*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Masha ALLAH Mutanen Dije sannunku da k'ok'arin comments all musamman wad'annan groups d'in:*
*Mata Rahama group*
*D/Auta Novel Fan's*
*Dijen K'arangiya fan's*
*TAURARI fan's 1&2*
*Fadar Ummun fareesa fan's*
*Fatima ce ko zarah fan's*
*Aseela fans group*
*Salmancy fan's group*
*Tamegari Novel fan's*
*K'aramar bazawara fan's*
*Daular Billyn Abdul*
*Kwai cikin k'aya fan's*
*Novels Arena group*
*Maman Maleek group*
*Zauren Uom Mumtaz & Zaratan Mata group*
*Dukanku all ina godiya sosai da dad'ad'an comments dinku kai har ma da wad'anda ban lissafo ba ku sani duk inda kuke HADIZA D/AUTA tana yinku all💋**Lamba ta 29*
Cike da mamakin abun Hajiya Mama ta dinga jan carbon tana kallonta har ta kammala jaye sauran 'ya'yan carbin da suka rage ta yi addu'a a gajarce ta shafa ta kalli Dije da har lokacin sai maimaita addu'ar take yi kanta a sama idonta suna kallon rufin d'akin, sai da ta bari ta kammala don kanta sannan tana k'ok'arin yi mata magana Dijen ta janyo jikinta ta k'araso gabanta ta duk'a tare da sunkuyar da kanta k'asa tace
"Ina kwana Hajiya ALLAH ya biya ya saka da gidan Aljannah ALLAH karo maku kud'i ku yi ta cin dad'inku"
Hajiya Mama da ke ta fad'in "Ameen Ameen" addu'ar Dije ta k'arshe tasa ta yi guntun murmushi sannan tace,. "Naji kin fad'i sunan Abokin Safwan Lawi shi miye dangantakarki da shi ne??"
Dije ta yi saurin gyara zamanta ta rufe ido tace,. "Shine ya so ya aureni Babana ya hana kuma bayan yace zai sakani Makaranta har in zama Likita"
Hajiya Mama ta yi shiru sannan tace,. "to ya aka yi shi Safwan aka amince ya aureki??"
Dije ta b'ata fuska tace
"Wai cewa ya yi nace Zan kashe Balan Duduwa bayan Ni WALLAHI ban tab'a cewa haka ba"
Ta k'are maganar cikin zubowar hawaye sannan caraf ta tuno da alk'awalin da Safwan ya yi mata akan cewa in tace itace ta fad'a zai sakata Makaranta, aiko ba shiri ta washe Baki tace
"Laah! Kinga na manta ashe aljanuna ne Suka fad'a ba Ni ba"
Mama ta sake zaro Ido tace,. "Aljanu gareki???"
Dije ta rufe Baki tace
"In fad'a maki gaskiya?"
Mama ta d'aga Kai ba tare da ta sami damar magana ba, Dije ta washe bakinta tace
"Tsakani da ALLAH Ni kam bani da komi amman fa ke kad'ai na fad'awa don ALLAH kar ki fad'awa kowa kinji?"
Hajiya Mama ta yi Yar dariya tace "idan har kina son kar in fad'a to sai kinyi man alk'awali ba zaki sake k'aryar aljanu ba kin amince?"
Ta yi saurin d'aga kai tare da cewa "ai dai ke Zaki sakani Makarantar Likitar ko?"
Hajiya Mama tace "in dai kina so Kuma Mijinki ya amince to Ni zan sakaki da kaina, amman sai in kin daina yawan surutu sannan duk abunda kika gani wanda Baki sani ba ki zo ki tambayeni"Dije ta ce "WALLAHI Ni nama bari daga yau idan ma kina so ki lissafaman da me da me zan dinga fad'a kullum don bana son inyi abunda zai sa ki fasa sakani Makarantar, bayan kuma ga shi Ni nike son in dinga yiwa Usmanu allura saboda kullum sai ya dakeni ya yi ta man fad'a sai kace shi ya haifeni"
HAJIYA Mama tace "ya kike da shi?"
