24

3K 307 56
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*24*

Kallon ta yake a razane, yana son tabbatar da abunda kunnen sa suka jiye masa, "Kai nake jira, saki uku nake buk'ata", Wani banzan kallo ya watsa mata yace "Are you out of ur sense, kinsan me kike fad'a?", "K'warai kuwa Suraj takardata nace ina buk'ata", Mamaki ya cika sa ganin yadda take masa magana gatsau,

   "Taya kake tsamannin na cigaba da zama da Dan' fashi wanda cin sa, tufafin sa, muhallin sa duka daga haramun ne, har nima ya ciyar dani ta wannan hanyar, taya kake tunanin na cigaba da zama da mutumin da ya bada umarnin a kashe mahaifina" Ta k'arasa hawaye masu d'umi na wanke fuskar ta,

    "Sam ban gane ina maganganun ki suka dosa ba, Ni Dan' fashi ne amma taya na sama silar kashe mahaifin ki?", "Gidan Alhaji Adamu da kaje fashi, mai gadin sa shine mahaifina, Ka cuce ni Suraj, Allah ya isa tsakanina da kai, ina fatan wannan ta zama rana ta k'arshe da zan saka a idona, bana fatan sake ganin ka a rayuwata" Ta zauna k'asa tare da k'ank'ame Mimi a jikinta tana kuka mai tsuma zuciya, zuciyarta na d'aci wanda ke kawo mata har cikin mak'oshin ta zuwa bakin ta,

   Suraj tashin hankalin da bai tab'a ji a rayuwar sa ba yaji ya dabaibaye sa, ko rasuwar mahaifin sa bai ji irin sa ba, zufa ta shigo karyo masa, zuciyar sa na dokawa da tsananin k'arfi, yana jin ina ma mafarki yake ya farka, har cikin ransa yake jin kukan ta, wanda ke k'ara d'aga hankalin sa da dagula masa lissafi, Cikin karyewar zuciya ya gurfana gaban ta, yana k'ok'arin kai hannun sa ya tallabo fuskar ta, Tayi saurin ja da baya tana fad'in "Kada ka sake ka tab'a ni, bana buk'atar komai daga gare ka sai takarda ta", Yawun bakin sa ya kafe, ya kasa furta komai, ya rasa da wacce kalma zai fara bata hak'uri ya tausasa zuciyar ta, mutuwar mahaifin ta shine babban laifin da yake ganin ya aikata mata, zaman shi dan' fashi bai shafi rayuwar ta ba,

  Ta katse mishi tunani "Ka bani takarda ta ko naje na sanar da Hajiya komai da sani game da kai", Jin haka ya girgiza, baya son tashin hankalin Hajiya, haka baya jin zai iya sakin ta, bai tab'a jin rashin son rabuwa da ita kamar yau ba, Cikin karyewar zuciya yace "Dan Allah Fatima ki.....", "Bana son jin komai, bana buk'atar jin wata kalma da zata fito daga bakin ka", "Ki duba Mimi, kina so ta taso babu uwa a tare da ita, kina so tayi rayuwar maraici", Sai a lokacin ta d'ago tana bin sa da kallo mai cike da tsana tace "Kana tunanin zan tab'a barin ya'ta ta taso cikin k'azamar haramtacciyar rayuwar ka, har abada bazan bari tasan waye Mahaifin ta ba, dan bara ta tab'a alfahari da kai ba, daga yau mahaifin Mimi ya rasu, na shafe tarihin shi a cikin rayuwa ta da na ya'ta, bana fatan mu sake ko da awa d'aya a k'ark'ashin inuwar ka"

   Zuciyar shi ke tafarsasa, maganun ta sun b'akanta ran sa da zuciyar sa, babu mahalukin da ya tab'a fad'a masa magangun da suka sosa zuciyar sa kamar yau, lips d'in sa na k'asa ya cije cikin tsananin b'acin rai, har sai da ya jini ya fito, Zuciyar sa na ingiza sa da hasassa masa ya sake ta, Takardar ya jawo tamkar zai yi k'wace a hannun wani, ya d'auki biro cikin zafin nama, ya rubuta mata saki biyu, Ya jefa mata takardar yana ficewa daga falon,

    Takardar ta d'auko ta karanta, zuciyarta ta harba da k'arfi wanda ta rasa dalili, mik'ewa tayi, Ta goya Mimi, ta saka hijab da nik'ab, K'aramin littafi mai d'auke da asalin ta kad'ai ta d'auka, Ta fice daga gidan ba tare da kalli b'angaren Hajiya ba, bata son duk wani abu da zai tsayar da ita, Zuciyarta take bi, ba abunda take buk'ata kamar tayi nisa da Suraj da duk wani abu da ya dangance shi,

   Gidan Waheeda ta nufa, Ta same ta ita kad'ai mijin ta baya nan, Kallo d'aya Waheeda ta mata ta hango rashin natsuwa a tare da ita, "Lafiyar ki kuwa Fetta?", "Jikina ne baya mun dad'i", Ba dan ta yarda ba tace "Allah ya baki lafiya", "Amin Dan Allah aron dubu goma nazo ki bani", Karon farko a rayuwar ta da ta rok'i abu wurin wani, shima babu yadda zata yi ne, duk kud'in da ta samu ta hanyar Suraj, ta ajiye masa, hatta ATM d'in ta bata d'auko ba, Waheeda tayi mamakin jin haka sanin irin dukiya ta Suraj, ba tare da tace komai ba, Ta shiga d'aki ta d'auko ta bata, tace "Kyauta na baki", Fetta ta amsa ta mata godiya.

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now