1&2

585 42 0
                                        

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*

*Lamba ta 6*

Aiko mai makon taji shigowar su Inna sai taji saukar duka a jikinta, da sauri ta zabura ta fara sosa inda dukan ya sauka tana muzurai saboda ganin Yaya Usman a tsaye da bulalarshi a hannu, cikin fushi ya fara magana yana cewa

"Don Ubanki buge bugen Uban mi kike yi muna cikin dare?"
  
Dije ta zaro Ido waje tace,. "Buge buge kuma? Yaushe?"

Ya d'aga bulalar ya sake kai mata wani dukan aiko ta fasa Kara, Inna da baffa da tunda Suka jiyo sautin tafiyar Usman suka sha jinin jikinsu suna addu'a k'asa k'asa tamkar wasu sababbin larabawa, ihun Dije yasa Suka kalli Juna ba shiri Inna ta dafe k'irji tace

"Wayyo Ni Uwata wayyo Ubana Dije ALLAH ya kawo maki d'auki"

Baffah ya yi saurin kallonta yace,. " Mi kike nufi? Ai dole muje mu dubo mu ga meke faruwa"

INNA ta zaro Ido tace

"Wa? Ni! WALLAHI ka je dai nikam ba inda zanje kana jin tana zuba irin wannan ihun haka kawai ace tarko ne suka had'a man inje su tsigale man idanuwa su barni da kwarmin ido wayam ba komi"

Baffah ya maka mata wata jar harara ya fara gungurowa yana fitowa karkashin gadon, musamman kuwwar da yaji Dije tana zubawa yasashi k'ara kid'imewa ya nufi k'ofar d'akin a sukwane zai bud'e, daga cen karkashin gadon Inna tace

"Ka rufeni ta baya da kwad'o Don Allah kar ka barni a bud'e"

Baffah yayi saurin bud'e d'akin yana tofa addu'a a gaggauce saboda ihun Dijen da yak'i k'arewa, Aiko yana fitowa ya fara jiyo sautin Dije tana magiya har ya Kai bakin k'ofar ya dawo da sauri saboda sautin saukar dukan da yaji ana yiwa Dije,  sai murzar hannu yake yi yana muzurai yana sake tofa wata addu'ar, sannan yayi kundunbalar fad'awa d'akin aguje kamar an jefoshi sai gashi karaf ya hango Usman da bulalar dokinshi yanata laftar Dije, cikin tsananin b'acin Rai ya d'auke Usman da wani bahagon mari sannan ya fisge bulalar cikin fushi ya fara fad'in

"Wane rashin Imani ne ya sakaka dukanta cikin wannan talatainin dare? Me ta yi maka da bazaka bari har safiya ta waye ba ka horatan?"

Usman cikin k'unar zuciya yace,.  "Yanzu Baffah duk wannan iya shegen da take yi a cikin gidannan baka ji ba?"

Baffah ya yi saurin fad'in,. " Don naji sai Kuma aka ce maka itace mai yin abun? WALLAHI Usman ahir dinka ka kiyayi janyowa kanka abunda zai hanaka bacci mai dad'i"

Usman ya nufi hanyar fita yana fad'in,. "Duk buge bugen iskancin da tayi ta hana mutane bacci baka gani ba sai ma Ni laifina aka gani"

Cikin d'aga murya Baffah yace,. "Tunda ifrituwa ce ai dole ta fito cikin dare tana Wasa, WALLAHI in banda muke dare da yanzu sai na rama mata dukan da ka yi mata na d'aukar alhaki"

Ya dubi Dije cikin d'aure fuska yace,.  "Me ya kaiki fitowa cikin daren nan kina buge buge?"

Dije ta fara matsar kwallah tace,. "Ba fa inda naje ina tsaka da baccina mai dad'i na ji saukar duka"

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now