*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*14*
UNEDITEDTa dad'e tana addu'o'in neman tsari da dukkan sharrin mai sharri, da neman kariyar ubangiji, har aka fara kiraye kirayen sallar asuba.
10:30am
Kiran family Dr d'in su ya tashe sa daga bacci, tunda ya dawo masallaci sallar asuba ya koma, Ya d'auka tare da kangawa a kunne, Suka gaisa yace yana bakin gate, Ya mik'e ya saka jallabiya ya fita.
Fetta bacci ta koma wuraren k'arfe bakwai, Suraj ya fara shigowa, yayi tapping d'inta a k'afa, Ta bud'e ido tana mitsitsika su, alamun baccin bai sake ta ba, "Za'a miki allura", Tayi nodding kai tare da cewa "Ina kwana?", "Lafiya lau, tashi kisa hijab", Hijab dake gefenta ta jawo ta saka.
Yayi ma Dr iso ya shigo, shi ya rik'e mata hannu aka mata allura, baya son hannun Dr na tab'a jikin ta, Dr mamakin kishi irin na Suraj yake, murmushi kawai yayi,
"Ina tunanin gobe ba sai an mata ba, jikinta yayi sauk'i sosai, ta dage da shan magani", Cewar Dr, Hakan ya mishi dad'i, sam baya son Dr na mata allura, dan ba yadda zai yi ne, Ya masa rakiya har motar sa, ya cika masa aljihu da chanji, Dr nata godiya, yana matuk'ar son aiki da Suraj, dan ba k'aramin alkhairi yake masa ba.
B'angaren sa ya koma, yau zai tafi lagos, jirginsa sha biyu na rana, yanzu pass 11, Da sauri yayi wanka ya shirya cikin suit da suka matuk'ar yi mishi kyau, briefcase d'in sa kad'ai ya d'auka,
A falo ya samu Hajiya tare da Fetta suna breakfast, ta tilasta mata zama suyi tare,
"Mama ina kwana", "Lafiya lau, tafiyar ta tashi", "Eh", " Toh Allah ya tsare, ya bada sa'a da nasara", "Amin, ina sauri 12 zamu tashi", Ta juya kan Fetta "Kije kuyi sallama", Wane sallama zasu yi, banda tana jin nauyin Hajiya bata ga abunda zai sa ta mik'e ba, D'akin ta taga ya nufa, tabi bayan sa,
Yana tsaye ya saka hannaye cikin aljihu, "Da Mama bata ce kizo ba, ba zaki zo muyi sallama ba kenan", Ta sunkuyar da kai k'asa, "Haka ake wa miji, sam baki san kula da miji ba", Maganganun sa mamaki suka bata, ta kasa furta komai, Ya d'age kafad'a yace "Anyway am travelling, if you need anything you call me", Ya ajiye mata bandir na 500, Ya juya zai fita, Murya a sanyaye tace "Allah ya tsare ya bada sa'a da nasara", Ya juyo ya kai dubansa gare ta, Ya amsa da "Amin, you take care", Ya fice.
Mimi ta fara kuka alamun tashi daga bacci, ta d'auketa tana jijjigawa, tare da tofa mata addu'o'i.
Tasleem ta tashi jikinta duk yayi tsami, wanka tayi ta zura doguwar riga, ta fito main falo na gidan, Alhaji Tambari ya fito da shirin sa na zuwa office, Lauratu ta rako sa a baya, "Daddy ina kwana?", "Lafiya lau, ya jikin naki?", "Da sauk'i", "Mummy ina kwana?", "Lafiya lau", "Daddy maganar mu ta jiya", Ya sauke ajiyar zuciya ya kamata hannun ta, ya zaunar da ita kan kujera, shima ya zauna,
"Ina so ki saurare ni kuma ki fahimce ni", Tayi nodding kai, "Suraj da kike gani ba k'aramin mutum bane, hukunta shi zai iya jawo ruining reputation d'ina, ni dan' siyasa bana son abunda zai tab'a political career d'ina, Am sorry my daughter, kiyi hak'uri", Ya fad'a yana murza hannun ta, K'ulloton bak'in ciki ya tsaya mata a mak'oshi da k'yar ta iya furta "Ok Daddy na fahimta", "Yawwa yar' albarka, idan na dawo i have something special for you", Ta d'aga kai, "Kiyi murmushi", Tayi faking smile, "Sai na dawo", Ya fad'a yana mik'ewa, nauyin dake k'irjinshi ya rage sosai, atleast yayi convincing d'in ta, duk da yana jin takaici na rashin hukunta Suraj.