22

3.6K 347 17
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*22*
*Unedited*

    *Kuyi sorry da yadda zaku ga typing na yau, am very busy*

    *Yan Wattpad votes d'inku yayi k'asa zan daina muku post fah*

   "Fetta kece dai kamannin ki basu canza ba", Cewar wani dattijon mutum, " Fettan mu ta girma, kin tafi kin barmu muna ta cigiyar ki" D'ayar matar ta fad'a,

    Kanta ne ya masifar d'aure mafarki take ko da gaske, wad'annan mutane bata tab'a ganin su ba, ko yan' uwan ta ne, "Kar dai kice baki gane mu ba", Mutumin ya fad'a, " Ban gane ku ba, kuna da masaniya ne akan dangi ne", "Haba Fetta mu girma mu tashi dake, ki nuna baki san mu ba", Matar ta fad'a,

   Kafin tayi magana, Aunty Jummai tace " Kada ki raina mana hankali kinji koh", Da mamaki ta bita da kallo, Hajiya tace "Zauna Fetta", Sai a lokacin ta samu zama, " Ki fad'a mun tsakani da Allah, meye tsakaninki da mutane nan", "Wallahi ban san su ba, ban tab'a ganin su",

   " Laahhh ni Hard'o ne baki sani ba", Ya fad'a yana tab'a hannu, Hajiya ce ta mishi alama da hannu yayi shiru, Ta juya kan Fetta tace "Kada kiji tsoro, ki fad'a mun gaskiya, sun gaya mun komai a game dake", Kanta ya fara d'aurewa ta fara shiga rud'u tace " Me suka ce miki Dan Allah?",

     Hajiya ta gyara murya tace "Iyayenki sun rasu tun kina jaririya, suka barki a hannun k'anin mahaifinki wato Hard'o, a wani kango kuke zama, yana garuwa, Matar sa ke rainonki har kika girma kika yi wayo, Ta fara zuwa dake tasha wurin bara, Mazan tasha da yawa suna sonki saboda kyan ki, da haka suka fara jan hankalin ki da kud'i, tun kina shekara goma kika san maza, ki kwanta dasu su baki kud'i", " Ki kwanta dasu su baki kud'i", Ya sauka a kunnen Suraj, da shigowar sa kenan, Hajiya ta matsa masa ya dawo,

   "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un", Ta shiga maimaitawa, jin sharrin da aka k'ullu mata da Allah kad'ai zai wanke ta,

" Karuwa kenan, Karuwa zan aura", Duka suka juyo kallon su gare shi, banda Fetta da taji kalmar Karuwa tamkar saukar aradu, Kuka take son yin ko zata rage nauyin da k'irjin ta ya mata, jin ta take tamkar a wata duniya, jikinta banda kyarma ba abunda yake, Aliya kasa ko da k'wararran motsi tayi, "Meyasa Fetta zata b'oye mata ainahin labarin ta?", Suraj ya k'arasa shigowa cikin falon, Zuciyar sa na tafarsasa, wane masifar haushi da tsanar Fetta yake ji, tamkar ya rufe ta da duka,
 
    Ta saitin ta yazo wucewa, ya take mata yatsan hannu, sai da yayi k'ara, Tayi saurin janyewa cike da azaba, tana yarfa hannun,

    " Ya akayi ta bar wurin ku?", Aliya ta tambaya, "Wani ta kwanta dashi, yak'i biyan ta kamar yadda yayi alk'awari, ta d'auki kwalba ta buga masa ta gudu",

   Hannu biyu tasa ta toshe kunne, k'wak'walwarta ba zata iya d'aukar labarun k'aryar da ake fad'i akanta ba, " Munafuka bud'e kunnen ki", Ya daka mata tsawa, Ko gezau batayi ba, Ya d'aga hannu zai falla mata mari, Hajiya tace "Kul, kar ka fara",

    Hajiya ta taso ta d'aga ta tace " Taso muje", Ta mik'e tabi Hajiya ba dan tasan inda take jefa k'afar ta ba, D'aki ta shigar da ita, ta zaunar da ita kan gado, ta saka ma k'ofa key,

     "Fetta ina so muyi magana dake kamar yadda uwa zata yi da yar' ta", Kai kawai ta iya d'agawa, " Ki fad'a mun gaskiya tsakani da Allah",

     "Wallahi Hajiya Allah shine shaida ta, bansan su ba, bansan nufin su namun wannan sharri ba, Mahaifiyata ta rasu tun ina shekara biyu, Mahaifina yan fashi suka kashe shi, bansan kowa nawa ba, a gidan Alhaji Adamu na tashi naga Mahaifina na gadi, kisa a miki bincike", Hajiya taji ta gamsu da zancen ta, tabbas wani tuggun aka shirya dan a lalata auren, Tasan abun yi,

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now