*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*ALHMDLLH Lalle dole ne in godewa ALLAH saboda Littafin Dije k'arangiya ya Kai in da Ni din ban isa in je ba, Na gode sosai mutanen Dije Ina yinku all dinku wallah💃🏻💃🏻💃🏻*
*Jinjinar ban girma gareki Kanwata ta gefen awazar damata waton HAJIYA DUDUWA Ina godiya da soyayyarki ga Littafin K'arangiya ALLAH ya bar zumunci tawan🥰🤝🏻*
*Lamba ta 14*
An d'auki lokaci kafin ayi nasarar dawo da numfashin Safwan dai dai, sannan aka kaishi d'akin hutu tare da makala masa ruwa in da shi yake ta barcinshi sharkaf yana ta sauke numfashi a hankali.
Daga Lawi har mutanen da suka zo da su sai a lokaciin hankalinsu ya kwanta, ganin ya dawo cikin natsuwarshi duk da har lokacin bai farfado ba, amman alamun nasarar da suka bayyana ne yasa suka ji natsuwa ta zo masu, a k'arshe dai Lawi ne ya kwana da shi su kuma suka juya suka koma kauyensu domin su sanarwa da Maigarin halin da ake ciki.
***
Dije kam ko da ta saka turaren ba gida ta yi ba lab'ewa tayi tana jiran taga ta ya abun zai kasance, aiko sai gashi tana jikin gini mak'e ta sha jinin jikinta ta fara jin yana ta dukan k'ofa, ta rufe bakinta saboda dariyar da ta sub'uce mata cike da jin dad'i ta k'ara bud'e kunnuwa domin ta ji me yake fad'a, jin yanata atishaya yasa ta fara tsallen jin dad'i ta nufi k'ofar da nufin ta bud'e katakon da ta rufe d'akin dashi ne ta jiyo takun talkami za'a zo, cikin firgici ta koma maboyarta cikin duhu ta lafe luf jikin ginin, sai dai abunda ya firgitata shine ganin an fito da Safwan rangai rangai yana wani numfashi sama sama, nan take jikinta ya d'auki rawa tare da gwalalo ido cikin tsananin tsoro ta biyo bayansu Lawi da sauran mutanen, ganin an sakashi a mota ana shawarar a kaishi Asibiti yasa ta zunduma aguje cikin tashin hankali ta nufi gidansu.
Aiko shigarta ke da wuya Inna ta fara balbaleta da fad'a akan ina ta fito cikin daren? kuma me ya fitar da ita?.
Dije ta yi tsuru tsuru tana warar idanuwa cikin tsoron abunda zai je ya dawo in har wani abin ya sami Safwan d'in, aiko ba shiri ta fashe da wani irin kukan tausayin su Innar, don tasan muddin ya mutu to daga ita har su sun shiga Uku don zaman duniyar ma sai ya gagaresu bale garin nadu, cikin Kuka ta fara fad'in
"WALLAHI Ni ban yi komi ba Inna don ALLAH ki yafe mani"
INNA Hasiya ta bita da kallo cikin duhun daren ta cafko hannunta cike da rud'ewa da jin tsoron in ba wani abu miyagun garin suka yi wa Dijenta ba, sai da ta d'auki wuk'a a kitchen sannan ta jata har kuryar d'akinta ta jefar da ita a tsakiyar d'akin, fuskarta a had'e ta nuna mata wuk'ar tace
"Zaki fad'a man abunda ya fitar da ke gidan nan ko ba zaki fad'a ba sai na kasheki an huta?"
Dije ta zaro ido tare da ja da baya tana kumshe kukanta Inna ma tana biyarta da wuk'ar zare da idanuwa kamar da gaske yankatan zata yi, Dije ta kai jikin bango ta fara kyarma tana fad'in
"WALLAHI Inna ban yi komi ba ki yarda dani"
Cikin b'acin rai Inna tace,. "Baki yi komi ba kika fita? Bayan kin San cewa Baffahnki ya hanaki fitar daren?yanzu haka ga Abincin Inna Gambo nan ajiye ina jiran Usman ya dawo ya kai mata, in da ina b'ukatar ki fitan ai sai a baki kije ki kai mata, zaki fad'a ko sai na yankaki d'in?? "
Inna ta nufota da wuk'ar saitin wuyanta Dije ta zaro Ido tare da fasa k'ara tace
"Wayyo Inna ki yi hak'uri wajen Dan birni naje na yi masa
turaren hayakin toshhi da kuka"INNA ta dafe kirji tace
"La'ilaha illallahu Muhammadur'rasulullahi Dije kashemu zaki sa ayi a garin nan ne?me yayi maki kuma ya zu da zaki yi masa turaren mayu?"
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.