*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
_Da sunan Allah mai rahma mai jin kai_
*The long awaited day has come kamar yadda na muku alkawari zan cigaba da typing Fetta wanda zai zo a matsayin kashi na biyu, hope you will continue to enjoy every part of the story, wanda suka fara manta yadda labarin yake sai suyi going through part one*
*01*
UNEDITEDTasleem a hargitse ta iso asibitin, kallo d'aya zaka mata kasan bata cikin natsuwar ta, Gaf da shiga ward na masu haihuwa tayi kokarin tattaro natsuwa tare da b'oye damuwar ta, Wata Nurse taci karo da ita, "Excuse me Madam" Ta fad'a tana shan gabanta, "Yes can i help you?" , "Ina tambayar Matar Suraj da ta haihu yau?" "ohh wata nigerian?", "Yes" Ta fad'a tana nodding kai, "Ni na karb'i haihuwar" , "Ohh wow", Hannun ta taja gefen can lungun da ba kowa, Tace "wani taimako zaki mun", Ta zaro dollars cikin jaka wanda zasu kai kimanin dubu d'ari biyar, "Idan kika mun aikin da zan saki sa zan baki su"
Nurse ta zaro ido tace "Wane aiki?", "Ki sato mun babyn", Cike da tsoro tace "Am scared Madam idan aka kamani kashe ni za'a yi", " Ba za'a kama ki ba, da daddare zan zo na karb'i babyn" Tayi k'asa da murya tana rad'a mata yadda zasu yi, Cike da gamsuwa Nurse tayi nodding kanta.
Suraj throughout asibitin ya wuni, duk abunda ake buk'ata sai dai ya kira a kawo, Yaso a sallame su a ranar, Dr yace za'a k'ara duba lafiyar babyn.
12 na dare ya bar asibitin zuwa gida, basa bari a kwana, Ya tafi cike da kewar babyn sa, Allah ya dasa mishi wata zazzafar k'auna ta babyn.
Fetta na rungume da babyn ta tana bata nono, zuciyarta cunkushe da tsananin k'aunar ta, tare da tsantsar farin cikin da Allah ya sauke ta lafiya, wani b'angare na zuciyarta na fargabar wulak'ancin Suraj tasan yana d'aga mata k'afa ne saboda babyn sa da take d'auke dashi, babbar fargabar ta shine ya raba ta da gudan jinin ta, Bata so yar'ta tayi rayuwar maraici kamar yadda tayi.
Nurse ta turo k'ofa ta shigo, Fetta ta d'aga kai ta kalle ta, tayi murmushi, "Zamu maida baby ward na jarirai", Ta mik'a mata ita tana jin kamar a barta ta kwana wurin ta, ta karb'i jaririyar ta nufi d'akin jarirai da ita, A can Dr zai duba ta tare da sauran babies da aka haifa yau.
*2:00am* na dare
Tasleem ce sanye da kayan nurses, ta saka facemask, zaka rantse tana d'aya daga cikin ma'aikatan asibitin, Ward na jarirai ta shiga, Mai kula dasu ta b'ingire a kujera tana bacci, wanda da had'in bakin ta, taba Nurse Charlie lemo mai d'auke da maganin bacci, ta bata tana sha ba'a yi minti biyu ba, bacci ya d'auke ta.
Nurse Charlie ta d'auko babyn ta mik'awa Tasleem, Tayi saurin ficewa daga ward d'in tana sauri sauri, gudu gudu, Fatan ta ta fice daga asibitin ba tare da kowa ya ganta ba.
K'arar wayarta ya tashe ta daga nauyayyen baccin da take, Kamar ba zata d'auka ba, Ta jawo ta kanga a kunne ba tare da ta duba mai kiran ba, "Me kuke needing?" Taji muryar Suraj, "Nothing" Ta bashi amsa tana mamakin kiran sa cikin dare.
Ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba, Ta ajiye wayar, ta koma baccin ta.
Suraj hankalin sa yaji ya kasa kwanciya, yana son dawowa asibitin, Ya mik'e ya d'auki mukullun mota ya nufo asibitin.
