*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*30*
UNEDITEDYasmeen da kallo tabi sa, yayin da zuciyarta ta raunana, Jin tayi shiru ya d'ago idonsa da suka soma ja yace "A shirye nake na karb'i duk wani hukunci da zata yanke a kaina, but bazan iya jure rashin ta ba", Tausayin sa taji ya kamata, wani b'angare na zuciyarta na sanar da ita watak'ila had'uwarsa da Fetta ya zama silar shiryuwar sa ko da ace ba zata koma gare sa ba, a yadda taga soyayyar Fetta ta kamasa ko shakka babu komai zai iya dan ganin ta dawo gare sa, Tsintar kanta tayi da furta "Masarautar Agadez", A razane yace "Kina nufin Fetta na masarautar Agadez", Kai ta gyad'a masa, "Meye had'in ta can?", "Shine kad'ai abunda zan iya sanar da kai", Godiya ya shiga yi mata tamkar ba Suraj mai ji da kai, da isa, Murmushi tayi ta mik'e ta shige cikin gida.
Wayarsa ya fiddo a aljihu, ya shiga kiran Rabi'u, bugu biyu ya d'auka, "Ranka ya dad'e ina kwana?", Bai amsa gaisuwar ba yace "Ina so kamun booking flight na Agadez, if possible jirgin yau nake so", "Ok Sir", Ya kashe wayar, Rabi'u murna yake ogan nasa ya kira sa, ya jima bai ga kiran sa ba, ko ya kira ma baya d'auka, har ya soma zargin ko wani laifin suka masa duba da yadda ya canza musu gaba d'aya.
Cike da tunanin meye had'in ta da Masarautar Agadez ya dawo gida, k'aramar jaka ya d'auka ya saka kayansa kala biyu da abubuwan da yake tunanin zai buk'ata, Hotan ta da ya mayar d'akin, ya masa ma'ajiya gefen gado, Ya d'auka ya kalla yace "Am coming to you and My little angel", Ya sumbaci hoton yana jin sanyi a ransa, da jin tamkar ya bud'e idon sa ya gansa a gaban su, Kiran Rabi'u ya katse masa tunani, Yayi receiving yana fatan an samu, "Ranka ya dad'e an samu gobe da safe k'arfe bakwai", Ya kashe wayar cike da haushin rashin samu yau, yayin da wani b'angare na zuciyar sa ke nuna masa farin ciki ya dace yayi, Ya sauke ajiyar zuciya, ya kwanta kan gado tare da saka wayoyin sa flight mode, baya son damuwa.
"Am sorry Fetta na karya alk'awarin da na d'aukar miki, ina ganin sanar dashi shine alkhairi" cewar Yasmeen dake zaune a d'aki, hankalin ta ya kasa kwanciya tunda ta sanar dashi, She is feeling guilty.
Bilkisu shiri sosai take na zuwan Suraj, gidan ta gyara tsaf, tayi cefane wanda bata tab'a yi ba, ko taba Aunty Jummai ayi, Kaji biyu ta siyo tayi pepper chicken, tayi fried rice da coleslaw, ta had'a ginger drink wanda tayi barbad'en magani a ciki, Bayan sallar la'asar tayi wanka ta chab'a ado cikin fitted gown na atamfa, tabi jikinta da turaruka ta feshe,"Yau dole Suraj ya bada kai bori ya hau, wannan kyau haka tamkar lu'u-lu'u" Cewar Aunty Jummai, Bilkisu tayi fari ido tana jin tamkar tafi kowa a yau, Tana karairaya ta nufi d'akin ta, ta d'auki waya ta danna kiran Suraj, jin ta a kashe, zuciyarta ta buga, ta sake kira, kusan sau biyar tana kira amsar d'aya ce a kashe, zama tayi gefen gado, ta rafsa tagumi tana addu'ar Allah yasa ba ruining ranar ta zai yi ba.
