59

383 25 0
                                        

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*

*NA HADIZA D/AUTA*


*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*

*special thanks to you all my FANS😉*


*Lamba 59*

Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da janyo ƙafafuwanshi zuwa inda take sannan ya yi ƙarfin halin riƙo hannunta, cikin fushi ta ƙwace hannun tare da matsawa baya tana yi masa wani kallon mai cike da fushi tace

"Wacece wannan baƙar yarinyar da kake ambata a gabana?? Don na ce ina sonka laifi na yi da har kake ƙoƙarin baƙanta man cikin lokutana da Allah ya bani daga gareka??, Sakayyar da zaka yi man.. ke....nan?"

Ta ƙare maganar cikin sarƙewar murya tare da zuwan wani masifaffen kuka, cikin tsananin damuwa Safwan ya isa wurinta ya rungumota jikinshi, ba shiri ta faɗa ta narke masa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, cikin dakusasshiyar muryarshi da ta sha kuka ya shafo gashinta ya ce

"Don ALLAH ki yi haƙuri kinji? Insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba"

Zee ta share hawayenta sannan ta ɗago tana kallonshi tace

"Matuƙar kana son mu yi zama na jin daɗi da farantawa juna ni da kai, to ya zama dole ka nisanci duk wani abunda zai janyo muna matsala, saboda akanka wallahil'azim zan iya aikata koma menene saboda haka ka kiyayi faɗin sunan kowace shegiya a gabana, that's the first and last idan har kana son farin ciki a gidanka"

Safwan ya yi shiru yana nazarin rashin dacewar abunda ya aikata, amman duk da haka wani sashe na zuciyarshi cike yake da jin zafin baƙar da ta kira Khadijarshi, sai dai saboda sanin shine mai laifin yasa ya zare jikinshi daga nata ya nufi kan gadon ya kwanta, tare da dafe kanshi yana nazarin mafita akan matsalolin da suke son ruftowa rayuwarshi.

Cikin damuwa Zee ta bishi da kallo sannan ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tare da riƙo hannunshi ta ce

"Baka sanar da ni matsayin wannan suna da naji kake ta ambata ba tun jiya har yau, wacece ita? Saboda jikina yana bani cewa tabbas itace silar shigarka cikin wannan sabon yanayin da ka ke ciki"

Safwan ya janyo hannunta saman ƙirjinshi sannan ya ce, "ki yi haƙuri khadija matata ce asali ma itace matar da kika ji an ce da ke ina da, kuma ita ce Uwargidana a yanzu haka, amman duk da haka nan ina baki haƙuri akan laifin da na aikata kuma insha ALLAHu bazan sake ba"

A hankali ta zare hannunta cikin na shi saboda wani kuka da ya zo mata, sannan ta   miƙe cikin jarumta ta ce "bari in je  wajen su Ruma kada su ga na barsu"

Ƙanzil bai ce da ita ba har ta fice zuciyarta cike da tsantsar baƙin ciki,   tafiya take yi idonta a rufe saboda zallar tsagwaron kishin Dijen da ya rufe mata idanuwa, har ta isa sashenta bata san ma ta kai ba har sai da ta jiyo shewarsu Ruma sannan ta yi saurin share hawayenta tare da saita kanta ta shiga tana wasar baki, aiko suka yo mata caa da tsokana ko wa da abinda ya ke faɗa akanta, da kyar ta sulle ta faɗa toilet inda ta ɗauki lokaci tana ta kukanta sannan ta baiwa kanta haƙuri ta yi wankan ta fito.

Da taimakon ƙawayenta ta fesa wata arniyar kwalliya  ta ci wani danƙareren less black colour tare da ɗigon pinck a jikinshi, an mata ɗinkin half bubu ta ji aiki sosai a gaban rigar, sannan ga ɗaurin ɗankwalin da suka yi mata irin na wayayyun ƴanmata, sai gata da fitowa sharri! Masha ALLAH sai pics ake yi mata tana jin kanta wata shegiya, sannan su ka ta yi tare da ƙawayenta suna iya shegensu, duk da ita kam  ƙarfin hali ne kawai ta ke yi tana wayancewa cikinsu ana ta sharholiya.

Bayan sun yi break ne Safwan ya zo suka gaggaisa tare da yi masu godiya akan ɗawainiyar da suka yi, sai dai da yawa wasu daga cikin ƙawayen nata sun ƙyasa sosai akanshi, wasu ma har kwatantawa suke yi ina ma ace sune suka sameshi, wasu kuma suka ga gaskiyar Zee da ta nace sai shi duk cewa shi kanshi Aminun ba abun kushewa bane, amman ko kaɗan ba za'a haɗashi da Man ɗin Zee ba, saboda Safwan ƙosasshshen ingarman namiji ne cikakke mai cikar haiba ta ko'ina, saɓanin Aminu da yake siriri sosai sai dai daga ganinshi zaka gano cewa shima jarumin gaske ne.

DIJE ƘARANGIYAWhere stories live. Discover now