuma tunda kince baki sonshi shikenan zance ya wuce, amman ki sani don yace yana sonki kin amince masa ba shi zai sa ki yi ciki ba, don haka kai yarona ka bata hakuri kuma a kiyaye faruwar hakan a gaba tunda dai ita tace bata sonka"
Lawi ya mike Dije ta yi saurin kallonshi tace,. "Ina zaka je kuma bayan baka bani hak'urin ba?"
Ya fuske yana saka talkamanshi yace,. "To ki taso mu je daga cen sai in baki hakurin in kina so"
Dije ta mike ta bi bayanshi har zuwa wani k'aton kututturen icce da ke gefen k'ofar gidan Maigarin ya zauna, Safwan ya bisu da kallo ya yi mere ya shige d'akinsu sai dariya yake kyakyatawa.
Dije ta yi tsaye kikam tana girgizar jiki tace,. "Bani hak'urin Ni dai in tafi inda zan je kar aga na dad'e"
Lawi ya kai kallonshi ga su Maigarin ganin basu kallonshi ya washe fuskarshi yace,. "Ai dai nasan kina son kije Makarantar gaba da primary ko?"
Dije ta saki baki sake tace, "Eh kai zaka kaini?"
Ya yi saurin fad'in
"Tabbas in har kin amince kin aureni to Ni na yi maki alk'awali Ni zan kaiki kiyi Makarantarki har ki yi degree ki zama likita kina yi wa marasa lafiya allura"
Dije ta zaro Ido cikin jin dad'i ta yi saurin zaunawa kan iccen tace, "Don Allah da gaske kake yi zaka kaini in yi likita ???"
Yace "me zai hana in har zaki aureni"
Dije ta yi shiru sannan ta ce "Ni ba Wai aurenka ne matsalata ba bana son ne ince ina sonka don WALLAHI na tsani in haifi macizai saboda tsoronsu nike ji sosai, akwai ranar da muka je daji muka ganshi WALLAHI har suma sai da na yi acen aka kwasoni aka kawoni gida"
Ta k'are maganar cikin zubowar wasu yanmatan kwallah, Lawi ya yi saurin fad'in
"To ya isa daina kuka Ni na hak'ura ko baki ce kina sona ba in dai har kin yarda zaki aureni shikenan Ni kin gama mani komi, Ni ko zan kaiki ki yi karatu har ki fito matsayin babbar likitar Mata"
Dije ta washe Baki cikin tsananin jin dad'i tace,. "Aiko WALLAHI na amince kai Ni gobe ma ayi auren muje in fara karatun Likitancin"
Lawi ya zaro Ido waje yana dariya yace,. "Masha ALLAh lalle Ni Lawi dangata ne"
Dije ta rufe fuska tace,. "WALLAHI ina son inga ina yiwa mutane allura nasan sai sunyi ta kuka"
Lawi ya tuntsure da dariya yace,. "Au to mugunta ma za ki yi ashe ba taimako ba??"
Dije tace "duka biyun ai Ni ina da tausayi wani zubin fa in naga ana kuka nima sai inji ina yi"
Lawi bakinshi a washe yace,. "ALLAHu Akbar ashe haka Dijen take da imani ban sani ba?"
Dije ta rufe fuska tace,. "Ni dai yaushe za'a yi auren in fara zuwa karatun likitar?"
Lawi ya sassauta murya yace, "to ai ke sai kin gama wannan da kike yi sai kije ta gaba sannan ki fara ta Likitar"
Dije ta zaro Ido tace,. "Cabd'i ashe abun da wahala? To yanzu ita ta gaban wannan da muke yi mi ye sunanta??"
Lawi yace,. "Secondary". Dije ta yi saurin maimatawa tace,. "Sakandari?"
Ya ce,. "Eh".
Tace "shekara nawa ake yi a gama to?"
Yace "shekara shida ce itama kamar primary"
Dije ta zaro Ido cikin sanyin jiki tace,. "Anya ko Baffahnah zai barni in yi karatun kuwa??"
Lawi cikin farin ciki yace,. "Me zai hana ke dai kawai kice masa kina son akai ki idan har ya amince ko kina cikin karatun sai a yi muna aurenmu ki je kici gaba a gidana"
Dije ta rufe fuskarta cike da jin kunya ta tashi ta zank'ara da gudu aguje ta nufi gida cikin tsananin farin ciki, Lawi ya bita da kallo yana dariyar shirmenta musamman da ya tuno da zancen zai lalatata ya yi mata ciki don ba ya da imani.
Dijelawis asha luv lfy🤣
Akafta😛
D/AUTA CE✍🏻

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
قصص عامةLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.