*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*16*
UNEDITEDGanin tana neman fad'uwa Fetta tayi saurin rik'e ta, "Lafiya?, meke damun ki?", Tayi k'arfin halin cewa "Kaina ke ciwo", Tana dafe gefen kanta dake masifar sarawa tamkar ana buga mata guduma, Ta zaunar da ita kan kujera tana mata sannu, Suraj kallo d'aya ya mata bai sake duban ta ba, Yana faman jijjiga Mimi.
"Bari na tafi", Ta fad'a tana mik'ewa, "Zaki iya kai kan ki gida?", Fetta ta tambaya cike da damuwa, "Kar ki damu zan iya", "Allah ya k'ara sauk'i", Ta amsa da "Amin"
Bata san ina take jefa k'afarta har ta kawo bakin motar ta, ta bud'e ta shiga, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Take maimaitawa, Da k'yar ta tayar da motar ta nufi gida, cike da tsananin tashin hankali, bata bi ta kan mutanen dake falo ba, ta nufi d'akin ta, tasa key ta rufe, jakarta ta cillar da mukullin mota saman gado, ta hau zagaye d'akin,
"Tabbas shine, ko shakka babu shi ne, bazan tab'a manta tabon da ke hannun shi ba", Hawaye masu zafi suka zubo mata, "Taya zan fara sanar da Fetta waye Suraj?, taya zan sanar da ita ?", Ta fad'a cikin d'aga murya, ta fad'a kan gado tana fashewa da matsanancin kuka.
Fetta jikinta yayi sanyi da yanayin Yasmeen, tana kyautata zaton ba ciwon kai kad'ai ke damun ta ba, amma kuma ba a haka ta shigo ba, meya canza ta suddenly, Suraj ya katse mata tunani "Karb'e ta, zan fita", Tasa hannu ta karb'e ta, d'aki ya shiga, ya sake fesa turaruka ya fito, "Allah ya bada sa'a" Ta fad'a cikin sanyin murya, "Amin", Har ya kai k'ofa ya juyo yace "Ba zaki mun rakiya ba", Ba musu ta mik'e ta raka sa harabar gidan, Driver ya taso da sauri ya bud'e masa mota, Ta koma cikin gida, tana mamakin sabon salon da ya tsirfu dashi.
Wayarta ta jawo ta kira Yasmeen taji jikin ta, Yasmeen wacce fuskarta tayi jajir tsabar kuka jin k'arar wayarta, da k'yar ta iya d'ago kanta da ya mata nauyi, tayi receiving, "Hello Yasmeen ya kika je gida?, ya jikin ki?, "Da sauk'i Alhamdulillah", Ta fad'a murya a dashe, "Dan Allah ki fad'a mun meke damun ki, nasan ba ciwon kai kad'ai bane, kuma ciwon kai ba zai sa kiyi kuka har muryar ki ta dashe ba", Ba zata iya fad'a mata ba, ba zata zama silar rugujewar farin cikin ta ba, a yadda ta hango soyayyar Suraj a k'wayar idon ta, ba zata zama silar jefata a wani yanayi ba, Ta katse mata tunani "Kinyi shiru, ba zaki gaya mun ba ko, you can't share your problems with me, baki d'auke ni yar' uwar ki kamar yadda kike fad'a ba", "Tamkar jinina haka nake jin ki Fetta, ki yarda dani babu komai", Fetta ta kashe wayar cike da takaicin rashin sanar da ita.
Yasmeen tabi wayar da kallo, tana ji wasu hawaye na zubo mata, gara kiyi fushi dani Fetta akan na gan ki cikin damuwa da tashin hankali, i can't bear to see you in pain, rayuwar k'uncin da kika yi a baya ta isa, bana so ki sake wata.
Fetta ta kasa natsuwa, tana son tasan damuwar Yasmeen ko zata iya taimaka mata, haka take jin ta tamkar yar' uwarta ta jini, wunin ranar sukuku tayi shi,
Ana sallar isha'i Suraj ya dawo, ya tarar da ita tana sallah, Mimi na sashen Hajiya tunda yamma ta aiko aka karb'e ta, Shima alwala yayi ya gabatar da sallah, Ta idar tayi folding sallaya, Ta koma falo ta zauna, yana idarwa ya biyo ta falo, "Sannu da zuwa", "Yawwa" Ya amsa yana zama kujerar kusa da ita, Ledar da ya shigo da ita, ya bud'e shawarma ce, ya d'auki d'aya ya mik'a mata d'aya, Tace "Thanks", Duk da dad'in da tayi, rabi taci, ta ajiye saura, Suraj ya lura da sanyin da tayi, bai tambayeta dalili ba.
Daren ranar ma sai da suka raya shi, idan yana tare da ita sam baya iya controlling kansa, Fetta bata hana sa.
3:00 na dare