25

4K 308 24
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*25*

    _Masoyan FETTA tana godiya😂_

    Zaune take a falo, bayan wasu mintuna tana duba agogo, Ana sallar isha'i ya fita, gashi sha d'aya da rabi bai dawo ba, ba rashin dawowar sa ya dame ta ba, baccin da ya dami idon ta,  kar ya dawo yana knocking tayi bacci.

    Duk k'ok'arin ta kar tayi bacci sai da yaci k'arfin ta.

        12:15am na dare

Ya shigo gida, ransa a matuk'ar b'ace, kallo d'aya zaka masa kasan a gajiye yake, Masu gadi ma sai da ya balbale su basu bud'e gate da wuri ba, Hak'uri suka shiga bashi,

      Knocking k'ofar yake, Fetta sam bata ji ba, tayi nisa a duniyar bacci, Wani duka ya kaiwa k'ofar kamar zata b'alle da ta katako ce ba abunda zai hana ta b'allewa, A firgice ta mik'e,  lek'awa tayi ta jikin k'ofa, Shi ta hango ya had'e rai kamar hadarin gabas,

     Ta bud'e, Tamkar zai bi ta kanta ya shigo falon, Kallo d'aya ya mata, yaga alamar daga bacci ta tashi, "Kasa", Ya fad'a yana jan tsaki, " Bacci ma lafiya ne", Har ya wuce, Ya dawo,

    Gab da ita ya tsaya k'irjinta ya shiga bugawa bata d'auka yaji ba, Kanshi ya had'a da nata ya gwara da k'arfi, Tayi baya ta fad'a kan kujera cike da azaba, komai na falon double take ganin sa, "Suraj ba sa'an wasan yarinya ba ne, wallahi kika k'ara mun rashin kunya sai na bambamce miki tsakuwa da aya", Ya wuce ciki yana huci.

    Hannu tasa ta dafe goshinta dake  zugin azaba " Allah ya isa na mugu", Ta fad'a tana hawaye,

    "Tukur you must pay for this, Wallahi bashi ka d'auka, babu wanda ya isa ya shiga trap d'in SURAJ SA'ID ya kwana lafiya", Ya fad'a yana cukwikwiya rigar da ya cire, ya jefar da ita cikin basket, tare da fusgar da iska.

    Toilet ya shiga, ya watsa ruwa, Cikin minti 5 ya shirya, Singlet da boxer ne a jikin shi, Ya fito hankali kwance, Ganin sa tayi saurin sunkuyar da kai, " Mara kunya", Ta fad'a a ranta,

    " Taso kiyi aikin ki", Ya fad'a da umarni, Ita sam ta manta da zancen wani tausa, Kamar ta fasa ihu ta mik'e tabi bayan sa, goshin still yana azaba.

     Kan gado ya kwanta ya mik'e k'afa, Yasa hannu ya tallabo kansa saman pillow, Fetta tunanin yadda zata d'aura hannun ta kan jikin sa take,  k'ato a gabanta sanye da boxer da singlet, taga tausa ana yi ko sanye da kaya, jikinta bai tab'a had'uwa da na da' namiji ba,

     "Oya start", Ya daka mata tsawa, A hankali ta d'aura hannun ta kan k'afar sa tana runtse ido, Laushi da taushi da yaji ya saka shi jin zirr, bai tab'a tunanin zai ji hannunta haka ba, yasan masu aikin wahala hannun su tauri yake, Bata fara ba, kuma bata d'auke hannunta ba, A tsawace yace  " Zaki fara ko sai nayi ball dake",

    A hankali ta fara masa tausa, Cinyar sa ya nuna mata alamun har nan zata yi, Ta runtse ido tana cije baki, ta shiga yi,

   Lumshe ido yayi sakamakon sak'on da tausar ke aikawa gangar jikin sa, Ba zai iya misalta yanayin da yake jin sa ba, Gajiyar da ya tattaro a hankali take barin jikin sa,  wani k'arfi na sauko masa.

    Fetta har ta fara gajiya bai ce ta daina ba, sai ma k'ara lumshe ido da yake, Tsayawa tayi ta huta, Ya bud'e idon sa ya zube kanta, Sai da ta tsargu da irin kallon da yake mata, ba shiri ta cigaba, Da hannu ya mata alama, ta daina taje ta kwanta,

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now