*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Ina yabawa ƙoƙarinku COMMENTERS😉*
*Lamba ta 48*
Safwan ya bishi da wani malalacin kallo yace, "idan har ka ga ka sami damar auren khadija a dai nan wannan duniyar da muke ciki to ka ɗauka cewa bana numfashi ne a doron duniyar, sai ka jira idan har na mutun sai ka yi murna ka garzayo ka auretan, amman yanzu kam WALLAHi bazan taɓa baka damar mallakar macen da na fi so fiye da kowace mace da zan aura ba duniya, kar ka ɗauka cewa wai ka fini sonta to WALLAHi kashi ɗaya cikin goman da nake mata to ko rabi ba zaka kwasa ba, amman bazan taɓa ɗaga mata ƙafa ba matuƙar ta yi man abunda bai gamsheni ba, saboda haka ka kawar da kanka akan matata ka yi gaggawar fito da taka matar don wannan kam ta yi maka nisa, saboda na fahimci cewa idan ban fito na yi maka gwari gwari ba to zaka janyo man abunda zai saka jinina ya hawa, yanzu ga shi daga zuwanka ka firgice mani mata na kasa gano kanta"
Ya kalli Kamal yace, "Aboki ka yi masa wa'azi don ya gano kallon matar aure ma haramun ne balle ya tsaya mayar da yawu da ita yana jin daɗin zancenta, to ka zama sheda WALLAHi ya sake tsaf zan yi masa ALLAH ya isa akan matata"
Kamal yana dariya yace, "banga laifinka ba abokina saboda haka kai Malam ka tsaya iya matsayinka na malam kawai, don kaji a gabanka mijin ɗalibar taka ya kawo ƙararka"
Lawi da ke saurarensu zuciyarshi fess da jin kalaman Safwan, ba shiri wata dariya ta suɓuce masa ya kalli Safwan ɗin yace
"To kai mijin ɗalibata ka ji tsoron Allah ka riƙe man ita amana kada ka bari ɗalibata ta yi kuka matuƙar kana son inci gaba da koya mata dabarun biyayya gareka"
Safwan ya maka masa wata jar harara yace, "kar ma kasa ranka zan bari ka sake ganinta, don ba zaka sake janyo man kwaɓata yin ruwa ba"
Lawi yana dariya yace
"Kwantar da hankalinka nima na kusa angwancewa yanzu haka saura wata biyu masu zuwa insha ALLAHu"
Safwan ya yi saurin washe baki yace "ko kai fa? Ai da ka taimaki kanka gaskiya, zaman tuzururantaka ai ba daɗi ne da shi ba, ka ga ni naji daɗin daushen farko har wani sabon lambun nike son in ƙara ninƙaya a ciki"
Kamal ya yi saurin faɗin, "wai da gaske ne kai zaka auri Zee" Safwan ya washe baki yace
"Insha ALLAHu kwanan nan ma kuwa don bazan koma school ba har sai an shafa fatiha in kwashi matata mu bar maku ƙasarku"
Lawi ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce, "Abokina gaskiya zan sanar da kai wannan yarinyar da kake gani yanzu haka da mijinta da za'a haɗasu aure a gida, me zai hana ka riƙe matarka ka barta ta je ta auri zaɓin gidansu? WALLAHi ina jin tsoron haƙƙinshi ya kamaku kai da ita, don abinda ka yi mani ba kowa ne yake da sauƙin zuciyar yafiya ba, ka janye jikinka ka barta ta yiwa iyayenta biyayya ko don dakon jiranta shekara da shekaru da Aminu ya yi saboda kawai yana son aureta"
Safwan ya yi saurin faɗin, "Eh nasan da zancen amman tunda ita bata sonshi ai sai a barta ta auri wanda take so"
Lawi yace "ka dai sowa ɗan uwanka abunda kake sowa kanka yafi abokina, hadisi ne ingantacce kuma ina da tabbacin kasan da shi, saboda haka Ni ina baka shawara ne a matsayina na Abokinka idan kaji ka taimaki kanka, idan kuma ka rufe ido ka ka kasa hango gaskiya to shikenan Ni dai na fita haƙƙinka"
Safwan ya yi wata dariyar gefen baki yace, "idan ka ga ban auri Zee ba to sai in itace da kanta ta ce ta fasa aurena, saboda na riga da na yi mata alƙawari akan zan auretan duk runtsi"

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Fiction généraleLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.