*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅*
*Lamba ta 34*
Dije kam bayan kwana biyu ta ji sauƙi sai dai shatin bulolin da suka rage su ƙarasa warkewa kawai, inda ƙawarta Hannatu da sauran wasu da principal ɗin tasa su kula da ita sosai, sun bata kulawa tamkar ƴar uwarsu ta jini don ba ƙaramar gata tasha a hanunnsu ba, don wata prefet ma mai suna Zee Baby takanas ta maidata wurinta tana tarairayarta tamkar ƙanwarta ciki ɗaya, saboda shagwaɓar Dijen da yanayin barkwancinta yasa ta shaƙu da ita aɗan zaman jinyar da tayi clinic na kwana biyu.
Dije kam tana jin ta samu kanta ta fara komawa kan harkokinta kamar kullum, saboda yanzu ɗaurin gindin da ta samu wajen principal ɗin da sauran wasu prefet ɗin yasa take jinta ita wata ce.
A ɓangaren Malamai ma Dijen Baffah ba ɓoyayya bace, don duk malamin da ya shiga ajinsu tabbas sai yasan da zamanta, don kuwa ba laifi tana catching ɗin karatun yanda ake ɓukata.
Akwai wata rana ma wata malamar Hausa ta rubuta masu test cikin ɗoki Dijen Baffah itace ta farkon wadda ta fara gamawa ta miƙa, Malamar sai jinjina mata take yi saboda daman cen akwai jituwa tsakaninsu sosai, don saboda saurin gane karatunta da take yi kafin kowa ya gane.
Bayan an kammala ne aka haɗawa Malamar takardun ta fice wani malami ya shigo, bayan kwana biyu da rubuta test ɗin sai gashi hissar Malamar ta zagayo ta dawo, cike da ɗoki kowa yake murna saboda test ɗinsu da ta fara raba masu, wadda kusan kowa ma na ajin ya canye amman Dije cike da mamaki ta ƙurawa takardar kallo, cen dai ta kasa haƙuri saboda jin Malamar tace duk wanda yake da wani ƙorafi ya faɗa, aiko cikin sauri tace
"Malama naga nan ƙasan tambaya ta biyu kin zagaye mani baki bani marking ko ɗaya ba, gashi kuma na bada amsar karin maganar da kika ce a kawo guda biyar"
Malamar ta zo gaban desk ɗin Dijen ta tsaya ido cikin ido tace da Dijen,
"Karanto karin maganar muji me kika rubuta?"
Dije ta fara kwantawa kamar haka
"ALLAH ya kashe Uwar Ubana lafiya"
Malamar ta ce da ita
"Ƙara dubawa dai ki ga"
Dije ta sake karantawa kamar farko, Malamar tace ta dai sake dubawa da kyau aiko Dije ta ƙara ƙurawa takardar kallo tana karantawa fillah fillah tace
"ALLAH ya kashe Uwar.... Uban......ki lafiya"
Aiko ba sauran Yan ajin ba har ta ita kanta Dujen sai da ta zaro ido saboda ita har ga ALLAH ba haka taso ta rubuta ba, Malamar ranta a ɓace tace
Da sauran abokan zaman Dije wa zai riƙe mata ita?,kusan mutum huɗu ya fito yace "shi, shi," aiko cikin tsananin ɓacin rai Malamar ta kalli Dijen tace
"Daman jira nike yi ki kawo kanki Khadijah yau sai na wulaƙantaki"
Aiko jikin yan ajin yayi sanyi ƙalau saboda ganin yanda take ɗasawa da Dijen amman yau take faɗar haka, aiko Malamar ta sa aka kira sergent ya zo ta karɓi bulalarshi tace da Dije ta kwanta, cikin tsananin tsoro Dijen ta fara roƙonta akan ta yi haƙuri WALLAHI ita ba abunda ta je rubutawa ba kenan kuskure ne, aiko Malamar ta kasa sauraren magiyar da Dijen take ta kwantar da ita ƙasa flat ta dinga zuba mata buloli tun yaran class ɗin suna lissafi har suka gaji suka daina, don kuwa dukan Dijen take yi ba na wasa ba duka irin na fitar hankali har sai da Dijen Baffah ta yi suman ƙarya sannan ne ta ƙyaleta ta daina dukanta ta kwashi tarkacen kayanta ta tsallaketa ta fice.

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Ficción GeneralLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.