*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*03*
*UNEDITED*Fetta na d'aki kwance tana sauraren wa'azin Malama Khadija a wayarta, Suraj ya shigo "Ki tashi zamu fita", Ta amsa da "Toh" tana mik'ewa, ta kashe wa'azin, K'aton mayafi ta d'auka ta yafa, Suraj tuni ya fice daga d'akin da baby a hannun sa, Fetta ko da ta fito har ya kai mota, Ta bud'e gaba ta shiga ba tare da tace mishi komai ba,
Bakin wani had'add'en mall taga yayi parking, Ya mata umarceta ta fito, Ciki suka shiga, yaja basket guda biyu, Ya mik'a mata d'aya, Wurin kayan babies ya nufa, Tabi shi a baya, Kaya ya shiga jida hadda na wasan yara, Mamaki ya cika ta ganin uban kayan da yake kwasa, bayan akwai wasu da yawa gida, "Uhmm nace ba kamar kayan nan sunyi yawa", Harara ya watsa mata yace "Ina ruwan ki, abeg je ki zab'ar wa su Hajiya da Umman ki tsaraba", Ba tare da tace komai ba, Ta nufi wurin dogayen riguna,
Kowa sai da ta d'aukarwa tsaraba hadda su Su'ad, Hajar da Ali ma bata manta dasu ba, Ganin bata d'aukar wa kanta komai ba, Yace "Don't you need anything", Ta mishi nodding kai, Wurin dogayen riguna ya nufa ya zab'o mata masu azabar kyau, yana so yaga tasa abaya ba k'aramin kyau yake mata ba, Ita mamaki ya bata ganin yadda bai damu da kashe kud'i ba, tamkar wanda bai san zafin su ba, abaya har sun soma mata yawa, ko a saudia ya siyan mata wasu, gudun kar tayi laifi yasa tayi shiru,
Kud'i masu yawa taji an ambata duk da ba wani gane kud'in america take ba, tasan kud'i ne masu yawa, Ya mik'a ATM d'in sa suka zara, Ma'aikatan suka biyo su da kayan har mota.
Gida suka koma, A falo su Jane suka baje kayan da suka shigo dasu,
"Ki shigar dasu d'aki, ki shirya gobe zamu koma 9ja, flight d'in mu 6:30am", Bata san lokacin da ta saki wani murmushi ba, Farin ciki ya lullub'eta tayi missing Umman ta dasu Yasmeen, D'aki ta shiga ta hau had'a kaya, bayan ta shirya komai ta jawo wayarta tayi dialing number Aliya, bugu d'aya ta d'auka, "Mutanen landan", "Umma ina wuni?", "Lafiya lau, ina kishiyata?", "Gobe dai zaki ganta", "Kaii amma naji dad'i, me kike so a dafa miki? duk da nasan Hajiya zata had'a muku algwagwajiya", "Dan' wake", "Dan' wake Fetta ki rasa abunda zaki ce sai shi", "Eh Umma tunda nazo nan garin nan ban ci ba", "Toh shikenan, ki gaida Mai gidan, naji Mallam na kirana", "Sai anjima ki gaishe shi", "Zai ji"
Fetta ji take kamar ta jawo gobe, ta ganta a 9ja, bacci ma rabi da rabi tayi, Suraj ya lura da d'okin da take, bai ce mata komai ba.
Kiran assalatu a kunne ta, ta tashi ta shiga kitchen ta had'a musu breakfast, kasancewar bata sallah, Ko da ta dawo d'akin Suraj na sallah, Toilet ta shiga ta had'a ruwan wankan baby, Ta kira Jane ta kama mata, Tayi mata ta shirya ta, itama tayi ta shirya cikin abaya ta matuk'ar yi mata kyau, Suraj sai satar kallon ta yake yana jin tamkar ya rungumeta,
6:00am daidai suka gama duka shiri, Jane suka shigar musu da kaya mota, Suraj ya musu alheri mai yawa, Suka shiga mota suna waving juna, Driver yaja zuwa airport.
Su'ad na gaban dressing mirror tana kwalliya, Tace "Sis ashe baroroji ta haihu", "Haba dai?" , "Wallahi", "Yaushe? Me ta haifa?", "Wai yau 3days, Baby girl, nima d'azu Mama ke tambayata wai mun kira mun mata barka", "Nace ai ban ma san ta haihu ba, ta hau ni da fad'a wai bama kira mu gaishe ta kiji fah", Feena tace "Tabb wannan banzar zamu kira mu gaisar, ta tsinana mana me", "Ai shine, ni wallahi ko dawowa sukayi kallo basu isheni ba", "Sune zasu dawo yau kenan, shine Mama ke ta faman hidima, tasa masu aiki suyi girki ya kai kalar biyar bayan snacks da drinks, ana ta fama gyaran gida", Su'ad taja tsaki tace "Kai kace yar governor za'a tarba, ba yar mai gadi ba", "Bari ke dai, ni ko babyn bana son gani", "Nima wallahi"
Wayar Su'ad da tayi k'ara ta katse musu hirar, "Am sorry darling, gani nan fitowa", Ta d'auki turare ta bad'e jikinta dashi, Feena ta kalle ta tace "Mu dai Allah ya nuna mana ranar biki mu chashe", "Kar ki damu Sis very soon", Ta fice.
Yana jin shigowarta motar, Ya d'auke kai ya b'ata rai, Kwantawa tayi jikin shi tace "Haba habibina Am sorry" Ta sumbaci lips d'in shi, "Bazan hak'ura ba" Ya fad'a yana sake d'aure fuska, "Babyna please me kake so na maka ka hak'ura", A kunne ya rad'a mata "Muje hotel", Ba tare da wani ja ba tace "Muje", Su'ad tayi nisa a soyayyar Adnan, ko kad'an bata son b'acin ran sa.
