*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*16*
_Hidaya s bakery, Ummu Zarah, Elbeelah, Firdausi Adam, Habiba Muhammad, Zainab Namadi Thanks for d love💕💞_
Sallama tama Hajiya Tumba da alk'awarin gobe zata dawo.
Da haushin magangunan Suraj ta dawo gida, A tsakar gida ta tarar da Aliya tana yanka alayyahu, "Sannu da aiki Umma", " Yawwa Fetta, kin dawo?", "Eh", Ta fad'a tana zama kan kujerar tsugunno, " Ya kika baro Hajiyar?", "Da sauk'i, ta buk'aci na zauna da ita har zuwa lokacin da za'a sallame ta", " Toh ya kika gani zaki iya?", Ta d'aga kanta sama, "Kinsan fah kina jarabawa?", " Zan iya Umma, ai muna samun interval, Hajiya Tumba nada kirki ina so na samu ladar jinya", "Toh Shikenan, idan Mallam ya dawo zan sanar dashi",
"Kawo na yanka miki", " A'ah bar shi ai na kusa", Mik'ewa tayi ta shiga d'aki.
Baban Bilkisu ya kira Suraj ya tambaye shi ba'asin sakin, Ya fad'a masa bai b'oye mishi komai ba, Ya matuk'ar girgiza da jin abunda ta aikata,
Sun ga ruwan bala'i da tijara, Daga Bilkisu har Aunty Jummai ya had'a yayi wa tass, Yace kuma wallahi ba zai ciyar da ita ko k'wayar shinkafar sa ba, Lamuni d'aya zai mata na zaman gidan, Aunty Jummai kam cewa tayi sharri ake wa yar'ta, taji zata kula da cin ta da shan ta.
Labari ya kaiwa su Kawo Sule, "Zan so naga idon Jummai ta gama yi mana dariya da tijara, ga ranar da ake gudu, Bilkisu da aikata mad'igo har an sako ta", Ta fashe da dariya, Karima tace " Allah ya sawwak'a", Taja hannun dan' ta suka fita, Gaba d'aya tayi sanyi tun abunda Bash ya aikata mata,
Aunty Yelwa murna take sosai da faruwar haka, Kawo Sule ma yayi Allah ya k'ara, Da yawa yan' uwa Allah ya k'ara suke yi, Jummai ba irin wulak'ancin da bata musu ba, Tana ganin tafi k'arfin su yar' ta na auren Young billionaire.
Sallama Yelwa ke tayi tun daga bakin k'ofa, Bilkisu dake kwance tsakar gida da d'aurin gaba(Haka take wuni saboda k'onuwar dake bayanta, ga shatin duka duk sunyi rud'u rud'u)
Ta amsa sallamar,Jummai ta fito, Ganin Yelwa ta bi ta da harara, Tasan ba zuwan arzik'i tayi ba,
"Ya da harara Jummai, ni fah jaje nazo yi muku", " Baki zo sanya alkhairi ba lokacin biki sai yanzu da aure ya mutu", "Kinsan fah lokacin muna cikin jimamin na Karima", Aunty Jummai tace " Uhmm, ga tabarma ki zauna toh",
Ta zauna tana fad'in "Haka Suraj ya mata, Gaskiya ya d'auka da zafi wai, amma dole zai yi haka ka kama matar ka na aikata mad'igo", " Ni fah bana son k'ananun maganganu da k'ala sharri, ya'ta bata ga mad'igo ba", "Ohh jama'a da k'in gaskiya suke, kowa dai yasan abunda yar'ki ta aikata kenan aka sako ta", " Kina da Shaida na ta aikata, ke kuwa yar'ki da yake karya ce akan bin maza, ai hadda guzuri tayi"
Nan suka shiga yi wa juna gori, mak'ota ne suka jiyo su, Suka shigo suka raba su, aka fitar da Yelwa tana ta zage zage, haka aka rabu dai ba arzik'i.
Zulaihat da labari yaje wa iyayen ta, korar ta Mahaifin ta yayi sai gidan kakannin ta na gefen uwa ta koma, A can take jinya.
A daren aka shiga yi wa Hajiya tiyata, Su'ad, Feena da Ya Suraj suna asibitin hankalin su ya kasa kwanciya, addu'ar nasara a operation d'in suke, Suraj ya yanke shawarar idan bai yi ba, Zai fitar da ita k'asar, Bai sanar da kowa ba a yan'uwa ya kuma hana su Feena fad'a, Baya so a zo a cika asibitin a isheta da hayaniya, Idan operation d'in is successful zai fad'a musu su zo dubiya, shima dan kar Hajiya tayi fad'a, Tayi ciwo bai sanar da yan' uwa ba.