64

352 31 3
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Rigiji Gabji wani kaya sai Amalii ina gwanayen wasu ga nawa 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻har ga ALLAH ruwan sharhinku akan book ɗin Ƙarangiya yana faranta man rai ba kaɗan ba, haƙiƙa dole inyi alfakhari da ku saboda ku ɗin nawa ne ba ƙarya,ina miƙa ɗinbin godiyata gareki ƴargata Maman Sultan, irin godiyar da baki ba zai taɓa iya zayyanowa ba, alkhairin ALLAH ya kai maki har ƙasar Niger cikin gidan Baban Sultan akan gadonki wanda kike bacci a kuma gefen da kike kwanciya😝😜*

*Lamba ta 64*

A zafafe Ruma ta yi wani tsalle ta cafke ashanar cikin wani firgici da tashin hankalin da ya ziyarceta, don garin cafke ashanar fetur ɗin da ke malale ƙasa tyles ɗin ya jata ta faɗi tim! A ƙasa, amman duk da hakan sai dai ta yiwa ashanar murzar bala'i duk da zafin ƙunar da ya ratsa hannun nata, cikin fushi ta miƙe ta yo kan Zee zata ƙwace ashanar, Zee ta ƙara yin baya cikin bushewar zuciya da ta yi dacen aka janye mata imani a zuciyar don babu abunda take so irin ta ƙonesu da kowa ma da ke gidan har itama kanta, saboda a ganinta hakan ne kawai zata yi ta cire zafin abunda take ji a zuciyarta, Ruma tana girgiza kai cikin ruɗewa tace

"Kar ki aikata abunda zaki zo ki yi danasani daga baya"

Hawaye suna zuba akan fuskar Zee da idonta suka rikiɗe zuwa jajaye saboda tsallar tsagwaron bushewar da zuciyarta ta yi, ta sake kunna wata ashanar hawaye suna zuba akan fuskarta tace

"Matuƙar na barsu da rai bazan taɓa yafewa kaina ba, ya zama dole su ɗanɗani azabar mutuwa dai dai da cin amanar da suka aikata ma....."

Wani mari ne da ya sauka akan fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin guntuwar ashanar da ta kusa cenyewa a hannunta, Ruma ta yi saurin taketa da ƙafa ta murje,  a zafafe Zee ta waiga domin taga wace mai ƙarfin halin ce ta mareta, yanda ta ga fuskar Surayya da ke tsaye gefenta tana huci yasa ta yi wata gajerar dariya ta ce

"Wow sannu fa ki ce masu mutuwar yau yawa ne da su? To ki jira ke ma saura kaɗan naki ajalin ya iso ku sa da ke"

Tana ƙare maganar ta fiddo wata ƙwarar ashana kafin ta kyasta ta sake jin wani uban naushi da Surayya ta sauke mata a gefen fuskarta, ba shiri ta saki ashanar ƙasa Ruma ta ɗauke ta fice da ashanar cikin sauri, Zee ko ta yi cikin Surayya suka fara kaiwa juna duka, kafin ka ce damben bala'i ya kacame a tsakaninsu ƴan'uwan Zee ɗin su biyu da ke tsaye suna kallon abunda ke faruwa suna rabon faɗan, sai ga Husnah aguje itama kamar wata zakanya ta rufarwa Zee suka yi ta mazgarta ita da Surayya, sai dukanta suke yi kamar ALLAH ya aikosu tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta koma laƙwas Husnah ta kwashe mata ƙafafuwa ta faɗi ƙasa ba shiri, Surayya ta yi saurin haye ruwan cikinta suna ta duka duk da ƙoƙarin hanasu da ƴan'uwan Zee suke yi, amman hakan bai hanasu yi mata dukan kawo wuƙa ba.

Safwan da Dijenshi kam basu ma san me ke faruwa ba har sai da Surayya ta kirasu a waya ne take sanarwa da Safwan ɗin abunda Zee take yi don a lokacin itama suna sashen Dijen ne wani ma'aikaci ya zo aguje yake sanar da su abunda ke faruwa, shiyasa hankalin Surayya a tashe ta kira Safwan ɗin saboda zuciyarta ta bata cewa Zee ba alkhairi zata shuka ba, tun yanayin da ta ganta lokacin da suka dawo ta yi sashenta cikin fushi, bayan ta gama kiran Safwan ɗin ta sanar da shi abunda aka faɗa masu ne ta ce da su  Husnah su kira Aunty Ummi su sanar da ita kafin ta je ta ga abunda ke faruwa, aiko sai gashi tana zuwa ta ji kalaman da Zee take faɗa Shiyasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai mata hannu.

Ko da Safwan ɗin da Dije suka fito cike da firgici akan fuskarsu, sai ga wani sabon firgicin da ya sake sakasu ruɗewa saboda ganin gaba ɗaya falon warin fetur ne da wani wanda bai ƙasara bin iska ba malale a ƙasa, Safwan ya kai kallonshi inda su Surayya da ke ta jibgar Zee har lokacin, ya yi saurin katsa masu wata uwar tsawa suka zabura cikin firgici daga su har ita Zee ɗin da ke kwance ligya ligya don ta daku ba ƙarya.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now