*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Alhmdllh jikin Mummy ya yi sauƙi masha ALLAH, naji daɗin addu'o'inku sosai da sosai, hakan ya tabbatar man da cewa ni ma ɗin ashe kuna yi na😉, don da har na fara kishi da Dijen Baffah saboda yanda naga kuke sonta da yawa, shine na yi zaton kamar ta fini matsayi😅 ashe dai Ni ma ɗin ta ku ce ba algus tom Alhmdllh na gode sosai🙏🏻*
*Lamba ta 62*
Safwan ya bi ta da kallo baki a sake ya ce "wai ke me yasa ko kaɗan ba ki da hankali ne?, Yanzu ke ashe zaki iya kashe mutum da hannunki saboda kishi?"
Ta murguɗa masa baki tare da riƙe ƙugu tace, "kai da bakinka ka sanar da ni cewa ƴar aikinku ce, kuma daga kai har munafukar ƙanwar ta ka kun nuna man cewa ita ce ke sonka kai baka sonta, to yanzu kuma akan mi take bibiyarka? kuma sannan har ka bata damar da Ni ma da kake aure baka bani irinta ba? Ga shi ka janyo ta yi nasarar shiga tsakanina da kai, don na tabbata akanta ne kake raba daren da kake yi a waje, to WALLAHI ka ji da kyau ka ƙara ji matuƙar baka sanar da ita ta fita sha'aninka ba WALLAhi ka ji na rantse sai na watsa mata fetur na ƙoneta ƙurmus kowa ma ya huta da mugun halinta na bin Mazajen mutane, yar iskar banza baƙar karuwa ALLAH ya tsinewa iyayen da suka kawota duniya ma balle it.......... "
Saukar marin da ta ji ne a kumatunta yasa ta yi saurin haɗiye sauran maganar, cike da mamaki ta ke kallonshii hawaye suna sauka akan idonta ta ce
"My man ni ce na zama jaka a hannunka saboda matarka?, Yanzun ma kuma saboda da tsananin lalacewar akan wata ƙaramar karuwa ka ɗaga hannu ka mareni?"
Safwan ya yi saurin ɗaga hannun da nufin ya ƙara kai mata wani marin, me ya tuna kuma ya dunƙule hannun ya naushi iska sannan ya nunata da yatsa kamar zai tsole mata ido, jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsabar ɓacin ran da ta cusa masa, ya ce
"Duk ranar da kika sake kiran Matata da sunan karuwa to WALLAHIL'AZIM kin ji na rantse a ranar zaki gano ainahin wanene Safwan, don kuwa sai na yi maki dukan da a RAYUWARKI kaf ba'a taɓa yi maki irinshi ba"
Sannan ya cisgo gashinta da ƙarfin gaske ta yi ƙara fuskarshi daf da tata suna kallon juna ido cikin ido ya ce
"Wannan da kike gani ita ce Matata Khadija kuma Uwargidana wadda kike da labarin na aureta tun kafin ke, zancen Ƴar aiki ya riga da ya wuce tuni don daman cen kawaici ne na yi maki na ƙi sanar da ke gaskiyar wacece, saboda kawai bana son ranki ya ɓaci idan kin ji ina da aure, to amman yanzu tunda har kin gano komi to kenan ɓoyon da nake maki ma ba shi amfani, saboda haka ki kwantar da hankalinki zan baki wata dama"
Ya fidda wayar da key ɗin da take ya damƙa mata wayat a hannu cikin fusata ya ce "karɓi ki shiga chat ɗina da ita da kike son ganin abunda ake yi maki ɓoyo kullum, to yanzu ki shiga duk inda kike so na baki wannan damar ki karanta komi kuma ki ga komi da idonki, kin ga kin hutar da ni akan duk wani labari da zan sake ba ki a yanzu kuma da gaba ma idan ta kama, na ba ki awa biyu ki yi duk abunda kike so saboda kawai idan kin ta shi kashetan sai ki haɗa da Ni, ke in ma da hali ki fara ta kaina kafin zuwan lokacin da za ki haɗu da ita itama ki kashetan"
Yana ƙare maganar ya fice ya barta da waya a hannu baki a sake kamar wata sakarya, idonta akanshi suna zubar da hawaye wasu bayan wasu, saboda tsabar baƙin ciki da takaicin da ya cika mata ciki, cikin sauri ta jefar da wayar kan kujera itama ta durƙushe ƙasa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi.
Saboda izuwa lokacin ta fara yin nadamar biyewa son zuciyarta da ta yi ta aureshi, yanzu ga shi ba'a je ko'ina ba ta fara cin karo da takaicin auren mijin wata da ta yi, don ta tabbata inda Aminu ta aura to da babu yanda za'a ya yi mata irin wannan wulaƙancin akan wata mace, tuno irin renin hankalin da ta yi wa Aminun yasa ta ƙara sautin kukanta, don har awa biyun suka cika ya dawo bata daina kukan ba.

YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
Ficção GeralLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.