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT*
Jirginsu Suraj yayi landing safely, Ya kalli Baby dake hannun sa yace "My little angel kin dawo origin d'in ki", Fetta ta kalleshi tayi murmushi, "Yana magana tamkar tana jin sa", A zaton ta a zuci tayi maganar sai ji tayi yace "Is she deaf da bara taji ni ba", Fetta ta tab'e baki ta mik'e tayi hanyar fita jirgin,
Drivers d'in shi already suna airport suna jira, ba b'ata lokaci suka shiga, Suka ja zuwa gida.
Yasmeen tuni tana gidan ita da Aliya dasu Hajar suna jiran isowar su, Ana yin horn Yasmeen tace "My baby is here", Banda tana shakkar Suraj, waje zata fita ta tarbe su.
Tun daga bak'in k'ofa ta buga tsalle ta rungume Fetta, "Oyoyo Maman Baby", Hajiya tuni ta karbi babyn hannun shi, Ta shiga juyata tana fad'in jikalle oyoyo, Aliya kuwa sai washe baki take, Hajar da Ali suka mak'ale Fetta, Bayan gaishe gaishe, aka dabaibaiye su da abinci kala kala, Fetta kad'an taci shima dan kar Hajiya taji ba dad'i, Ta jawo cooler dan' waken da Aliya ta mata, Ta fara ci, sosai taji dad'in shi.
Feena na d'aki na jiyo su, tayi tsaki, taja bargo ta lullub'e tamkar mai bacci,
"Ina su Su'ad ne?", Suraj ya tambaya, "Su'ad sun fita tare da Adnan, Feena kuma na d'aki ina ga bacci take", "Mum bai kamata ana barin ta suna fita tare ba, tunda ba auren ta yayi ba", "Hakane kuma In shaa Allah daga yau bazan k'ara bari ba", "Zanje na watsa ruwa na huta", "Toh Allah ya hutar da gajiya", Ya amsa da "Amin", Ya mik'e, a zaton sa Fetta zata biyo sa, sai ma k'ara gyara zama da tayi.
"Fetta ga d'aki can nasa an gyara miki, idan kika buk'atar wanka ki huta, anan zaki zauna har sai kinyi arba'in", Fetta murmushin k'arfin hali tayi tace "Nagode Hajiya", "Meye na godiya, kefah ya'ta ce", Har cikin ranta bata jin dad'in haka ba, taso ta koma ta zauna da Umman ta, tayi kewar zama dasu shine babban dalilin da yasa take zumud'in dawowa, Aliya ma sam bata ji dad'i ba, taso Fetta ta zauna dasu, har d'akin Fetta ta gyare tass tayi sabon fentin, yanzu ba laifi tana samun kud'i.
Fetta ta mik'e jiki a sanyaye ta shiga d'akin, ba k'aramin gyara Hajiya tasa aka mishi ba, Komai na buk'ata akwai, Aliya ta biyo bayanta, Bakin gado ta zauna kusa da ita, tare da kamo hannun ta, Tace "Kar ki sa damuwa a ranki kinji Fetta, k'aunar da Hajiya kema tasa haka, nima na so ki zauna a wurin mu, Amma In Shaa Allah kullum zan rik'a zuwa ina wuni anan, ni zan rik'a ma baby wanka", Taji dad'in jin haka kullum zata rik'a ganin Umma dasu Ali, Yasmeen ta shigo rik'e da baby tana kuka, "Gata ki bata", Ta karb'eta tana jijjigawa, Kunyar Aliya take ji, ba zata iya breastfeeding a
gabanta ba, Aliya ta fuskanta tace "Bansan sai yaushe zaki daina kunyar nan ba, yarinya kamar fulani", "Wai kunyar ki take ji", Yasmeen ta fad'a tana dariya, "Eh wai, ai bari na tashi na bata wuri", Fetta ba tace komai ba, sai faman jijjiga baby take,Aliya ta fita, sannan tayi breastfeeding d'in ta, "Baki ji kunyar d'aukar cikin aka ganki dashi ba, sai shayarwa", Harara ta wulla mata tace "Ki fita a idona Yasmeen", Ta cigaba da dariya, Sai da tayi bacci ta shinfid'e, Tace "Dan Allah kama mun na fitar da tsaraba", "Ba zaki bari ki huta ba", "A'ah gara nayi gaba d'aya na huta"
Ta fitar ma kowa da tsarabar shi, har yasmeen kowa yayi farin ciki, sab'anin su Su'ad da ko d'aki basu fito ba, tana dawowa ta shige abun ta.
Aunty yelwa ta rafsa tagumi, rashin sanin halin da yar'ta ke ciki ba k'aramin damun ta yake ba, Binta tazo ta janye mata hannu tace "Ba kyau tagumi Mama", "Dole nayi tagumi, rashin sanin wane hali yar'uwar ki take ciki ba k'aramin damuna yake ba", "Addu'a zaki rik'a mata Allah ya kareta a dukkan inda take", "Ina yi Binta", Ta fad'a tana matsar k'walla.
Kiran sallar magrib ya tashi Suraj daga bacci bai ga alamun Fetta tazo part d'in ba, "Me take nufi? Meya hana mata zuwa?",
Alwala yayi, ya gabatar da sallar magrib, Ya nufi sashen Hajiya dan jin dalilin Fetta na rashin zuwa part d'in ta har ana magrib bata zo ba.
*FOLLOW*
*VOTE*
*COMMENT**ZEELISH*💕