*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Addu'o'inku da kullum kuke bina da su ba ƙaramin faranta man zuciya suke yi ba🥰, na gode 🙏🏻sosai Mutanena Alkhairin ALLAH ya kai maku a ko ina kuke👍🏻 muna kyawon tare🤝🏻*
*Lamba ta 56*
Likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu amman numfashinta sai sama da ƙasa yake yi, wani likita ya ce da Safwan ɗin ya yi mata magana cikin daɗaɗan kalamai, ko da ALLAH zai sa ayi nasarar ceto ranta cikin mawuyacin halin da take ciki, saboda tana sonshi idan ta ji muryarshi kuma ALLAH ya shiga cikin lamarinta aka yi dace za'a yi nasara.
Safwan riƙe da hannun Zee ɗin da har lokacin take riƙe da shi jabau!, yana hawayen tausayinta ya ce
"Plss my precious ki tashi gani a kusa da ke, ke ma kinsan ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu ke ba, plss and plss for give me i apologies for you and everything else, ki tashi ki kalleni ido cikin ido in sanar da ke a shirye nike da aurenki a kowane lokaci, kinsan na yi maki alk'awali kuma insha ALLAHu bazan saɓa ba, ki tashi ki kalli Man ɗinki ki ido cikin ido ki ce kin yafe masa plss my dream"
Ya ƙare maganar cikin wata muryar kuka saboda yanda yaga har lokacin numfashinta ya ƙi daidaita, saboda yana jin tsoron ace ƴar mutane ta mutu ta sanadinshi, ganin anƙi samun abinda ake buƙata ne yace da likitocin su bashi minti biyu, saboda sun san kan aikinsu yasa suka bashi haɗin kai wajen ficewa dukansu, Safwan ya miƙe ya yi sunkuyo saiti da fuskarta ya buɗa bakinta ya saka nashi ciki, cikin wani salo ya fara zuƙo numfashinta a hankali tare da yi mata kalamai masu sanyi tare da kiran sunayen da suke faɗawa junansu cikin wata murya mai tsada, cikin nasara Zee ta dawo hayyacinta tare da fara zubar da hawaye gefe da gefen fuskarta, sannan ta ƙura masa ido ko ƙiftawa bata yi saboda ganin take yi abun kamar almara ko a mafalki, Safwan ɗin da ko hannunta bai son taɓawa ko acen ƙasar Turai wai shine yau da tsotsar bakinta, cikin mayen sonshi da ke fisgarta ta riƙe hannunshi gam ta ce
"My man me yasa ka yaudareni?"
Ya yi saurin ɗora hannunshi akan lebenta yace, "ki bar zancen plss a shirye nike da aurenki a duk lokacin da kika tashi"
Zee ta washe baki cikin farin furucinshi ta ce, "duk da ka yaudareni amman still har yanzu ban daina sonka ba, me yasa so yake makaho ne? me yasa zuciyata ta ƙi karɓar ƙiyayyarka da na yi ta cusa mata?, Haƙiƙa ka yi nasarar samun sarautar zuciyata You are my prince chrmn and my everything shonah"
Safwan cike da tausayinta yace "na yi kuskure ki yafe mani albarkacin son da kike mani ko don ceto lafiyarki, saboda ko da ina son a yi muna auren yanzu kin ga sai an jira kinji sauƙi tukunna, don kin san ba za'a yi aure kina cikin ciwo ba"
Zee ta yi saurin share hawayenta ta yunƙura da nufin ta shi zaune amman ta kasa, dole ya riƙata ta tashi zaunen tare da taimaka mata ta jingina jikinta da filo tana binshi da kallon ƙauna, cike da jin daɗin ganin nasarar da aka samu ne Safwan ɗin ya leƙa ya kira likitocin, abun mamaki sai ga Zee sun taradda ita zaune tana share hawayenta jefi jefi.
Cikin sauri wani likita ya kira Iyayenta suka shigo cike da jin daɗin albishirin ɗin da ya yi masu, mamaki fal zuciyoyinsu saboda ganin yanda ta ke zaune har da su dariyar ƙarfin hali, dukansu har likitocin sun gasgata ba ƙaramin so Zee take yi wa Safwan ba, Aminu kanshi da ya dawo ya taradda ita zaune ana bata tea tana sha ya jinjina lamarin, take yanke ya sallamawa kanshi barin Zee ko don ta samu abinda take so, saboda a yanzu ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya yi abunda ALLAH bai tsara a cikin rayuwarshi ba, haka wani bai isa ya auri matar da ba ta shi ba, don da tuni ya aureta saboda dakon sonta da ya yi ta yi a zuciyarshi tun tana ƙarama.
![](https://img.wattpad.com/cover/254073193-288-k970802.jpg)
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Ficción GeneralLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.