01

12.7K 644 43
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

     *Haske writers Association*
Home of expert and perfect writers

_Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki_

*01*

   *GARIN KANO*

Hadari ne ya gauraye sararin samaniya, Garin yayi duhu, Ruwa zai iya sauka a kowane lokaci, Tsaye take jikin k'ofa tana jiran saukar ruwan, Yarinya ce yar' kimanin shekara 12, Fara ce tass, kamar ka tab'a jini ya fito, Gashin ta a fake, ya zuba har gadon baya, Kallo d'aya zaka mata kasan buzuwa ce, Daga kayan jikin ta zai tabbatar maka iyayen ta ba masu k'arfi bane.

    Saukar ruwa sama, ta buga tsalle ta fad'a ciki, Ruwa na sauka kanta, Tana wak'a da juyi, hakan na cikin hobby d'inta, Ba k'aramin nishad'i take tsintar kanta ba a duk lokacin da ake Ruwan sama take wasa ciki.

     "FETTA! FETTA!"(Na nufin Fatima da yaren buzaye), Taji muryar mahaifin ta na kira, " Ba zaki fito cikin ruwa ba sai mura ta kama ki", Ya fad'a da hausar sa da bata kama baki ba,

    Wasanta ta cigaba da yi kamar bata ji sa ba, Sai da ruwan ya tsagaita, Ta nufo k'aramin d'akin su, wanda ko ba'a fad'a maka ba, na masu gadi ne.

    Rawar sanyi take, ruwa na d'iga daga jikin ta, Mahaifin ta ya kalleta yace "Son wasan ruwa kamar yar' ruwa", Tayi dariya tana tub'e kayanta, Ta shanya su a jikin k'ofa, Ta d'auko wata tsohuwar rigar atamfa, wacce yaran masu gidan ne suka bata, Ta saka, Ta kwanta kan yar' yoluluwar katifar ta, Taja bargo da duk ya tashi tsabar tsufa ta lullub'e.

   Garwashi ya had'a, Ya d'auko k'aramar butar su ta had'a shayin ataye, Ya zuba garin, Ya tafasa, Ya sauke, Ya tache, Ya zuba a k'aramin k'ofi guda uku, " FETTA tashi ki mik'awa Hajiya, shayin Alhaji ki dawo ki sha naki", "Toh Addani"(Yana nufin Baba), Ta fad'a tana mik'ewa,

   Ta karb'a ta nufi cikin gida, a bakin k'ofar kitchen taci karo da Yasmin yarinyar masu gidan, " FETTA ya aka yi?", Ta fad'a da sakin fuska, "Shayin Baba ne na kawo", Ta mik'a mata ta karb'a, Ta koma d'akin su.

    Shayin ta zauna tana sha, sai da tasha kofi uku, tana tsananin son ataye, " Addani waya koya maka had'a shayin nan?", "Al'adar garin mu ce", " Sai yaushe zamu je?", "Ba yanzu ba", " To yaushe zaka bani tarihin mu?", "Sai kin k'ara wayo", Yana fad'ar haka ya mik'e ya fita, Baya son yawan tambayoyin da take mishi.

  FETTA tun da tashi bata san kowa ba sai mahaifin ta, tun tana shekara biyu Allah yayi ma mahaifiyar ta rasuwa, Maciji ya sare ta, A gidan nan ta tashi taga suna rayuwa, mahaifinta matsayin mai gadi, Yana tsananin son ta, Baya son b'acin ran ta ko kad'an, Duka rayuwar shi ya sadaukar a kanta, Ko albashi aka bashi, Ita yake kashewa kud'i, Idan bata da lafiya, tsananin rud'ewa yake, Ya shiga tashin hankali.

    Bata had'a mahaifin ta da kowa ba, Tana tsananin k'aunar sa, Makarantar gwamnati take zuwa nan kusa dasu, Tana da tsananin son karatu, Makarantar ba'a wani koyar dasu abun arzik'i, Wataran har suje su dawo ba malamin da ya shiga aji (Hmm Yayan talaka na ganin rayuwa)

    D'umamen tuwo suke ci, wanda aka aiko musu daga cikin gida, A kwano d'aya suke ci, " Kiyi sauri FETTA, lokaci na k'urewa", "Ko naje da wuri sai kaga har k'arfe 10 malami bai shigo ba, watarana ma haka zamu je mu dawo ba'a koya mana komai ba", " Gwamnatin ce sai dai muce Allah ya sawwak'a amma komai k'ara lalace yake", "Addani, idan na girma nayi kud'i, Zan gina mana k'aton gida mu tashi daga wannan, na siyan maka mota irin ta Alhaji", Yayi dariya yace " Allah ya yarda ya'ta", Kullum maganarta kenan, Tayi kud'i ta kula da mahaifin ta.
      