Suraj sam ya manta da zancen had'uwar sa da Bilkisu, zumud'in zuwa yaga Fetta yasa ya manta duka schedules d'in sa na ranar, Bayan ya idar da sallar la'asar a masallacin dake had'e da gidan, Ya nufi b'angaren Hajiya, bai sameta a falo ba, ya shiga cikin d'aki, Kwance take da charbi a hannu tana lazimi, ya kalleta yana jinjina k'ok'arin mahaifiyar tasa wurin ibada, shi kam bazai iya tuna when last ya d'auki charbi yayi lazimi ba, ko karatun Qur'ani baya samun lokaci ya zauna yayi, a ko da yaushe busy yake kan neman duniya da burin tara arzik'i mai yawa, Tunanin sa ya katse yace "Mama ina wuni?", "Lafiya lau", ta fad'a tana tashi zaune, "Uhmm dama nace zanyi tafiya gobe", "Toh Allah ya kai ka lafiya ya bada sa'a", Ya amsa da "Amin", "Ga abinci can kan dining ka d'auka kaci, naga ko an kai b'angaren ka haka ake dawowa dashi", Ya d'an sosa k'eya yace "Mura ce ke damuna, so nayi losing appetite", "Allah ya sawwak'e" Ta fad'a ba dan ta yarda ba, tasan sarai rashin Fetta ke damun sa, Ya amsa da "Amin" Yana mik'ewa ya fita, tabi bayansa da kallo, ta girgiza kai ta sake kwanciya tana cigaba da lazimi.
Su'ad na kitchen na k'ok'arin dafa indomie ta saka ma cikin ta, yunwa sosai take ji, Taji k'arar wayarta, ta fito da sauri zuwa falo ta d'auka, Ganin Adnan ne mai kiran tayi mamaki, sanin baya kiranta idan ya fita tun safe sai dare yake dawowa ko abincin ta baya ci, tana gab da tsinkewa ta danna receive,
"Wane irin iskanci ne ina kira sai ta kusa tsinkewa zaki d'auka", Shiru tayi tana tuna kafin auren su ko sau goma zai kira bata d'auka ba, baya tab'a nuna fushin sa, sai ma fatan ba laifi yayi mata ba, lallai maza basu da tabbas, "Ko baki ji bane" Ya fad'a cikin tsawa, "Uhmm ina kitchen ne wayar na falo", Yaja tsaki yace "Ki had'a kayan ki, zan turo mota yanzu za'a kwashe hadda gadaje", Ya kashe ba tare da ya jira cewar ta ba, wayar tabi da kallo tana jin tsananin tashin hankali, ba dai sakinta zai yi ba, watanni kad'an da auren ta ace ya mutu, ba k'aramin kunya da abun fad'a zata sha ba, zama tayi ta kasa wani motsi balle tayi yunk'urin had'a kayanta,
Kusan minti ashirin tana haka, jin k'auri a kitchen tayi saurin mik'ewa, sam ta manta da indomie da ta d'aura, ta k'one k'urmus,
Fitowar ta kitchen yayi daidai da sallamar mai gadin ta, yake sanar da ita masu kwasar kaya ne, jiki a sanyaye ta had'a kayan sawar ta, a akwatun nan lefe, ta had'a nasa, Masu kwasar kaya suka shigo suna kwashewa.
