*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*51*
*Unedited*Ya ajiye ta gida, Ya wuce ya kai international passport nashi da nata a musu visa.
Karima anyi auren su da Bello, ya d'auke ta sun koma Abuja da sunan ya samu aiki a can, Ta shiryu, ta koma ga Allah, kullum cikin istigfari,
Su'ad da Adnan abun su yayi gaba, almost all the time suna tare, ya d'auke ta suje hotel suyi sharholiyar su, ta saba wani lokaci ita ke requesting.
"Please bana so yayi taking time", Cewar Suraj, " Kada ka damu ranka ya dad'e in two days time komai zai kammala", "OK", Ya fad'a tare da ficewa.
" Komai baya tafiya daidai, yanzu ya kamata ace tuni na dad'e da mallake Suraj", Tasleem ta fad'a tana zagaye d'akin, Sophy dake zaune bakin gado tace "Nasha gaya miki ki hak'ura da Suraj, samun irin shi nada matuk'ar wahala", A fusace ta juyo tace " Ni kuma nasha gaya miki bazan tab'a hak'ura dashi ba", "OK then", Ta fad'a tare da d'age kafad'a, Ta shiga danna wayar ta,
Tasleem ta kasa zama, tunanin ta ya zata shawo kan Suraj, duk hanyar da ta bi is not working, Ya zama dole ta k'ara zage damtse, babban takaicin ta Fetta da zata haihu, " Ki sace babyn ki kashe shi", Zuciyarta ta fad'a mata, Tayi murmushin mugunta.
Aunty Yelwa ce zaune tsakar gida, Wayarta a hannu tana kira ana ce mata number busy, "Ko da uwar wa yake waya yasan ina jiran sa", Ta fad'a tare da yin k'wafa, Kiran sa ne ya shigo wayar, Ta danna receive,
" Dawa kake ta waya ne?", "Ai ke nake ta kira ana cemun busy", " Oh toh, ya ake ciki ka same shi?", "Eh yanzu haka muna tare", " Good aikin ka yayi kyau, gani nan zuwa", "Sai kin zo", Ta kashe wayar tare da fad'in " Lokacin ramuwa yazo Jummai, kin d'auka kinci bulus", Tayi murmushi mai cike da ma'anoni.
Aunty Jummai tana zaune d'aki ta rafsa tagumi, Bilkisu ta shigo da sallama, sam bata ji ba tayi nisa a tunani, Ta janye hannun ta tace "Umma tunanin me kike?"
Ta sauke ajiyar zuciya tace "Hmm cikin Fetta da yak'i zubewa, gashi har ya girma", Bilkisu tace " Nima abun na matuk'ar damuna, dan wallahi ina so na koma gidan Suraj kuma bana son kishi da ita", "Ina tunanin mu kashe jaririn kar yazo duniya ko ranar da aka haife shi", " Nima nayi tunanin hakan", Cewar Bilkisu, "Wannan itace mafita", " Umma zan fita", "A dawo lafiya, kina da yan' chanji", Ta bud'e jaka ta zaro dubu biyu ta bata, Ta karb'a tana washe baki, Bilkisu a ranta tace " Umma ba dai son kud'i ba", Ta fice zata je wurin wata yar' lesbian da suka had'u a Dubai.
"Zancen tafiyar ka da Fetta, hankalina bai kwanta ka tafi da ita haihuwa wata k'asa, ba wani nata a can" Cewar Hajiya, "Mama tafiyar nata shine mafita, duba da yawan rashin lafiya da take, wanda mak'iya ne gara ta bar 9ja ta haihu a can lafiya", Hajiya ta nisa tace " Hakane but ya kamata ku tafi da wani babba da zai kula da ita", "Kada ki damu Mum, a can zan samu masu kula da ita", " OK Allah yayi jagora, Allah ya sauke ta lafiya", Ya amsa da "Amin"Fetta na kwance a kujerar falo tana kallon Sunna TV, Ya shigo da sallama, Ta amsa ba tare da ta d'aga kai ta kalle shi ba, Kusa da ita ya zauna tare da d'aura hannun shi saman cikin ta, Ta d'ago kai ta kalle shi, Kallon da ya jefa mata yasa ta sunkuyar da kai jiki a sanyaye, Suraj ya nak'alci kallo iri-iri,
Cikin yake shafawa cikin wani salo wanda ya saukar mata da kasala, Rigar ya d'aga ya sumbaci cikin, "Safe delivery", Ya fad'a tare da mik'ewa ya nufi d'aki.