52

3.9K 293 14
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*52*
*Unedited*

    *4:00pm*

Jirginsu yayi landing a airport na Madina, Fetta tayi nisa a bacci, Suraj ya kai duban sa gare ta, Yayi tapping d'inta da hannu, Ta bud'e ido ta zube su a kan shi tare da karanta addu'ar tashi daga bacci, Har ya mik'e tana zaune saboda jikinta da ya mata tsami,

    "Baki gaji da jirgin ba ne, naga ya miki dad'i hadda bacci", Shiru ta masa tamkar ba da ita yake ba, Ganin bata kula shi ba, Ya fice ya barta,

   Da k'yar ta mik'e tabi bayan sa, Taxi suka d'auka zuwa hotel, Had'add'en hotel suka nufa, Ya musu lodging d'aki, Fetta ba abunda take buk'ata kamar kwanciya, Suna shiga tabi lafiyar gado, Suraj toilet ya shiga yayi alwala, ya fara rama sallolin da ake bin sa, Itama mik'ewa tayi ta shiga toilet tayi alwala, Ta gabatar da salloli,

    Telephone na d'akin ya d'auka, Yayi dialing number kitchen, Yayi ordering  shinkafa da kaza, Cikin mintuna kad'an aka kawo, Daga bakin k'ofa ya karb'a, Fetta wacce bacci ya fara d'aukar ta akan sallaya, taji muryar sa " Tashi sarkin bacci",

    Mik'ewa tayi tana mamakin yaushe bacci ya d'auke ta, Da hannu ya mata alama tazo taci abinci, Kusa dashi ta matsa, Ta kai hannu zata d'auki spoon, ya rik'e hannun ya matsar dashi gefe, Ya d'auki spoon d'in ya d'ibi abinci ya kai bakinta, Ba tare da wani tunani ba, ta bud'e baki ya saka mata, tasan yana yi ne saboda babyn shi, A tare suka cinye abincin, Yana feeding d'inta, Ya saka tissue ya goge mata baki, ya goge nashi.

    Kayan sa ya shiga tub'ewa, Ya umarceta ta cire nata, Da kallo tabi sa, Ya d'aga mata gira alamar Ya dai, "Ka fara yin wankan", " A tare zamu yi", Zata sake magana, Ya saka hannu akan lips d'inta alamar tayi shiru, Zip na rigar ta ya zuge, tare da b'alle bra d'inta, Tayi saurin saka hannu tana kare gabanta, "Wane dare ne jemage bai gani ba", Ya fad'a yana kafe ta da ido,

Ta sunkuyar da kai cike da kunya, Hannun ta yaja zuwa toilet, Tabi sa tamkar rak'umi da akala, a tare suka yi wankan cike da kunyar sa.

  Ta riga shi fitowa, da sauri ta shafa mai, tana saka kayan bacci, ya fito, tayi saurin kawar da kanta gefe, sam bata so su had'a ido, A gaggauce ta saka kayan, tabi lafiyar gado tare da jan bargo ta rufa.

     Aunty Jummai ta dawo daga kasuwa rik'e da ledoji a hannu taci karo da Sahabi a zaure, " Sahabi" Ta kira sunan shi cike da mamaki da fargabar ganin sa, "Hajjaju", " Lafiya dai?", "Lafiya ce ta kawo haka", " Toh Madallah", Ta fad'a tare da sauke ajiyar zuciya, "Nazo ne kawai mu gaisa", " Ka kyauta kuwa", "Ni zan koma", Ya fad'a tare da saka hannu a aljihu ya zaro dubu biyar ya bata, Ta zaro ido tace " Sahabi ina ka samu kud'i?", Yayi guntun murmushi yace "Yanzu komai ya zauna, wani hamshak'in mai kud'i nake wa aiki, shirin aure ma nake, zan zo na d'auke ki muje kiga gidana", " Ahh abu yayi kyau, Allah ya sanya alkhairi", "Amin"

    Ta rako shi bakin k'ofa, Ya nufi dalleliyar mota ya shiga, Aunty Jummai tabi motar da kallo, ta tafi da imanin ta, "Lallai Sahabi yaja kaya, bari ya dawo na rok'e sa kud'i naja jari",

Ta koma cikin gida, a tsakar gida ta tarar da Balkisu, tana kwalliya, " Umma sannu da zuwa", "Yawwa sai ina?", " Wurin aiki", "Wai wannan aikin naku ba'a zuwa ne sai da kwalliya", " Umma ai gara ka k'ure a daka kar a raina ka", "Ke ko, da Allah yayi ki yar' masu kud'i da bansan ya zaki yi ba", " Kai Umma", "Ai gaskiya ne", Tayi dariya tana cigaba da kwalliyar ta, Aunty Jummai ta shige ciki.

      Washegari Suraj da Fetta sun zagaya garin Madina, ya kai ta wurare Fetta nata raba ido, garin ba k'aramin kyau ya mata ba, Sun ziyarci kabarin Manzo SAW, Sunje wani shopping mall, kayan babies da yawa ya siya, Itama yace ta zab'i abunda take so, Turare kad'ai ta d'auka, Ya harare ta yace " Kilibibi", Gefen dogayen riguna yaje ya zab'o mata guda biyar masu masifar kyau da tsada, Wurin biyan kud'i tayi mamakin jin tsadar su, Daga nan suka wuce wurin cin abinci, Yayi musu order dankali da kaza, Kad'an taci, Ta ture plate d'in gefe,

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now