*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*41*
UNEDITEDYau jumu'ah bayan an taso daga masallaci aka d'aura auren Suraj da Fetta a karo na biyu, dumban mutane sun halarta, Ango Suraj da yasha d'inkin shadda sabuwa dal wacce Amanukal ya bashi a matsayin karramawa, yana ta washe baki, Sultan ma ya halarta, yana ta far'a sam bai nuna wata damuwa ba, ya yarda da k'addara, Allah yayi Fetta ba matar sa ba ce.
Amarya Fetta tasha ado cikin shadda mai masifar tsada wacce tasha d'inkin nijar, kunnen ta, wuyan ta da hannun ta sun sha adon zinari mai azabar kyau da tsada, kallo d'aya zaka mata kasan amarya ce yadda take k'yalli, hannun ta da k'afa sun sha adon lalle ja da ya k'ara haskata, tabbas wannan auren ya sha bambam da na fari, auren ta na farko sam bata farin ciki kasancewar babu d'igon soyayyar sa a zuciyata kuma babu ahalin ta ko d'aya sab'anin yanzu da take jin tsantsar farin ciki, zuciyarta cike da d'umbin k'aunar sa, ko ina ta waiga yan' uwanta ne mak'il,
"Kizo zaku yi hotona da ango" cewar Yasmeen tana jan hannun ta, Ba tare da musu ba tabi bayanta, a ranta tace "Tamkar auren fari ba na biyu ba", Auren fari ma bata samu arzik'in yin hoto dashi ba, A babban falon Amanukal ta same sa, yana zaune tare dasu Sultan, Mimi na hannun sa yana mata wasa,
Numfashin sa ya d'auke na wucen gadi ganin tsananin kyan da tayi, ya kasa d'auke ido daga kallon ta, Ba b'ata lokaci mai hoto ya shiga yi musu hotona, wanda suka yi different styles, Sunyi hotona sosai da Mimi, Kafin kowa ya watse aka bar su kad'ai a falon, Fetta wani kunya da nauyin sa taji yana dabaibayeta, ya matsa daf da ita, k'ugun sa yana gugar nata, wanda hakan ya sakar mata da jiki, ta kasa ko da k'wakk'waran motsi, hannun ta ya kamu, taji wani yar, "Lallen ki yayi kyau sosai", Tayi murmushi, yatsan ta na tsakiya ya kama ya saka mata d'an k'aramin zobe na zinari wanda kud'in sa ba zai wuce dubu goma sha shida ba, yace "Ga sadakin ki, kiyi hak'uri da wannan, nasan shine k'arami cikin zobunan dake hannun ki",
"Duk da kasancewar sa k'arami yafi mun duka sauran muhimmanci da daraja" Ta fad'i maganar da ta zata a zuci ne, "Really sanyin idaniyata", Kunya ce ta kamata jin maganar ta fito fili, ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa, "Yau kuma ni ake jin kunya", Tayi shiru tana murmushi, saitin kunnen ta yasa bakin shi yace "Kinyi masifar kyau Amarya ta, ina jin tamkar na sace ki na gudu" Maganar tasa dariya ta bata, ta fashe da dariya, "Au dariya ma na baki" Ya fad'a yana janyo ta jikin sa, yana shak'ar daddad'an k'amshin turaren ta, sam ya manta a inda suke, itama ta kasa raba jikinta da nasa, sai ma k'ara narkewa da tayi jikin sa, jin k'arar bud'e k'ofa tayi saurin janye jikin ta, Abutalib ne ya shigo yace "Ahh ango kana nan, ana can ana neman ka ayi hotona", "Yayar ka ce ta rik'e ni" Ya fad'a yana dariya, Abutalib ya kai dubansa ga Fetta yace "Tumuqqartin ai mana hak'uri mu tafi dashi", Dariya kawai tayi bata ce komai ba, dan yasa ta jin kunya, Suka fice, itama ta mik'e ta koma b'angaren Azagas.
Bayan sallar la'asar wanda za'a tafi dasu nigeria ke ta faman shirye shirye, Jirginsu shida na yamma, Fetta na d'aki tana shirya sauran kayan ta da taimakon Yasmeen, wayar yasmeen tayi k'ara, Sunan Habibi Fetta taga yana yawo saman screen d'in, Yasmeen tayi receiving da fad'in "i will call u back",
"An samu mana suriki shine ba sanarwa" Cewar Fetta, Murmushi tayi tace "Ba haka bane, ina da niyyar sanar dake", "Toh wanene shi?, kuma a ina yake?", "Wallahi a super market muka had'u shine ya biyo ni har gida, kafin na taho iyayen sa suka zo aka tsayar da magana, wata uku masu zuwa", Cike da tsantar farin ciki Fetta tace "Allah ya nuna mana lokaci lafiya ya sanya alkhairi", "Amin", "Wallahi nayi murna matuk'a", Yasmeen tayi dariya.
6:00pm
Jirginsu Fetta ya d'aga daga jamhuriyar Nijar zuwa nigeria garin Kano, da kuka ta tafi tana jin tamkar kar ta bar ahalin ta, mutane goma suka mata rakiya, Amanukal ya had'a ta da hadimai biyar wanda zasu cigaba da mata hidima a can, Aliya da Mallam ba k'aramin sha tara na arzik'i suka samu ba daga wurin Amanukal da Azagas, Mummy da Daddy suma sun musu alkhairai mai d'umbin yawa.