*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*09*
UNEDITEDHannun sa rik'e da nata har zuwa part d'in shi, Bakin gado ya zaunar da ita, Ya shimfid'e Mimi wacce tuni tayi bacci a hannun sa,
K'aramin fridge dake d'akin ya bud'e ya d'auko bottle na ruwa masu sanyi, Ya bud'e ya mik'a mata, ba musu ta karb'a,
Kusan rabin robar ta sha, ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya, ruwan sun saka ta jin wani sanyi a ranta, "Oya sleep bana son na k'ara ganin hawayen ki", Ya fad'a yana nuna mata pillow, Kai ta mishi nodding ta kwanta, shima ya kwanta tare da kashe wutar d'akin.
Fetta ta nemi bacci ta rasa, ta kawai rufe ido ne tamkar mai bacci dan kar Suraj ya fuskanta, tunani ne birjik a k'wak'walwar ta,
Cikin mintuna kad'an bacci ya d'auke sa, saukar numfashin sa kad'ai take ji, Hakan yasa ta bud'e ido ta zuba a kansa, Ba zata iya fassara me take ji a kan sa ba, Tabbas yau taji yana da matsayi a rayuwar ta, yayi rescueing life d'in ta,
"Ashe yana da tausayi?" Ta tambayi kanta, Wata zuciyar tace "Yayi ne dan yar' sa", Siririn tsaki taja tare da kawar da kanta daga kallon sa,
"Ba zan tab'a bari asiri na ya tonu ba, sai an samu Suraj ta kowane halin, son da nake masa ba zai tafi a banza ba wallahi", Tasleem ta fad'a, ta kasa bacci sai faman juyi take kan gado.
*5:40am*
Kiran sallar asuba ya tashi Suraj, ya mik'e da sunan Allah a baki, Fetta har lokacin bata yi bacci ba, ta hau mitsittsika ido alamun daga bacci ta tashi, "Zan koma sashen Hajiya",
Ran sa ne yaji ya b'aci, wato har ta gaji dashi tunda asuba tana buk'atar komawa, "K'ofa a bud'e take ai, ko na rik'e ki", Ya fad'a yana shigewa toilet,
Cike da haushin kalaman sa, ta d'auki Mimi ta fice daga sashen, "Wato shi ba zai tab'a canzawa ba", Wani b'angare na zuciyar ta yace "Hali zanen dutse"
Toilet ta shiga, tayi wanka, pad take son canzawa, shiyasa ta buk'aci dawowa, doguwar riga ta saka, ta fesa turare ba tayi kwalliya ba, Ta kwanta kan gado, cikin ikon Allah bacci ya d'auke ta,
Suraj ya fito toilet bai ganta ba, ita da Mimi, Prayer mat ya shimfid'a ya kabbara sallah.
Bello sun dawo sallar asuba tare da Kawu Lamid'o, Zai wuce d'akin sa, Kawu Lamid'o yace "Nayi wata yar' shawara ka duba yarinyar mai gidana watak'ila taku tazo d'aya", Bello yace "Toh", Yana jin wani k'ulloton bak'in ciki ya tsaya masa mak'oshi,
Ya wuce d'akin sa, yana tunanin hali irin na iyayen shi, burin su ya auri yar' mai hannu da shuni basu damu da tarbiyar ta ba, ya tabbata saboda kud'in mai gidanshi yace ya nemi yar' sa, sanin kowa ne bata da natsuwa, Ya kwanta kan gado yana had'iyar bak'in ciki.
Masu aikin gidan da hirar abunda ya faru jiya suka tashi, kowa yana tofa albarkacin bakin sa.
Suraj ruwan tea kad'ai ya sha, Ya fito burin sa ya isa station, yaji wanda ya turo su, A lek'a sashen Hajiya tana bacci, bai bi ta kan Fetta ba ya fice.
Tunda aka kai su Jangwal cell aka rufe, ba'a musu komai ba, suna jiran su ji daga Suraj, an dai cirewa Jangwal bullet aka d'aure k'afar,
Yan' sandan wurin na matuk'ar girmama shi, cikin ladabi suka gaishe shi, Ya amsa, Ya buk'aci ganin su Jangwal, aka fito dasu, ganin shi kad'ai sai da gabansu ya fad'i, suka dake, suna son su nuna su yan iska ne,