46

3.6K 290 12
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

  _*Haske writers association*_

*46*
*Unedited*

Ta jingina da motar,  tana kallon harabar wurin, Suraj ya juya mata baya, ta zuba masa ido tana jin son shi na ratsa jinin jikin ta, Driver ta ya bud'e booth yana fitar da kaya, kayan abinci da ghana must go cike da kayan sawa,

     Mai kula da gidan marayun ta buk'aci gani, aka mata iso zuwa office d'insa, "Madam duk abunda ya shigo gidan marayun nan, sai Sir Suraj ya duba ya tantance", " OK", Ta fad'a hakan ya mata dad'i, Tayi dama dan ya yaba,

     Office na Suraj dake orphanage d'in suka nufa da kayan, Sule(Mai kula da wurin) ya nuna mata kujera ta zauna, Shima ya zauna suna jiran Suraj.

    K'amshin turaren sa da ya daki k'ofofin hancin ta yasa ta lumshe ido, Ya shigo cikin takun sa na k'asaita, Taji tamkar ta rungume shi,

    Ya zauna fuskar sa ba walwala, Hankalin sa yaji ya kasa kwanciya da ita, "Sir ta kawo ma marayu kaya ne", Yayi nodding kai tare da cewa " Bud'e mu gani", Sule ya shiga bud'e kayan yana gani, "It's ok, a d'auka a kai musu", Ya jawo wani file yana dubawa, ba tare da ya sake bi ta kanta  ba,

  Tasleem ranta taji ya b'aci, ganin bai nuna appreciation ko jin dad'i ba, ya nuna tamkar bai san da zaman ta ba, Ta had'e b'acin ranta tace " Sir Suraj ni zan koma", Ya d'aga mata kai ba tare da ya d'ago kai ya kalleta ba,

   Rai a jagule ta bar orphanage d'in, "Akwai aiki a gabana", Ta fad'awa kanta.

     "Maigida haka zamu zuba ido, muna ji muna gani Bello ya rasa Feena", Cewar Gwaggo, "Toh ya zamuyi tunda tak'i sa", " Ni Hajiya Tumba tafi bani haushi yadda ta kasa tsawa ta mata", "Ai munafuka ce, ba son auren take ba, ita ke zuga su", Gwaggo cike da takaici tace " Hmm"

   Hayaniya ke tashi gidan karuwai na sabon gari, kowa da abunda yake, Masu shan sigari nayi, masu lido nayi, masu shan wiwi nayi, Karima ta fito d'akin ta d'auke da Abdul, zazzab'i yake zata kai shi asibiti,

     "Ban tab'a ganin inda zuwa bariki da yaro ba", cewar wata karuwa, D'ayar tace " Wallahi ai ko a bariki na same sa na yarda shege a bola", "Ni bazan bar sa ma yazo duniya ba"

   Karima bata tanka su ba ta wuce abun ta, Ta tari mai napep ya kai ta asibiti, Likita ya duba sa, ya mishi allura tare da bashi drugs, Ta fito bakin asibitin tana tare napep, Bello dake cikin mota ya hangota, Ajiyar zuciya ya sauke tare da hamdala, Ya nufa su, Bata lura dashi ba sai ganin sa tayi a gabanta, Zuciyarta ce ta buga,

   "Karima ina kika shiga, kin barni cikin tashin hankali, zuciyata ta kasa natsuwa", " Baka san Baba ya kore ni ba", "Na sani meyasa baki neme ni ba?", " Banyi tunanin haka ba", "Ok kina ina ne yanzu?", Ba tare da shakku ba tace " Gidan Karuwai dake sabon gari"

      Ya zaro ido yace "Gidan karuwai", " Eh", "Meyasa kika zab'i zama can?", " Ana so naje can shiyasa aka kore ni, bani da wurin zama da ya wuce can", Ta fad'a zuciya a raunane, Tausayin ta ya kama shi, Yace "Dan girman Allah ki bar gidan marayu muje na baki masauki", Ta girgiza kai tace " A'ah Ya Bello, kada ka jefa kanka cikin gurb'atacciyar rayuwata", "Kada ki k'ara danganta rayuwar ki da gurb'atacciya, muje", Ya karb'i Abdul hannun ta, Ya nufi mota, ba musu tabi bayan sa,

    Gidan karuwai ya kai ta, ta d'auko kayan ta tare da musu sallama, Gidan sa dake unguwar hausawa zoo road, Ya kai ta, ya siyan musu kayan abinci da komai na buk'ata, Zata mishi godiya ya hanata, Bello Allah ya d'aura mishi k'aunar Karima, yana son gyara mata rayuwar ta.

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now