*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Masha ALLAH Mutanen Dije sannunku da k'ok'arin comments all musamman wad'annan groups d'in:*
*Ina farin cikin tayaki murnar cenye gasar da kika yi Ƙanwata waton Balkisu Muhammad Garkuwa (Ummi) ALLAH ya ƙara basira da ɗaukaka kuma ya ƙara dafa maki ga dukkan al'amurranki na yau da kullum tare da mu gaba ɗaya🤲🏻*
*Lamba ta 31*
Mai motar har ƙofar gidan Maigarin ya ajiyesu, kowane zuciyarshi cike da farin cikin nasarar dawowa gida lafiyar da suka yi, kafin kace me ƙofar gidan ta cika maƙil da yara da manya tare da wasu sauran matasan garin da suka rako motar tun daga farkon shigowa har zuwa ƙofar gidan Maigarin, sai kuwwa ake yi ana ta yi masu sannu da zuwa saboda uwar tafiyar da suka shawo.
Ba ƙaramin daɗi Maigarin ya ji ba saboda ganin karamcin da Safwan ya yi masu, don saƙonshi daban na musamman Safwan ya bada akawo mashi, don manyan riguna ne na alfarma waɗanda suka sha aiki tun daga sama har ƙasa kala biyu ya bada akawo mashi tare da turaruka masu kyau.
Shiyasa mai motar bai bar garin ba har sai da aka ciyar da shi da abinci yaci ya ƙoshi sannan ya kama hanyar komawa gida, Baffah da sauran waɗanda suka tafi kowa ya nufi gida zuciyarshi cike da farin cikin wannan tafiyar arziƙi da suka yi.
Inna Hasiya zaune ta yi ta tasa saƙon da Hajiya Mama ta bada akawo mata a gaba tana kallo, zuciyarta cike fal! da farin cikin ganin Dijenta ta yi sa'ar aure har ma da dace da suruka tagari da tayi, ba tare da ta tantance ba sai jin ta yi hawayen farin ciki suna sauka a kan fuskarta, cikin farin ciki Baffah ya ce
"Ba kuka zaki yi ba godiya ya kamata ki yi don kam tabbas Dije ta yi sa'ar aure, don ina tabbatar maki da cewa kaf faɗin garin nan namu ba wanda ya isa ya nunawa Dijeta Miji ke har ma da mutanen birnin duka, saboda ALLAH cikin hikimar ya jefo muna yaran nan don kawai su haska rayuwar Dijenmu, na yarda da maganar Inna Gambo da tace shi bawa bai san ta inda alkhairinshi yake ba, fatanmu kawai yanzu ALLAH Ubangiji ya basu zaman lafiya kuma ya ƙara masu haƙurin zama da Dijen"
Inna ta saka gefen zane ta share hawayenta cikin sanyin jiki tace,. ,"Ameen Malam amman ina jin tsoron Dije ta je ta yi abunda zai janyo girmanmu ya zube a idanunsu ka fa san halinta sarai, ko mu ya muka ƙare da ita balai Mutanen da basu san halinta ba?"
Baffah ya maka mata wata ƙatuwar harara ya ce,. "Idan kin san bakinki ba zai faɗi alkhairi akanta ba to ki yi haƙuri bana son maganar don ALLAH"
Inna ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin kwashe kayan tace
"ALLAH ya baka haƙuri ita kuma ya sa ta canza ta zama dai dai da yanda ake son kowace macen kirki ta kasance gidan Mijinta"
Ya yi saurin sakin fuskarshi yace, "Ameen ko ke fa? Haka ya dace ki ce tun farko, ba ki wai ki zauna kina ta janyo maganganun da idan aka aunasu dai dai suke da muguwar fata ba"
Inna za ta yi magana kenan sai ga Usmanu ya shigo bakinshi har kunne ya ƙaraso wurinsu yana faɗin , "Sannu da zuwa Baffah ya hanya?"
Baffah ya washe baki yace, "Alhamdulillahi Usmanu ALLAH ya nufa mun dawo lafiya tare da abun alkhairin da aka cikomu da su"
Inna ta ajiye ledar da ke hannunta tana murmushin jin daɗi, Usman sai duba kayan yake yi yana faɗin
"Kai! Kai! Kai! Lalle Baffah Dijenka ta zama hamshaƙiya waɗannan kaya haka?"
Baffah ya janyo wata ledar ya fiddo shadda da turare yace,. "Kai ma ga naka sai ka ji daɗin yi wa ƴar uwarka addu'ar zaman lafiya gidan aurenta"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Ficción GeneralLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.