Da dai k'ofar shiga yaci karo da Tasleem zata fito tana sauri bata kallon gabanta, Kaurar sa tayi dashi, yasa tayi saurin ja da baya, idonta cikin nasa, Gabanta yayi mummunan, tashin hankali ya bayyana kan fuskar ta, Sam bai ganeta ba, Ta manta akwai face mask a fuskar ta, tuni ta sadak'ar ya gama gane ta,
Idon sa ya kai kan babyn dake hannun ta, "My little angel" Ya furta da k'arfi, Tuni ta saki guntun fitsari tsabar tsoro,
"Ina zaki kai mun babyna?" Tayi shiru ta kasa bashi amsa, zuciyarta na dukan uku uku, tamkar zara fasa k'irjin ta ta fito, "Nurse" Ya fad'a a d'an tsawace, Jin bai ganeta ba, Tayi k'ok'arin tattaro natsuwa tace "Zan kai babyn wurin mum d'inta ne she have been crying", "I guess nan hanyar fita ce kuma banjin babyn na kuka ba" Ya fad'a yana bin ta da kallon tuhuma, Tayi k'arfin hali cewa "I was carried away, yanzu tayi shiru", Hannu yasa ya karb'i babyn ya wuce ba tare da ya sake ce bata komai ba, A zuciyar sa bai yarda da ita ba.
Tasleem a guje ta fice asibitin ta shiga motar ta, taja a 360 bata dawo natsuwar ta ba sai da taga tayi nisa da asibitin.
Ajiyar zuciya ta sauke da hamdala bai ganeta ba, Wani k'ullotin bak'in ciki taji ya tsaya mata na rashin cikar burin ta, "Ba zan tab'a hak'ura da kai ba Suraj, sai na raba ka da shegiyar baroroji da yar'ta" Tayi assuring kanta ta buga sintiyarin mota.
Direct office na Dr ya nufa, ba b'ata lokaci ya samu ganin sa, Bayan sun gaisa, ya buk'aci sallama, Dr yace sai gobe, Suraj ya mishi narrating abunda ya faru, Ya k'ara da cewa ba zai bar family shi su kwana ba, Dr yayi mamakin jin lamarin yace zasu yi bincike, Ya rubuta musu takardar sallama.
Fetta bacci take hankali kwance, Suraj ya turo k'ofar d'akin ya shigo, Haushin ta ya kamashi ganin tana bacci a natse, Yana k'ok'arin rasa babyn sa.
Bottle na ruwa dake gefen gado ya d'auka, ya zuba a baki, ya watsa mata a fuska, Firgigir ta mik'e, ranta ya matuk'ar b'aci, "Salon wulak'ancin da ya fara dashi kenan, idan da ta d'auka yanzu bara ta d'auka ba"
Wani kallo ta jefa masa mai cike da takaici, "Wacce irin uwa ce ke da bata damu da yar'ta ba" , Mamaki ne ya cika ta gani yazo da sabon rainin hankali, ta raini ya' wata tara cikin cikinta, ta haife ta bayan azabar da tasha sannan yace bata damu da ita ba, idan ma yazo da salon raba su toh wallahi bai isa ba,
"Duk duniya babu wanda ya kaini so, k'auna da damuwa da ya'ta idan ma wani shiri kake ka gaggauta warware shi", Da kallon mamaki yabi ta, ya kasa furta komai, Ya fice daga d'akin da babyn a hannun, Ganin haka ta mik'e tabi bayan sa, Tayi saurin shan gabansa, "Ina zaka je mun da ya'?", Ganin idan ya biye ta zasu yi creating scene, Yace "Je ki kwaso kayan ki zamu koma gida"
Ta sauke ajiyar zuciya, ta koma da sauri ta tattaro kayanta, ta nufi motar, ganin take tamkar zai rabata da yar' ta.
A motar ba mai cewa kowa komai har suka kawo gida.
*FOLLOW*
*VOTE*
*COMMENT**ZEELISH*💓