*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*BAKINA YA YI KAD'AN YA NUNA DINBIN GODIYATA ZUWA GAREKU BA MASOYA BOOK D'IN DIJE K'ARANGIYA, AMMAN KU SANI INA YINKU SOSAI INA MAKU GASKIYAR SO FISABILILLAH💃🏻*
*Lamba ta 13*
SAFWAN kam cikin Bacci ya fara jin abu yana hawa jikinshi, wani jarumin beran ma cikin k'warewa da mugunta ya cafko masa farcen k'afa da k'arfi sai ga Malam Safwan a zabure tare da kwallah k'ara, idonshi suna kaiwa kan berayen ya fasa wata arniyar k'ara ya nufi k'ofar fita, sai dai mamakinshi rufe take gam gam ba alamun zata iya budewa, SAFWAN kam ya fara tsalle yana ihu Berayen suka firgice suma su ka dinga gudu suna neman maboya, wurin gudun ne wasu Suka yo kanshi aka yi sa'a wani zai hau sama ya kuskure sai gashi ya fado jikinshi, cikin firgici ya fasa wata arniyar k'ara tare da yin tsalle sai ga bera ya shige cikin rigarshi, Safwan ya ci gaba da ihu yanata tsalle har ya samu ya fito rigar da k'yar, amman duk da hakan bai daina zuba ihun ba don kafin kace me k'ofar d'akin nasu ta cika fam da dan Adam, don kuwwar da yake yi iya karfinshi ta janyo hankulan Mutane da yawa ciki kuwa har da Lawi da ke dawowa daga wajen kiran wayar da yayi da mutanen gidansu, kai tsaye aka fara k'ok'arin buge kwadon don a samu k'ofar d'akin ta bud'e, sai dai kafin ma a sami sa'ar budewa tuni Malam Safwan ya some saboda tsabar tashin hankali da firgici da tsoron da ya kamashi, don daman cen shi babu abunda yake tsoro a duniya face b'eraye, akan bera guda d'aya sai ya hargitsa d'aki kaf wajen nemanshi don kuwa muddin akwai bera a d'aki to kam sam shi bashi ba bacci a ranar har sai ya kasheshi sannan ne hankalinshi ke kwanci, to gashi yanzu ya janyo Dije ta yi masa gudunmuwa da manyan zaratan lukutayen kosashin Berayen kauyensu.
Aikuwa ko da aka samu sa'ar bud'e d'akin kwance yake a sheme tsakiyar d'akin tsilla tsillan berayen sai hawa suke yi kanshi suna ta wasa, ganin Berayen yasa Lawi firgicewa saboda yasan yanda Abokinshi yake tsananin tsoronsu, cikin zafin nama ya dauko ruwa ya kandama masa, sai gashi da sauke k'atuwar ajiyar zuciya ya mike a zabure ya fito d'akin yana ihun kiran wayyo a taimakeshi beraye zasu kasheshi.
Mutane kam sai kumshe dariyarsu suke yi ganin wai shi duk akan bera ne yake wannan firgici da tashin hankali har da su suma, Lawi kam sanin wanene abokin nashi da beran ya nufi wajenshi yana ta bashi Baki, sai dai ganin babban farcenshi na k'afa yana zubar jini yasa ya gano ba k'aramar barna Berayen suka yi masa ba, uwa uba fuskarshi da wuyanshi da ya yi jawur ga sawun yagar beran nan ya fito a jikinshi kasancewarshi farin mutum wurin yayi jawur, da kyar ya ciyo kanshi ya daina haukar da yake yi ya samu natsuwa ta ziyartoshi, ya jashi ya kaishi gindin iccen da ke k'ofar gidan Maigarin ya zaunar dashi, maigarin da sauran mutanen kowa sai yi masa sannu suke yi.
Maigarin yasa aka fito da Berayen d'aya bayan d'aya anata kashesu, amman duk da hakan Safwan kafewa yayi akan shi ba zai sake shiga d'akin ba, don ko wunin ranar ma duk a waje yayi komi saboda tsoron shiga d'akin da yake yi, lokacin da dare yayi ma Dole sai d'akin wasu samarin yaran Maigarin aka kai shi ya yi bacci, amman duk da hakan motsi kad'an zai sa ya zabura haka ya kwana zuciya ba natsuwa.
Ko da safiya ta waye tun da sassafe ya nufi Makarantarsu Dije don ko karyawa bai jira ya yi ba saboda gaba d'aya zama gidan ya gundureshi, aka yi dace itama Dijen ta yi sammakon fitowa don kusan ma itace ta biyu ko uku da zuwa Makarantar duka, tana hangoshi saman baranda kanshi duke yanata tunani ta fara kumshe dariyarta, ta yi k'ok'arin saita kanta ta isa wurinshi ta tsaya gabanshi cikin jarumta tace
"Toch me toch fire live me live dengerous your cross the bala'i kaddara your business for nown you tunani in kwakwalwarka"
Tana kare maganar ta gyara zaman Jakar fatar da ke rataye a kafad'arta ta yi masa wani kallo ta wuce fuuu abinta zuwa class dinsu, don tsoron ya sake yi mata irin dukan da yayi mata ranar, Safwan kam binta yayi da wani kallon tafi cen sakarai yana wani mere sai cen Kuma ya tuntsure da wata arniyar dariya, don a iya zamanshi garin ko Murmushi bai tab'a yi ba amman sai gashi yau da kyakyatawa kuma duk a sanadin abokiyar fadan nashi Dije, yarinyar da yake jin tsanarta har cikin zuciyarshi tsana irin wadda bai tab'a yiwa kowa irinta ba.
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.