1

459 33 3
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Jinjinar ban girma gareki masoyiyata ta asali mai Sona da zuciya d'aya Yar kanawa d'iyar mutan Yola Alkharin ALLAH ya Kai maki har gadon baccinki, Ina alfakhari da samunki gareni AISHA YOLA kisani sonki cikin jinina yake ALLAH ya bar mu tare har aljannah gaba dai gaba dai tawajena makiyanki fadawanki😛*

*BAK'ON YANAYI COMPLETE ga Mai b'ukata 300 kacal Mai so ta tuntubeni ta wannan number 09032685442*

*Lamba ta 10*

Dije kam tana gudu tana haki har takai gindin wata bishiya ta fadi zaune k'asa tana sauke nishi a wahalce saboda Uban gudun da ta kwaso, Jummala ta k'araso itama tana haki ta fad'i kusa da ita tana hakin tana fad'in

"Haba Dije shine kika ki tsaya man in fa an kamani kice me?"

Dije ta kalleta Kai tsaye tace,   "Zan ce Sabida kinje ganin Yan birni ne sun kamaki kina lekonsu"

Jummala ta zaro ido waje tace,.  "To ai kece kika leka ba Ni ba don ni ban ma hangosu ba"

Dije tuno abunda ta gani yasa ta yi saurin rufe fuskarta tace,. "Ai nikam na ganowa kaina shiyasa Inna tace leke baya da amfani don garin leken sai ka ganowa kanka abunda ba shi ba ashe da gaskiyar Innata"

Jummala ta bi ta kallo mai cike da son karin bayani tace,. "Me kika gano halan?"

Dije ta runtse idonta da sauri cikin jin kunyar kanta tace,. "Kinga Jummala bazan iya tuna komi ba tashi muje gida tun kafin a gano mu ne muka lekasu idan har ya sanarwa da Maigari"

Jummala ta Mik'e jikinta yana rawa tace,. ,"Hakane fa to Ni dai Kinga na tafi ko banza tallah zan je ma  yanzu"

Jummala ta yi hanyar Gidansu Dije ta yi Gida zuciyarta sai wassafa mata Yanayin da taga Safwan d'in take yi, inda take jin kunyar kanta da kanta saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi.

Aiko haka ta kwana duk wani motsinta sai taga fuskar Safwan tana yi mata gizo yana harararta tare da yi mata kashedi da gargadi kala kala, don har Inna sai da ta gano akwai abunda yake damunta, amman da ta tambayeta tace, "wasu bak'in Yan boko suka zo garin nan zasu koya muna karatun Boko, shine na matsu Litinin ta zo mu fara zuwa Makarantar".

Inna kam sanin wacece Dije dangane da son karatun yasa ta amince, sai ko gashi ko da safiya ta waye aka yi gangami akan kowa ya taru k'ofar Gidan Maigari ana nemansu babba da yaro, aiko cikin kankanin lokaci aka hallara k'ofar gidan inda kai tsaye Maigarin yayi masu bayanin zuwansu Safwan da Lawi da dalilin da ya kawosu garin, inda yayi masu gargadi da jan kunne sosai akan tabasu da abunda zai biyo bayan hakan.

Aiko kowa jikinshi yayi sanyi duk da wasu da yawa cikin garin bokon ba damunsu yayi ba bale har su damu da wani zuwansu, don da yawa cikinsu yaransu ko Makarantar basu tab'a lek'awa ba, masu k'ok'arin zuwan ma irinsu Dije kasancewar Malamman daga wani babban garin da suke a karkashinshi ne ake turosu, saboda sun fahimci daliban kalilan ne yasa suke yin tsalle akan zuwan nasu garin kullum, don wani zubin ma sau biyu ko sau uku ne suke zuwa a sati har ta kai yaranma kansu basu zuwa Makarantar sai ranar da suka san malamman zasu zo,Dije ma tana cikin masu k'ok'arin zuwa Makarantar na sahun farko, don wani zubin ma a sanadinta wasu yara da yawa suke zuwa Makarantar don habaici da take yi masu tana yi masu gorin cewa su jahilai ne tunda har basu iya abacada ba, amman duk da hakan a class d'aya duka ba zasu wuce mutum biyar zuwa shida ba, yanzu haka aji biyar Dije take a Makarantar tare da su Jummala da su Hansai, yan ajin shida mata duka anyi masu aure mazan kuma daman cen karatun bai wani damunsu ba.

Haka Maigarin ya Kare yi masu bayanin ya gabatar da su Safwan garesu, Lawi dai kam ya saki jiki yayi masu bayani dai dai da saninsu amman Safwan kam iyakacinshi gyad'a kai yana dariyar yake, saboda shi warinsu  ma yakeji yana damunshi a gundure yake da akai k'arshe ya bar wajen.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now