*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*10*
Kawo Sule ya dinga matsawa Hajiya Tumba da kira kan sadaki, Dan dole ba da son ranta ba, Taba driver ta ya kai, Ya amshe yana washe baki.
Cikin gida ya samu Yelwa, tana tatar k'ullun kunu, Yace "Ga sadakin yar'ki dubu hamsin", Sakin matacin tayi, Ta rafsa gud'a " Ahayye Allah nagode maka, ya'ta tayi goshi, sai a saka rana ba tare da d'aukar lokaci ba", "Sati biyu nace", " Yawwa haka ya dace, dama na dad'e ina mata tariya, kuma a irin dukiya ta Suraj, ai bai ci ace taje da kayan d'akin ba, ko dan zumunci", "Hakane amma ko yaya ne mu k'ok'arta mu kai ta da wani abun gudun gori", " Gaskiya ne, Allah dai ya nuna mana ranar aure", "Amin", Ta shiga rawa da juyi.
Kawo Sule da yaje wa sauran yan'uwan sa da batun, Sunyi murna a fili, but da yawa cikin zukatan su tsantsar bak'in ciki da hassada ta mamaye su, Kowa yar' sa yayi wa kwad'ayin auren Suraj.
Aunty Jummai da labari yazo mata wata ashariya ta danna, Aminiyar ta tace " Kin tsaya sanya gashi an miki tsakiyar da ba rana", "Ko yanzu basu ci bulus ba wallahi", " Hmm meya rage yau fah saura sati biyu a d'aura aure", "Ai wallahi ko ranar d'aurin auren ne sai a fasa, rashin cikakkiyar hujja yasa tuni ban sa auren ya lalace ba, amma ina nan ina had'a hujjoji, k'wakk'wara d'aya nake nema", " Ki dai tashi tsaye, arzik'i muna kallo ya wuce mu", "Kwantar da hankalin ki Aminiyata", " Idan kinga hankalina ya kwanta, auren nan da Bilkisu akayi", "Anyi an gama", " Toh Allah yasa", "Amin"
Aunty Jummai nata faman jijjiga kai, tana kad'a k'afa, da cije baki.
Karima ta tattara ta koma gidan su, Mahaifiyar ta ta shiga aikin gyara ta, Duk wani gyara da tasan ana wa ya' mace idan zata yi aure shi take mata, Kullum sai ta mulke mata jiki da dilka ta hanata fita gaba d'aya, a cewar ta kada tasha rana.
Tafasar ya'yan bagaruwa ta sauke, Ta k'wala kiran Karima, Daga d'aki ta amsa, "Kizo ki d'auki ruwan bagaruwan nan ki zauna a ciki", Ta amsa da " Toh", Tana fitowa,
Kamar an jefo Aunty Jummai ta fad'o gidan, tana jefan su da matsiyacin kallo, Ta kalli ruwan bagaruwan tace "Duk gyaran da za'a mata, ba za'a tab'o maido da budurci ba dai, an gama kwararu a titi, za'a kai mishi ragowar wani", A kaf'ule Yelwa tace " Ke Jummai rashin mutuncin ki ya fara isa ta, dan kin bani shekaru bashi zai sa kizo gidana kina mun yadda kika ga dama ba", "Ahh lallai Yelwa, wuyan ki ya isa yanka, ni kike fad'awa haka", " An gaya miki, tunda ke baki san mutunci ba", "Zan shayar dake mamaki, daga nan gidan Hajiya Tumba zani, na sanar mata duk irin iskancin da yar'ki ta dad'e tana yi"
Dariya tayi tace "Wacce hujja gare ki, baki da dai hoton ta da wani, balle ya zama shaida", Aunty Jummai tasan hakane ko ta fad'awa Hajiya Tumba ba lallai ta yarda ba, tayi kwafa ta fita, a zuciyarta tana tunanin ina zata samu hujja.
" Umma nifah ina tsoron taje ta had'a wani k'ullin", Karima ta fad'a da damuwa d'auke a fuska, "Kwantar da hankalin ki, ba abunda zata yi barazana ce, nima ai a tafin hannu na take", Natsuwa taji, ta d'auki rubar ruwan bagaruwan tana nufar toilet.
Suraj kwanan sa uku ya koma Lagos, Baya son ko kad'an ana masa maganar auren Karima, Hajiya Tumba kullum addu'a take idan ba alkhairi bane, Allah yasa ya lalace.
Burinta Suraj ya auri yarinya mai natsuwa, hankali da tarbiya, mai asali mai kyau wacce zai samu natsuwa daga gare ta.
Kawo Sule da yan'uwan Yelwa kad'ai ke ta shirin aure, Hajiya Tumba ba wani shiri da take, ko yan uwan ta bata sanarwa da zancen auren ba, Suraj ma bata k'ara tuntub'ar sa da maganar ba, ko tace ya dawo, gashi saura kwana biyar a d'aura aure.