  K'arfe 8 ta fito, Sanye da Uniform da silifas, da jakarta ta buhu, Tana gani yaran gidan suka fito sanye da uniform d'in su masu kyau, da socks da sandal, kowanne ya rataya school bag, Suka shiga mota, Direba yaja su.

    Ta kalle su cike da burgewa, Ta gyara hijabin ta, Ta fita gate ba tare da ta damu ba, Tana ta yan wak'e wak'en ta na k'asar nijar, wanda mahaifin ta ne ke yawan kunnawa, har ta isa makaranta.

   Yau anci sa'a malamai har biyu sun shigo ajin su, Ana buga k'arrarawar tashi, Ta sab'i jakarta ta taho gida, bata da k'awaye, ita kad'ai ke yawon ta, Duk da cewa da yawa yan makarantar na son k'awance da ita, saboda kyanta.

    Bakin gate ta tarar da Mahaifin ta zaune, Yana sauraren radio, Ta gaishe shi, Ya amsa, Yace "An dawo?", " Eh Addani", "Toh ki shiga ciki, abincin ki na nan"

    Jakarta ta ajiye, ko uniform bata cire ba, ta bud'e kwanon abincin, Ta kwaso yunwa, Ba'a tab'a abincin ba, Wanda haka ke nuna bai ci ba, Baya tab'a cin abinci, sai taci ta rage ko su ci tare, ko rabi bata ci ba, Ta k'oshi, Ta rufe saura, Ta d'ibi ruwa a randa dake bakin d'akin su ta sha.

  Sam bata shigewa yaran gidan, Kullum tana d'akin su, sai idan mahaifin ta aike ta yayi, Waje ta fita wurin shi, Tana bashi labarin abunda ya faru makaranta yau.

      Dare ne ya tsala, gari yayi duhu, Hasken fitilun gidan ne Suka haska gidan baka jin motsin kowa, sai haushin karnuka can ba'a rasa ba.

   Garadan maza ne ke dirkowa ta saman fence na gidan, Dukkan su fuska rufe, Ogan su wanda matashin saurayi ne ta k'ofa ya shigo, wanda wani k'arfe yayi amfani dashi, Ya tsaga k'ofa, Ya shigo.

   D'aya daga cikin su ya buga k'ofar mai gadi sai da ta b'alle, A razane ya tashi da salati a baki, FETTA a tsorace ta tashi tana b'oyewa a bayan shi.

    "Muje kayi mana jagora zuwa wurin Alhaji" D'aya daga cikin su ya fad'a, K'in tashi yayi , "Zaka tashi ko sai na fasa kanka", Ya fad'a yana saita mishi bindiga, A cikin ranshi baya jin zai yarda a cuci Alhaji dashi, duk halaccin da ya mishi, " Taurin kai zaka mana", "Ba zan tab'a nuna muku wane sashe Alhaji yake ba", " Dama buzaye akwai ku taurin kai, yau zaka gane kuren ka"

   Ogan su ya mishi alama da hannu, Bindigar da ya saita a kanshi, ya harba, bullet ya shiga cikin kan shi, Ya fad'i a wurin matacce, K'ara FETTA ta saki a gigice, Ogan su yasa hannu ya toshe mata baki, Ya mata alama da bindiga, Ta sake ihu zai fasa kanta, Dole ta gimtse baki, Tana hawaye, Tare da jin tsananin tsanar wad'annan mutane.

   Cikin gidan suka shiga, Tana jin k'arar harbe-harbe, A gigice ta fito d'akin su, Ta fita a guje, ta tsorata kada itama su fito su kashe ta, Gudu take cikin dare ga duhu, bata san ina take jefa k'afar ta ba.

    *Ga dukkan mai son post na littafin nan yamun magana nayi adding d'inshi group dina, Zanyi left a groups*

*Follow*
*Vote*
*Like*

*TEAM FETTA*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now