*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*
*Lamba 69*
Duk da take cikin farin ciki haka ta fito ɗakin haɗe da fuska ta zo ta zauna tana shan ƙamshi tare da mayar da hankalinta ga kallon tv'n da ke ta aiki shi kaɗai, don shi kwance yake tare da rufe fuskarshi da hannu alamun yana cikin damuwa a zahiri, jin motsin shigowarta yasa ya buɗe ido yana kallonta, ganin yanayinta kuma ta ƙi kulashi yasa ya ji ba daɗi, ya miƙe zaune yana kallon yanda ta haɗe fuska tamau ba alamun wasa, cikin danne dariya ya taso ya zo gabanta ya yi tsugunno tare da riƙo hannunta yace
"Wai ke wace irin mace ce ke? Ni dai nasan kowace mace tana kishin mijinta amman ke har ingizashi kike yi akan ya yo maki kishiya"
Dije ta zare hannunta a hankali zata miƙe tsaye ya yi saurin dafeta ya ta shi ya zauna kan kujerar ya rungumota jikinshi ya ce
"Ki ji tsoron Allah kar ki jefa Mijinki a damuwa saboda macen da bata san muhimmancin kanta ba ma bale tasan na wani, kina kallo gaban idonki ta so kashemu da ma bata sami sa'a ba wuƙa ta ɗauko da nufin ta soka man, yanzu irin wannan matar kike so in sake dawo da ita cikinmu?"
Dije ta riƙo hannunshi ta ce "ba laifi bane don an yi maka laifi ka yafewa wanda ya cutar da kai, don ALLAH da kanshi haƙuri yake yi da mu da halayenmu saboda darajar fiyayyen halitta Annabinmu Muhammadu s.a.w da muke cin albarkacin shi, kuma a shirye yake da ya yafe muna a duk lokacin da mu ka yi tuba zuwa gareshi, tunda haka ne mu me zai hana mu yafe mata akan abunda ta aikata muna a baya?, Don ALLAH ka yafe don ni tuni na yafe mata ka sake bata wata dama matuƙar ka tabbatar da ingancin nadamar da ta yi "
Safwan ya sauke ajiyar zuciya yace "zan dawo da ita kamar yanda kika nema in har na tabbatar da gaske ta yi nadamar, amman da sharaɗin bata zo nan Abujar ba sai dai idan har ta amince zata zauna Yola, don bazan haɗaku waje ɗaya ba ta je ta koya maki mugun hali"
Dije ta ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarta cike da tsantsar farin ciki tace " ina sonka Mijina ALLAH ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
Ya lakuce mata hanci
"Ya ce Ameen Matata ke ma ina sonki son da Ni kaina ban san iya adadinshi ba, na godewa ALLAH da ya azurtani da samun mace irinki, wadda take da wankakkiyar zuciya mai sowa wata abunda ta sowa kanta, don ba kowa ce mace zata iya yin abunda kika yi ba, ALLAH Ubangiji ya yi maki albarka ya kuma saukeki man ke lafiya tare da Babyna"
Cike da jin daɗi take ta faɗin "Ameen Ameen Habibyna, tom kirata yanzu ka sanar da ita ta dawo ka yafe mata"
Ya maka mata wata uwar harara ya ce "su kenan ba sai an tantance ba? Ai WALLAHI sai na tabbatar da lalle ta gyaru sannan in ce ta dawo, don bazan taɓa yarda in siyowa kaina rariyar da zata yi man asarar ruwa ba"
Dije ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "uhummm har na tuna lokacin da ake yi man kashedi akanta, daɗin abun da dai komi yake wucewa don yanzu ga shi kai da kanka ka bayyana mata matsayina bayan ka gama yi mata ɓoyo, ai WALLAHI kai ma da naka laifi Malamina don da tun farko ka sanar da ita da abun bai yi tsananin irin wannan ba, don da ace ta kashemu da shikenan mun tafi bamu bar masu yi muna addu'a ba"
Ya sosa kanshi cike da jin nauyin maganar tata ya ce "Ni dai bana son tone tone idan abu ya wuce a dinga barinshi a matsayin ya wuce, ki ta so mu je dai ki ji wata magana dare ya fara tsalawa"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.