53

381 29 1
                                    

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*Sai kun yi haƙuri dani kwana biyun nan saboda uzurora da suka sha kaina, amman insha ALLAHu zan ƙoƙarta in yi maku ko ba yawa, sai dai ina son ku yi man uzuri idan kuka jini shiru ba ba daga gareni bane kamawa ta yi*

*Lamba ta 53*

Haka ya buɗe baki tana ta bashi ƙosan yana ci yana tuƙinshi hankali kwance yana jin kanshi cikin wani sabon nishaɗi, don ko tea ɗin ba ƙyama ba wata damuwa ya karɓa ya dinga shan abunshi, ƙarshe ma itama sai da ya tilasta mata ta ci kaɗan sannan ta buge tana ta bacci abunta, don kuwa tun tana kallon gefen titin tana ta wassfa  kunya zata ji idan ta je wurin Hajiya Mama, don sai yanzu take hango rashin dacewar abunda ta aikata, saboda ƙiri ƙiri ta haramtawa kanta tsayawa ayi bikin Surayya da ita, tana cikin tunanin ne taji wata muguwar kasala ta sauko mata a jiki, sai gata da jera hamma kala kala Safwan dai sai tuƙinshi yake yi yana kallonta ta gefen ido har baccin ya yi awon gaba da ita.

Tun daga babban birnin garinsu take ta sharara bacci mai shegen nauyi har ta kwashi kusan awa biyar bata falka ba, shima tun yana ganin baccin gajiya ne take yi har ya fara tsarguwa da baccin nata, dole da suka je wani gari ya sauka ya tada ita cikin mayen baccin suka ci abinci suka yi salloli sannan suka sake ɗibar hanya.

Tafiya tana miƙawa ta ci gaba da baccinta har suka kai Gombe bata san sun kai ba, saboda misalin sha biyun dare ne har da wasu mintuna sama suka shiga garin, daman yasa anyi masu booking ɗin wani hotel suka sauka da nufin da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola.

Shigarsu masaukin ke da wuya ya faɗa toilet ya yo wanka ya fito daga shi sai trouser yana goge ruwan da ke jikinshi da towel, ya kalleta a rakuɓe bakin gadon tana ta baccinta, cike da mamakin wannan bacci da take yawan yi ya duƙo ya sumbaci ƙwayar idonta da karan hancinta, amman ko motsi bata yi ba bale tasan me yake yi, ya saka hannu biyu ya tallafota jikinshi ta faɗo masa yaraf kuma still har lokacin baccin take yi, cikin fargaba ya ɗago fuskarta yana ƙare mata kallo sannan ya kai bakinshi cikin nata tare da jarumtar tsotso halshenta, sai gata da saurin buɗe idonta da suka yi jawur saboda baccin da ta sha ta saukesu duka a kanshi, ba shiri ta ƙwace daga gareshi tana ƙarewa ɗakin kallon sannan ta dawo da kallonta gareshi tace

"Safiya ta waye ne?"

Ya yi ƴar dariya ya ce

"Zata waye dai yanzu insha ALLAH, ki je kiyi wanka kiyo arwallah ga toilet cen ki zo mu yi sallah mu ci abinci"

Dije ta dafe goshinta saboda juyawar da taji kanta yana yi sannan ta nufi inda ya nuna mata ɗin, tsawon minti sha biyar tana toilet ɗin har sai da ya gaji da jiranta ya leƙo sai gata cikin bahon wanka tana bacci, da alama ma ko wankan ma bata fara yi ba, ya tako a hankali zuciyarshi sai nazarin dalilin wannan baccin nata yake yi amman ya kasa gano mafarinshi, ya ɗauki tsawon minti biyar tsaye a kanta yana ƙarewa cikar ƙirjinta kallo, ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya ya ranƙwafo ya saka hannu ya shafosu duka biyu ta zabura ba shiri,  tare da saurin buɗe idonta cikin firgici da tsoron ganinshi a kanta, ta yi saurin ƙanƙame jikinta tana ɓata fuska,  da wata murya mai cike da kasala tace

"Don Allah ka je ni dai yanzu zan yi wankan in fito?"

Ba shiri ya yi guntun murmushi ya yi kamar bai jita ba ya fara ƙoƙarin yi mata wankan tana zillewa, saboda inda yake son ya taɓo ta rufe da hannunta ta dunƙulewa waje ɗaya, ganin zata ɓata masa lokaci ne ya sake yin wata arwallah ya fice yana faɗin, idan bata yi sauri ta fito ba har ya dawo to shi zai yi mata wankan da kanshi, ai kuwa jin haka yasa a gurguje ta yi wankan ta fito ɗaure da towel iya cinya ta kwaso kayanta tana raɓe raɓe jikin gini.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now