*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*24*
Mu'azzam da yaji labarin auren Fetta yaji ba dad'i, but yana mata Fatan alkhairi, Allah ya mata sauyi da wanda yafi shi, "Suraj yayi dacen mata", Ya fad'a,
" Meyasa kika zab'i zama karuwa, abunda Bash ya aikata miki bai isa ya zaman miki darasi ba", Karima ta nisa tace "Abunda Bash ya aikata mun yasa naji tsanar iskanci da nadama, k'auracewar iyayena da nuna mun halin ko in kula, yasa na fad'a karuwanci dan na samu kud'in taimakon kaina", " Iyayen mu na kuskure, idan yarinya ta lalace maimakon a jawo ta a jiki ayi mata nasiha da lurarwa, sai a wofantar da ita daga haka yarinya ta shiga duniya" Cewar Bello (D'an Kawo lamid'o ya dad'e yana son Karima, itace ta k'i sa),
"Karima kiji tsoron Allah, ki tuba kiyi istibra'i ni zan aure ki na baki dukkan kulawa", Murmushi tayi a duniya babu wanda take so sama da Suraj, tasan ya mata nisan da bara ta tab'a samun shi ba,
" Ya Bello ba nak'i tayin ka bane, amma ina tsoron abunda zai je ya dawo, kasan halin iyayen mu", "Kada ki damu, ki bar komai hannu na", Tace " Allah ya tabbatar mana da alkhairi", Ya amsa da "Amin", cike da murna,
Ana kiran magrib Suraj ya dawo gida, Fetta na kwance kan doguwar kujerar falo, tasbaha ce a hannun ta tana lazimi, Da sallama ya shigo, Ta amsa, Ta tashi zaune tace " Sannu da zuwa", Ya kalle ta ya kawar da kai, Abunda Bilkisu bata tab'a masa ba, ko sau nawa zai fita ya dawo, bara ta d'aga kai ta kalle shi ba, idan ta mishi magana kud'i take buk'ata, ko tabi ta hanyar Hajiya.
Fetta tana k'ok'arin sauke nauyin da Allah ya d'aura mata ne, Bedroom ya shiga, k'amshin turaren wuta mai dad'i yaji d'akin nayi, gado da komai a gyare tsaf, Ya tab'e baki, ya shiga toilet, Ruwan d'umi ya tara a jacuzzi, ya shiga ya kwanta ciki, a hankali gajiyar da ya kwaso na barin jikin sa.
Knocking k'ofar ake yi kamar zata b'alle, A tsorace ta bud'e, Feena, Su'ad da k'awar su ne, Wani banza kallo suka bita dashi, Suka rab'a gefenta suka shiga ciki, kowaccen su ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya kan d'aya, K'awar sai yatsina fuska take tana chewing gum, Fetta d'auke kai tayi, tana latsa waya, banda Suraj na ciki shigewa zata yi ta barsu, bata ciki da rainin wayon su,
"Baki ga mutane ne bane", Banza tayi tamkar ba da ita ake ba, Su'ad tace " Fetta dake muke magana", "Amma Su'ad baki da kunya, ina matsayin matar yayan ki kike fad'in suna na gatsau", K'awar su tayi shewa tace " Lallai samun wuri", "Ke fah yar' firit daga ina", A fusace Feena tace " Ke yar' matsiyata yar' cin arzik'i", Karaf a kunne Suraj,
Basu san yana ciki ba, sai ganin sa suka yi a tsaye, Su'ad tace "Yaya matarka sai rashin.....", Wata tsawa da ya mata yasa tayi gum,
" Rashin mutuncin ku da iskancin ku har ya kai kan iyalina, ya zama na farko na k'arshe da wata cikin ku zata yi mata ko da kallon banza, yadda kuke daraja ni haka nake so ku daraja MATATA",
"MATATA" Fetta ta nanata a ranta, tabi sa da kallo, Ya d'auke kai tamkar bashi yayi maganar ba, Ya cigaba "Ku bata hak'uri", Kowaccen su ta shiga bata hak'uri, " Ba komai K'anne na", Da gayya ta fad'a, Rai a k'ufule suka fice,
"Bana son kowa ya fuskanci zaman da muke dake, har yaje kunne Hajiya, ina gudun b'acin ranta, tamkar yadda mutum ke gudu mutuwar sa", Yana fad'ar haka ya nufi dining area, Ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana jinjina soyayyar da yake wa Mahaifiyar sa,
" Ya Suraj ya kira barorojin can Matar sa", Su'ad ta fad'a unbelievable, Feena tace "Shima ta bashi a abinci ya cinye", K'awar su Tasleem tace " Baki ji yadda zuciyata ta buga ba, da ya kirata matar sa", "Don't worry Frnd, asiri na lokaci ne, ke kika dace da Ya Suraj me zai yi da matsiyaciya", Haka suka cigaba da zagin Fetta.