47

330 26 0
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*My fans bakina ba zai iya misalta farin cikin da kuka sakani ba, naso in zayyano sunayenku to amman yawanku ya kai ba zan iya lissafoku duka ba, amman na gode 🙏🏻na gode🙏🏻 sosai Alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke💃🏻ku daɗe ku yi ƙarko mutanena👍🏻*

*Lamba ta 47*

A harzuƙe ya taso da nufin kai mata duka sai ga motarsu Zee ta kunno kai harabar gidan, cikin sauri ya nufi motar yana washe baki saboda jin daɗin ganinta, Dije ta kai kallonta gareta take wani ɓacin rai ya ziyartota, amman a hakan ta kalli Lawi ta yi wani murumushi tace

"Zo mu je Malam"

Lawi ya yi shiru sannan yace da abokin nasu mai suna Kamal yace,  "zo mu je Abokina don wannan tafiyar dole ne a buƙaci rakiyarka"

Kamal kam sai kallon motarsu Zee yake yi mamaki fal ranshi yace da Lawi, "Abokina baka gane wannan yarinyar ba ne?"

Lawi ya kai kallonshi ga motar inda Safwan da Zee suke tsaye jikin motar suna fira kowanensu cikin farin cikin ganin ɗan'uwanshi, Lawi yace

"Kai ne idon gari Abokina ban gane su ba gaskiya"

Kamal ya ce, "budurwar Aminu ce fa wadda ya susuce kanta kullum yana dakon ta kammala karatun da take yi ayi auren amman Mahaifinta sai ja masa rai yake yi, ko kallon zumuncin da ke tsakaninsu ba ya yi, ya fifita son zuciyar ƴarshi akan na kowa"

Lawi yace, "Eh kam sai yanzu na tuna amman kasan ni daman bansan yarinyar ba ai labarinta kawai nake ji"

Dije tana tsaye tana saurarensu ba tare da ta ma nuna tasan wani abu da ke faruwa ba, cikin dariyar yaƙe tace

"Ai kam dai yanzu sai dai Aminu ya yi haƙuri saboda ita ce matar da Malam Safwan zai aura tare suke karatu a cen ƙasar wajen"

Daga Lawi har Kamal suka zaro ido cike da mamakin jin wannan zance a bakin Dije, haka kawai Lawi ya tsinci kanshi da cewa

"To ke har kin amince kenan?"

Dije ta yi shiru tana yar dariya mai cike da takaicin da ke cin zuciyarta tace, "ku zo mu je mu barshi ya ji daɗin firar don kada mu takurashi"

Suka wuce Safwan da hankalinshi gaba ɗaya yana kansu saboda tsabar kishin da ke cin zuciyarshi, ya bisu da kallo ranshi a matuƙar ɓace yace da Zee

"Zo mu shiga ciki ku gaisa da Hajiya"

Zee ta bishi da kallon mamakin me ke damunshi tace, "my man what's wrong with you?? Ko na yi maka wani abu ne?"

Safwan cike da ƙunar rai ya shafo kanshi ya ce

"No! no! kada kiji komi mu je kawai"

Yayi gaba Zee ta bishi da kallo ƙawarta ta riƙo hannunta suka shiga cikin gidan, suna shiga suka yi kiciɓis da Fiddo ya ce da ita ta kaisu wajen Hajiyar idan sun gaisa abasu muhalli a wajen walimar, sannan ya barosu ya nufi ɗakin baƙin da zuciyarshi take ta azalzalarsa akan ya je ya ga wace irin wainar ce ake toyawa, ai kuwa sai ko ya taradda Dijen ta gama zuzzuba masu abincin tana miƙawa Lawi lemun da ta zuba masa a cup, daga ita har shi murmushi ne kwance a kan fuskarsu, idonshi a rufe yana zuwa bai wata wata ba ya fella mata wani wahalallen mari har sai da ta saki cup ɗin saboda tsabar tsoronshi da kuma azabar da ta ziyarceta,  cikin wani masifar ƙarfi ya fisgo hannunta suka fice Kamal da Lawi suka bisu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai Lawi ya dafe kanshi zuciyarshi sai tafasa take yi saboda zafin marin da Safwan ya yiwa Dije ya ji shi har cikin ranshi.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now