*💣💣DIJE K'ARANGIGIYA💣💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*ALHMDLLH ALLAH DA YA NUNA MANI WANNAN RANA HAKA MA NA GODEWA ALLAH DA HAR YA ARA MANI LOKACI YA BANI RAI DA LAFIYAR DA ZAN SAKE DORA ALKALAMINA DA SABON LITTAFINA MAI SUNA DIJE K'ARANGIYA, SAI DAI GAJEREN LABARI NE MAI CIKE DA BARKWANCI DA NISHADANTARWA HADI DA ILMANTARWA DUKA, MASOYANA A DUK INDA KUKE INA ALFAKHARI DA KU HAR MA DA MAKIYAN DUKA D/AUTA TANA GODIYA👍🏻*
*LITTAFIN DIJE K'ARANGIYA SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA UWA MA BA DA MAMA BAYA GOYA MARAYUN ALLAH, UBANGIJI YA K'ARA MAKI LAFIYA YA JA MANA DA NISAN KWANANKI INA SONKI SOSAI MUMMYTA ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA SHARRIN SHEDAN ALLAH YA SAKA MAKI DA GIDAN ALJANNAH KO ALJANNAR TA CEN CEN KOLOLUWA I LOVE YOU SO SO MUCH MUMMYTA💋💋💋👍🏻*
*Lamba ta 1*
Tafe suke su biyar kowacensu kanta d'auke da daurin ciyawar da suka debowa dabbobinsu, kowace karkashin ciyawar da ganwo a kanta sunyi d'ana tafe suke akan siririyar hanyar da ta ratsa ciyayi suna tafe suna ta firarsu suna dariya, sai dai wadda ke gabansu duka wadda tana tafe da Yar bulalarta a hannu tana dukan ciyawar da ke gefe gefen hanya tayi wata kuwwa ta fara waka tana cewa.
"ku saura ku ji Yau fa in naga dama"
Dukansu Suka had'a baki da kalar wakar da tayi wajen fad'in cewa
"Dije k'arangiya yau kuma wacce kika k'ullo?"
Wadda aka kira da Dijen ta yi tsalle har sai da ciyawarta ta so fad'uwa ta tare da sauri cikin wakar tace,.
"Rumfar mai gari yau nike so mu je mu tarwatsa"
Hansai ta zaro Ido waje bakinta yana rawa tace,. "WALLAHI nikam Dije babu ruwana haka kawai mu je mu d'auki alhakin mutane a banz......"
Dije cikin zafin nama ta kaiwa bakinta faka tace, "ware anan tun kafin yau Inna Meramu ta yi maki tuwon k'asa, kuma WALLAHI kika kuskura na ji kin fad'i maganarnan sai na darje maki baki yayi jini"
Sanin halin yasa Hansai ta yi saurin yanke hanyar ta barsu anan tana yi tana waigen Dije don kar ta biyota ta jibgeta a banza, don ta santa sarai wannan k'aramin aikinta ne, Dijen ta kalli sauran abokan nata ta ajiye ciyawarta ganin haka yasa dukansu suka ajiye tasu, Dije ta saka bulalar dake hannunta ta daki d'aya daga cikin kawayen nata tace,
"Ke kuma Lanti in kinsan cewa bak'in halinki zaki nuna har kisa a gano Shirinmu ba gaske bane ba to ki tafi gida kawai zamu k'araso"
Lanti jikinta yana rawa ta marairece tace,. "A yi dani kawai ba Zan bari a gano ba"
Dije ta kalli sauran ta kyalkyale da dariya sannan ta janyo kansu ta had'e waje d'aya ta fara rada masu kus kus a kunne, gaba d'aya suka tuntsure da dariya Mune tana dariya ta ce,.
"Har na hango yanda maigari zai ....."
Dije ta yi saurin buge mata baki tace,. "To tonanna tonamu aji tun kafin muje cikin garin"
Aiko ba shiri Mune ta yi gum tana fiki fiki da ido daga nan Dijen tace da kowa ya shirya da sunje bakin garin zasu fara shirinsu, aiko Suka k'ara d'aukar ciyawarsu Suka dora akai suna tafe suna dariya har daf da shiga cikin garin Suka fara koyon K'ugin kukan Kura sannan dukansu suka ciccire talkaminsu suka sagala a hannuwa Dije ta fara dafe ciyawarta ta zankara aguje tana K'ugin kura tana kuwwa tana fad'in
"wayyoo Kura! kura a garinmu ku yo agaji gata nan shigowa garin daf take damu ta kusa k'araso"
Aiko sauran kawayenta suma Suka dafe mata baya suna K'ugin suna ihun ga kura nan ta shigo gari, Mutane tun da suka fahimci abunda suke fad'a Suka fara gudun ceton Rai Dije da kawayenta aguje har fadar Mai Garin don tun daga nesa da Suka jiyo sautin kukan Kuran suka natsu musamman da suka ji abunda take fad'a sai ga dandalin ya fara watsewa, saboda ganin yanda suke gudu a bala'e suna haki suka Fara gasgata lamarin, sai mutum biyu aka bari a wajen sai ko ga su sun k'araso tana haki tace da su
![](https://img.wattpad.com/cover/254073193-288-k970802.jpg)
YOU ARE READING
DIJE ƘARANGIYA
General FictionLabarine mai cike da barkwanci tare nishandarwa da fadakarwa a fakaice don kuwa zai saka mai karantashi ya ƙyaƙyata har ma ya faɗo kan gado ba tare da ya san yayi ba saboda dariya zai saka mutumcikin farin ciki marar misaltuwa.