Bilkisu ganin har bayan isha'i babu Suraj ba alamar sa, wayoyin sa har lokacin a kashe, Hankalinta ya soma tashi, kar dai watsa mata k'asa zai yi a ido, duk shirinta ya zama na banza, Aunty Jummai ta sama a falo tace "Umma kinji sa shiru, wayoyin sa a kashe", Ta k'arasa hawaye na wanke fuskar ta, "Bashi nan zuwa anjima mu gani, ina tunanin wani uzurin ya rik'e sa", "Allah yasa" Ta fad'a tana share hawayen ta.Adnan sai kusan sha d'aya ya shigo gidan, ya dawo da wuri kenan, Su'ad dake zaune tsakar gida kan kujerar roba, ta kalle sa tace "Sannu da Zuwa", "Tashi mu tafi, ina fatan ba komai naki a cikin gida", Kai ta girgiza masa, mayafi ne sanye a jikinta sai wayar dake hannun ta, Motar data gani bakin gate ta bata mamaki, Civic ce one door(Mai k'ofa d'aya), "Dama Adnan na hawa irin motar nan?", Ta tambayi kanta, "Zaki wuce mu tafi ko kuwa", Ya fad'a cikin d'aga murya, ta bud'e murfin motar ta shiga,
Ghetto area taga sun nufa, irin unguwar yan k'auye, cab'ali da kwata k'oina, ga yara na yawo ba kaya, awakai da raguna had'i da kaji nata yawo, Gidajen masu tsarin ginin da ne kewaye da unguwar, babu ginin zamani ko d'aya, Unguwa ce ta talakawa, Mamaki fal ranta bata da damar tambaya, mamakin ta bai k'aru ba, sai da taga sunyi parking bakin wani k'aramin gida, mai k'ofa babu gate, Yace ta fito, babu musu tabi bayan sa har cikin gida,
Gida ne k'arami mai d'akuna biyu a jere, d'aya ciki da falo, d'ayan kuma falle d'aya, kitchen da band'aki, sai tsakar gida, "Anan zamu cigaba da zama", Ya fad'a hankali kwance, A razane ta kalle sa tace "Me kake fad'a Adnan", "Abunda kunnen ki suka jiye miki", Ya juya ya fice abun sa, Zama tayi dirshan kn sementin dake shimfid'e tsakar gida, ta d'aura hannu ta fashe da kuka.
Bilkisu ranta ya kai k'ololuwa wurin b'aci da rashin zuwan Suraj, taci kuka ba kad'an ba, Aunty Jummai ta dinga lallashin ta, itama ranta ya b'aci sosai, ta d'auki alwashin ko zatayi yawo tsirara sai Bilkisu ta koma gidan Suraj, asiri ko wane iri duk tsaurin sa ta d'auki alwashin aiwatar dashi, Ta gaji da jiran tsammani, abu yak'i ci yak'i cinyewa.
Suraj daren yau gani yake tamkar an k'ara masa tsawo yadda ya k'osa gari ya waye, yayi tozali da muradin ran sa, sai faman juyi yake kan gado, yana duba agogo akai akai.
Kiran sallar farko a kunnen sa, yayi wanka had'i da brush, ya d'auro alwala yana jiran a tada ik'ama.
Fetta tunda ta tashi sallar asuba bata koma ba, kayanta take had'awa, jirgin safe zasu bi zuwa Niamey, waccan karan ma ita ta buk'aci tafiya a mota dan taga k'asar Nijar, Bikin yar' k'anwar Mummy ake, sati d'aya zata yi a can, Sanah taso bin su but suna zuwa makaranta,
*7:30am*
Jirginsu Suraj ya lola dasu sama zuwa k'asar Nijar, zaune yake ya lumshe ido, yana tunanin Fetta, da farin cikin cikin awanni kad'ai zai yo tozali da ita, yaga little angel d'in sa yana tsananin k'aunar gudan jinin tasa."Ba zaki tsaya kici abinci ba", Cewar Azagas, Fetta tace "A'ah Tanti, idan na tsaya zamu iya rasa jirgin mu", "Toh Shikenan Allah ya tsare ya kai ku lafiya, a gaishe da mutanen can", "Zasu ji", Ta fito harabar masarautar rungume da Mimi, da sauri dogari ya taso ya bud'e mata k'ofa, ta shiga suka nufi airport, suna zuwa ba b'ata lokaci jirginsu ya d'aga zuwa garin Niamey.
_Ku k'ara yawan votes da comments na k'ara yawan typing😎 duk da nasan kuna yi daidai gwargwado amma ina so yafi haka😀_
FOLLOW
VOTE
COMMENTZEELISH💕