*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*07*
UNEDITEDSu'ad da Feena sun dawo ba tare da kowa ya gansu ba, Suka shige d'akunan su, Sunyi nasarar shawon kan samarin nasu sun hak'ura, Su'ad sai da suka darje da Adnan, Feena duk chilling d'inta ko romance bata tab'a yi ba, tana tsoron zina(Nace da tsoron Allah a ranki).
Bayan sallar isha'i, kowa ya watse, Suraj ya shigo cikin gida, A d'aki ya samu Fetta tana k'ok'arin cire kaya ta shiga wanka, "Ki shirya zamu yi pics", Yana fad'ar haka bai jira cewar ta ba, Ya fice, Tabi bayan sa da kallo, ta sauke ajiyar zuciya, har ga Allah a gajiye take amma ya ta iya, Ta sake shiri, a babban falon gidan ta same shi, Yana d'auke da Mimi, Sukayi hotuna different styles,
Ta juya zata koma ciki, Ya rik'o hannun ta, Ta juyo tana kallon sa, Ya saki hannun tare da cewa "Biyo ni", Ba musu tabi bayan sa, A harabar gidan ya tsaya kusa da wata dalalleliyar mota, hannun ta ya jawo ya d'aura mata key, "Tukwicin haifa mun little angel" Ya fad'a yana kallon Mimi, Ta kalli motar itace wacce ya tab'a cewa ta taya shi zab'e, abokin shi zai siyan ma matar shi,
Mamaki ya cika ta, a ganin ta wannan mota tafi k'arfin ta, Murya a sanyaye tace "Nagode amma ba sai ka bani tukwicin komai ba, yayi yawwa besides ban iya tu....", Kallon da ya jefa mata yasa ta kasa k'arasa maganar, Fuskar ya d'aure wanda ta dad'e bata ga yanayin da haka ba, Ya wuce part d'in sa,
Ganin yanayin sa taji duk ba dad'i ba, tana ganin bata kyauta ba, Rai ba dad'i ta koma sashen Hajiya,
Bakin gado ta zauna shiru, Ta jawo wayar ta, tayi mishi text ta tura,
Suraj na rungume da Mimi, system na gefen sa yana operating, wayar sa tayi k'ara, kamar zai share, ya jawo ya duba
"Kayi hak'uri ba nak'i kyautar da kamun ba ne, sai dai ina ganin kamar yayi girma, hidimar da kamun kad'ai ta wadatar, Nagode Allah ya saka da alkhairi"
Yana gamawa karantawa yaji wani sanyi a ranshi da ya rasa dalili, Murmushi yayi ya ajiye wayar ya cigaba da operating system.
Fetta nata jiran taga reply d'in sa shiru, ko har yanzu fushi yake, ranta taji duk ba dad'i,
"Meyasa zaki damu?", Ta tambayi kanta, Siririn taki taja, Ta gyara kwanciyar ta, a haka bacci ya d'auke ta,
Feena taje sashen kai mishi abincin dare, Ya bata Mimi ta kai ma Fetta,
Cikin bacci taji k'arar k'ofa, Ta bud'e ido taga Feena ce rik'e da Mimi, "Gata inji Ya Suraj", Ta mik'a mata, ta fice
Tabbas fushi yake dani tunda har yak'i maido Mimi da kansa kamar yadda ya saba, Rai ba dad'i ta shimfid'e ta, ta koma bacci.
2:00am na dare
Jirgin su Tasleem yayi landing, Tana sauke k'afarta matattakar jirgi na k'arshe, Tayi wani shu'umin murmushi, Zuciyarta ta bushe, soyayyar Suraj yasa ta makance, komai zata iya aikata, ta dawo 9ja da k'udurin kawar da Fetta da yar'ta a doron k'asa.
Driver gidan su yazo d'aukar ta, Daddyn ta na falo na jiran isowar shalelen sa, Tana shiga falon ta fad'a jikin sa, "Oyoyo My daughter", "Daddyna i miss you", "Ya gajiyar hanya?", "Alhamdulillah", "Ki shiga kiyi wanka, kizo kici abinci sai ki kwanta", "Toh Daddy", Ta fad'a tana mik'ewa ta nufi d'aki,
Wayarta ta zaro daga cikin handbag, ta bud'e wadrobe na d'akin ta, sim ne a ciki zasu kai guda biyar, ta d'auki d'aya tasa a wayar,
Kan number Suraj taje, Ta tura mishi text