*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*
*Lamba ta 9*
Dije garin kallonsu har da su tuntub'e sannan ta sami gefe ta rakub'e kamar wata ta ALLAH tana yafito su Hansai da suka saki Baki suna kallon bak'in Yan bokon, Maigarin ya karb'i wata farar takarda daga hannun wannan farin mutumen, sannan ya bud'a takardar sai kace daman cen shi d'in wani jan wuya ne a bokon, gano ko harafi d'aya bai gano maanarshi ba yasa ya mik'awa Liman takardar, shima ya duba yaga bai san komi a ciki ba ya kalli Dije yayi wata dariya yace
"Karb'i takardar nan karanta muna ita Yar gidan Baffahnta"
Dije ta ji k'irjinta ya buga dam! da shiri cikin sanyin jiki ta karb'i takardar ta Kura mata Ido kurum!tana so ta gano abunda ke ciki, don ALLAH ya taimaka da harshen hausa aka yi rubutun sai dai kasancewar ba kullum ake zuwa Makaranta a garin ba yasa ba duka hausar ta sani ba, aiko kai tsaye wani tunani ya zo mata ta d'ago kanta ta kalli Yan bokon da suma ita suke kallo, sannan ta mayar da kanta tana k'ara tantance takardar ta mik'e cikin fara'a da wata jarumta ta kalli mai garin tace,
"Sak'o ne aka aiko daga birni akan a had'a duk wasu matasa na garin nan za'a daukesu aikin Soja a turasu Maiduguri domin a kwantar da tarzoma"
Maigarin da sauran masu ruwa da tsaki da ke garin har ma da su kansu bak'in suka zaro Ido, cikin firgici Tambari ya mike jikinshi yana rawa ya kalli Babanshi yace
"Muje Baba kasan bana jin k'arfin jikina idanuwana ma ko gani basuyi sosai, watakila ma shikenan Ni da lafiyar Ido haihata haihata"
Ba shiri dayan bakon wanda ba fari ba ya kumshe dariyarshi yayi saurin cewa,. "A'a ba haka bane mu an turo mu ne daga birnin akan zamu yiwa k'asa aiki mu zauna da ku anan Garin mu dinga koyawa yara karatu har na tsawon shekara d'aya, fatanmu kawai ku bamu had'in kai don ku sani tab'amu tamkar tab'a k'asa ne, don kuwa akanmu mutum zai iya k'are rayuwarshi gaba d'aya a prison in har ya kawowa hukuma ganganci"
Maigarin da sauran mutanen da ke garin suka zaro Ido alamun tsoro, Maigarin kam sai gyad'a kanshi yake yi alamun gamsuwa da zancenshi, Dije kam tana jin haka ta fara hararar dan farin saboda ganin yanda yake ta wani cin magani yana binsu da kallon kyama, Maigarin da kowa aka yi ta yi masu sannu da zuwa da fatar nasara akan aikinsu da suka baro gidajensu suka zo kauyen da nufin su tallafa masu.
Daga nan Maigarin yasa aka je aka gyara masu masaukin da zasu zauna sannan aka yi masu iso suka fito da jakunkunansu da suka zo da su aka shigar masu da su.
Dije ta bi dan farin da wata jar harara aranta tace,.
_"jishi don ALLAH sai kace baya tsugunnin Kashi, mu za'a nunawa fari?? farin banza da wani janbaki da ya gogawa lebenshi don kitifirin bala'i"_
Shi dai Kam bai ma san tana yi ba don hasali ma shi kwata kwata hankalinshi baya wurinsu yana cen tunanin ta yaya zai iya zama kauyen har ma yayi rayuwa a cikinta?.
Bayan sun shige ne Maigarin ya dawo da hankalinshi garesu ya Kai kallonshi ga Dijen yace,. "Wai ke me yasa ba kya jin kunyar yin k'arya? Idan baki gane abunda takardar ta kunsa ba ai sai ki bari wad'anda suka sani suyi bayani yafi da ki tayarwa da mutane hankali a banza"
![](https://img.wattpad.com/cover/254073193-288-k970802.jpg)
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.