*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*36*
UNEDITEDKusan minti talatin yana durk'ushe a wurin ya kasa aiwatar da komai, Hajiya tun shigarta bata sake bi ta kansa ba, a ranta ta k'uduri dole ta k'ara koya masa hankali, ya gane kuskuren sa, yasan kowane dan' adam nada daraja duk rashin sa.
Shigowar Samee ya fargar dashi, ya d'aga rinannun idon sa ya kalle ta, Cike da mamakin yanayin sa tace "Ya Suraj ina wuni?", Da kai ya amsa ta, Ta k'arasa k'ofar d'akin tana knocking, "Waye?" Cewar Hajiya daga ciki tana kyautata zaton Suraj ne, "Mama nice", "Samee kin dawo", "Eh", Ta taso ta bud'e mata k'ofar, Suraj yayi saurin rufa mata baya zuwa cikin d'akin, Ganin haka yasa Samee ficewa,
Gwiwoyinsa ya kai k'asa yana had'a hannayen sa guri d'aya yace "Dan girman Allah Mama ki taimake ni Fetta ta dawo gare ni, wallahi na tuba, bazan sake wulak'anta kowa a rayuwa ta ba, nayi alk'awari zan kula da ita, zan yi k'ok'arin wanke laifina na baya, bazan sake makamancin sa ba", Uwa da da' sai Allah, tausayin sa taji ya lullub'e ta, Tace "Tashi shikenan zamu je Agadez, na saka baki ta yafe maka, amma ka kiyaye gaba, ko da yake yanzu ai ta wuce sanin ka, tafi k'arfin ka", Tabbas Hajiya gaskiya ta fad'a yanzu Fetta ba ajin sa bace, tafi k'arfin sa, ya katse tunanin sa ta hanyar yi wa Hajiya godiya.
Su'ad da k'yar ta samu kud'in mota dubu biyu na zuwa Kano wurin wata mak'wabciyar ta a gidan da suka zauna farko, Gidansu ta nufa, tayi mamakin ganin babu security bakin gate, ta tura k'ofa da zumar shiga, Mai gadin da bata sani ba ya taso yace "Baiwar Allah wa kike nema?" Da kallon mamaki tabi sa tace "Amma kai bak'on zuwa ne koh?", Ya gyad'a mata kai yace "Eh amma babu kowa a gidan, mutanen ciki sun tashi", "Su Hajiya sun tashi ba sanarwa, ko da yake sai muyi sati bamu yi waya ba", Ta fad'a a ranta, ta juya gare sa tace "Ina suka koma?", "Rijiyar zaki", Ta jinjina kai ta masa sallama ta tafi.
Da tambaya ta kai gidan dasu Hajiya suka koma, cike da mamakin ganin gidan ta shiga, yayin da zuciyarta ke tabbatar ma ba nan suka dawo ba, Fitowar Samee ya gaskata mata nan d'in ne, "Ya Su'ad oyoyo" Ta fad'a tana rungume ta, "Nan kuka dawo Samee?", "Eh" Ta fad'a tana gyad'a mata kai, Suka shiga ciki, A falo suka tarar da Hajiya rik'e da charbi a hannu tana lazimi, Ta fad'a jikinta tare da fashewa da kuka,
"Lafiya daga shigowa sai kuka, ni dallah d'aga ni", Cewar Hajiya tana k'ok'arin ture ta daga jikin ta, wanda take kyautata zaton dan taga gidan da suka dawo ne take wannan kukan, Ta sake matse ta tana tsagaita kukan, "Kukan me kike?, ko kukan mun rasa komai", Mamaki k'arara kan fuskar Su'ad ta d'ago tana kallon Hajiya, sun rasa komai kamar ya, "Mama ban gane inda magangun ki suka dosa ba", Ba tare da wani tunani ba, ta zayyane mata komai, kukan ta ne ya tsananta, lallai ta yarda duniya ba a bakin komai take ba, kowa yayi d'amara domin ta ya kwance, Kud'i da dukiyar da suke tak'ama dashi ashe duk bata hanyar Allah aka tara ta ba, shiyasa kada ka tab'a son mutum dan dukiyar sa baka san taya ya same ta ba, ka godewa Allah da abunda ya baka,
Cikin shesshek'ar kuka tace "Hak'ik'a mun yi kuskure da muka d'auki duniya da zafi, muka d'auka kud'i sune komai, gashi Adnan ya yaudare ni ashe talaka ne bashi da komai, ya sakeni saki uku", "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Hajiya ta shiga jerawa, "Ina nadama sosai a rayuwata Mama, ina ma ana mayar da hannun agogo baya, na gyara rayuwata ta baya, da na sani Ya Bello na aura, mutum mai cikar kamala da kyawawar d'abi'a nak'i sa saboda abun duniya, Mama wallahi yanzu ko mai napep ne zan iya aura in dai zan samu kwanciyar hankali, kud'i basu ne zaman aure ba" Ta k'arasa tana sake zubewa jikin Hajiya tana kuka.
Feena fitowar ta daga kitchen kenan ta gama abincin rana, K'anwar Fahad ta shigo tana yatsina fuska tace "Mummy na kira", Ta amsa da "Toh", gabanta ya fad'i tasan kiran ta baya tab'a zama alkhairi, tsana k'arara take nuna mata, Mayafinta ta yafa ta nufi b'angaren Mummy, A falo ta tarar da ita zaune sauran yaranta mata uku suna zagaye da ita, suna hira,