Tace "yayana ne fa Baki ganshi ba WALLAHI mugu ne Abu kad'an sai ya dakeni don ma Baffah baya bari ya dakeni wani lokaci, amman kinga Innata WALLAHI itama baki ga dukan da take yi man ba ko tausayina bata ji, amman ai ke nasan ba zaki dakeni ba ko???"
Hajiya Mama ta sauke tagumin da ta yi tare sauke wata nannuyar ajiyar zuciya tace
"Ba zan dakeki ba amman idan kin daina rashin jin da kike fa, don ko ita Innar taki don baki barin rashin jin ne yasa ta ke dukanki"
Dije zata yi magana sai ga wata Yar aiki ta k'wank'wasa d'akin da sallamarta, Hajiyar tace ta shigo ta shigo tana yi mata Ina kwana tare da sanar da ita an kammala komi na break fast d'in, ta bata umurnin da zata bata ta fice sai ga su Surry sun shigo kowacensu da Hijabinta har k'asa suna gaidata, fiddo ta zauna tana sunne dariyarta saboda ganin Dijen ya sa ta tuno shirmen da ta yi ta bugawa jiyan, Hajiya Mama tace da su su gayar da Matar yayansu
Fiddo ta zaro Ido tace
"Haba Hajiya ita wannan yarinyar na fa girmeta WALLAHI"
Surayya ta rik'o hannun Dijen tace,. "Matar yayanmu ina kwananki dafatar dai kin tashi lafiya?"
Dije ta washe Baki tace,. "ke kam kina da kirkinki don kinfi wannan mai ido mitsi mitsin"
Fiddo ta maka mata harara zata yi magana sai ga Safwan ya yi sallama, aiko ba shiri suka mik'e dukansu za su fita cikin rawar jiki Hajiya Mama tace
"A'ah fiddo ki k'arasa maganar ai ko don......."
Fiddo ta yi saurin d'ora hannunta a baki tana yiwa Hajiya nuni da hannunta alamun ta yi shiru, yana shigowa suka gayar da shi suka fice da saurinsu ya k'araso ya zauna tare da gayar da Hajiyar.
Dije ta kalleshi tace
"Ina kwana Malam?"
Safwan ya yi banza da ita Hajiya Mama ta yi kamar bata lura ba ta k'wallawa Surry kira sai gata ta shigo cikin fargaba, Hajiyar tace da ita taje da Dije d'akinsu ta yi wanka ta nuna mata duk abunda batasani ba, sannan ta ce ta je ta d'auko mata doguwar rigar da zata saka cikin kayan da tun kafin su zo aka siyo mata su na wuccin gadi, kafin ta zo aga girmanta da yanayinta a siyo mata wasu a d'inka mata dai dai ita.
Surayya ta d'auko rigar ta ja Dijen suka fice Hajiya Mama ta kalli Safwan d'in ta sauke ajiyar zuciya tace,.
"Ya tashin bak'in??"
"Lafiya k'alau yanzu na dubosu har ma naga an Kai masu abun breakfast ai"
Ta yi shiru sannan tace,. "to sai ka yi k'ok'ari cikin kwanan nan a k'arasa gyara abunda ke b'ukatar gyara a gidanka ka kai Matarka a cen ku zauna"
Safwan ya shafa kanshi yace,. "Ta yi zamanta a nan kawai Hajiya Mama in da hali ma ta shiga cikinsu delu mai'aiki kawai su ci gaba da aikin gidan"
Hajiyar ba shiri ta zaro Ido tace,. "Me kake nufi da hakan?"
Ya yi saurin dafe kanshi yace,. "ta zama 'yar aikinki kawai Hajiya don gaskiya Ni ba Zan iya zaman aure da wannan tatsitsiyar yarinyar ba, musamman ma dai a yanda take d'in nan Tiphical Yar k'auyen nan?, Kai ina bazan iya ba gaskiya ai sai ta janyo ayi man dariya, ALLAH na tuba Hajiya me zan tsinta a jikinta Ni Kam!? astagfirullah ALLAH ya rabani da kayan takaici WALLAHI"
Not edited😕
Ayi manage plss 😍😍
Akafta🤣
D/AUTA CE✍🏻
![](https://img.wattpad.com/cover/254073193-288-k970802.jpg)
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Fiction généraleLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.